Kamar jiran fitar alk'ali ake aka sake kaurewa da maganganu kowa murya sama, Gomboy ce tayo kan Faduma kamar wata damisa da niyyar damk'arta, da sauri jami'in dake wurin ya shiga tsakiyarsu yana tare ta da hannu, mik'ewa Faduma tayi ta tattara kayanta, wata fizgowa ya mata ya rik'e hannunta gam ya nufi hanyar fita da ita, tana mutsumutsun k'watar kanta kuma jami'in yayi saurin tunkararshi yasha gabanshi, cikin had'e fuska ya nuna mishi wata k'ofa yace "Muje yallab'ai zaka biya tararka, daga nan zamu wuce da kai dan fuskantar hukuncin da kotu ta yanke maka."
Cike da gadara da raini yace "Minti biyu, ina so zanyi magana da ita ne."
Girgiza mishi kai yayi yana d'ora hannu akan bindigarshi yace "Baka da wannan damar, muje yallab'ai."
Da wani irin k'arfi ya tura Faduma ga bangon wurin ba tare daya saki hannunta ba, d'ora d'aya hannunshi yayi akan bangon shima ya k'urawa fuskarta ido, idonshi da sukayi jawur ta kalla tana sauke numfashi wani na bin wani, a hankali cikin amon muryar b'acin rai yace "Ina *d'ana* yake?"
K'asa tayi da idonta hakan yasa hawaye silalowa, saida ta sake sauke numfashi tana rarraba ido tace "Ban san shi ba nima, bana da d'a tare da kai, sake min hannu na."
A hankali ya sake cewa "Na biyu kenan zan sake tambayarki, karki bari nayi na uku Faduma, ina oddonur na yake?"
Saida ta rintse idonta cikin fashewa da kuka tace "Ban sani ba Tagur, ni babu wani d'anka a wajena, ka rabu dani na tafiyata."
Wani duka ya kaiwa bangon daya d'ora hannunshi da k'arfi da wata irin k'arajin murya kamar zai fasa wurin yace "Zaki gaya min inda d'ana yake ko saina kasheki a wurin nan? Ya zaki raina min hankali? Ni abokin wasanki nn..."
Bai k'arasa fad'a ba Faduma cikin tsoro da zabura akan tsawar daya mata da kuma tafasar zuciya ta d'auke fuskarshi da mari, bata bari ya gama tantance me ya faru ba cikin k'arajin murya ita ma har tana shak'ewa tace "Karka sake, kar bakinka ya sake kiran sunan d'ana da d'anka."
Numfashi ta shiga jerawa kamar wacce tayi gudu tana kallon idonshi kamar yanda shima yake kallon nata da mamaki. Duk wurin tsit ya d'auka dan babu wanda ya fita duk an tsaya kallon drama, su Atta ma dake can suna nasu fad'an ita da gomboy dole suka dakata jin k'arar mari.
Idonta jawur tana zubar da hawaye ta nunashi da yatsa manuniya tace "Karka sake kuskuren dangata kanka dashi, baka da alak'a dashi Tagur, kamar yanda na fad'a mishi ka mutu kaima ka d'auka ya mutu dan dama babu shi a wurinka, sannan karka sake d'aga min murya dan yanzu ba Fadu daka sani bace."
Ko da ta fad'a tasa k'arfi ta ture hannunshi da har yanzu yake jikin bangon ta fita, rintse ido yayi yana jin yanda zuciyarshi ke tafasa, sake dukan bangon yayi ya juya har zai fita sai kuma jami'in ya mishi nuna da d'aya d'akin, da k'arfi ya juya ya wuce shima ya bi bayanshi.
A b'angaren su Atta ma fad'a suke sosai ita da Gomboy tana fad'in "Dama kin min shiru ne dan haka ta faru, to yanzu kinji dad'i? Yar bak'in ciki kawai."
Tab'e baki tayi tace "Ai ba ni na aikeki yawon iskancin ba, da kin zauna d'akin mijinki ai da haka bata faru ba."
Cikin masifa tace "Ke har ni zaki kalla ki fad'a ma haka? Ba gwara ni ba nayi auren ma, ke fa? Kuma naga dani dake ai duk kanwar ja ce."
"Eh naji banyi aure ba, amma da aure irin naki gwara na tabbata babu aure, auren da zan dinga zina da aure na wallahi gwara banyi shi ba."
Hindu ce ta dakatar dasu da fad'in "Ya isa dan Allah, tsaya kuji."
Shiru sukayi sai huci suke suna kallon juna, a hankali tace "Kunga ba fad'a zakuyi ba, mafita zamu nema da zamu lalata shedar da aka kawo yau, kunsan miye abunyi?"
Girgiza kai sukayi dan haka tace "Mu nemi likitan, kud'i yake so ko jin dad'i duka zamu iya bashi, indai zai juya mana shaidar da aka gabatar yau d'in nan."
Cike da kurantawa Zaleeha tace "Sai ke uwar d'akina, wannan yayi."
Kallon Gomboy tayi tace "Ke kika sanshi, zamu je mu nemi rendez vous dashi, zamu sauya mishi tunani."
Jinjina kai gomboy tayi tace "Naji wannan, yanzu yanda zan fuskanci yan gida ne matsalar."
Hindu ce ta tab'e baki tace "Ke rabu dasu, murje ido zakiyi ki darzawa duk wanda ya nemi yaga miki rigar mutumci, dama can ai farin ki suke gani basu san bak'inki ba, karki sa matsalarsu a kan ki kinji." Jinjina kai tayi kafin suka rankaya suma suka fita.
_______________
Yana k'arasa shiga cikin makarantar ashe an sallami yaran nan sakamakon d'aya daga cikin malaman daya rasu, shiyasa aka ce duk su koma gida sai gobe tunda dama yau ba'a karatu da yamma, cike da damuwa ya samu wuri ya zauna yana kallon masu fita, baisan ya zaiyi yanzu Ayyarshi ta dawo ba, littafinshi ya fiddo zai fara karatu sai yaji wata yarinya a bayanshi na fad'in "Kai ba zaka tafi gida ba?"
Juyawa yayi ya kalleta, sai yaji kawai gabanshi ya fad'i dan haka ya k'yaleta ya koma karatunshi, matsowa tayi ta zauna kusanshi tana sake fad'in "Ka tashi ka tafi gida, ko d'aukarka ake zuwa kaima?"
Kallonta ya sake yi, ita ma kallonshi tayi sosai ita dai tana ganin fuskar kawunta a fuskar yaron, amma k'uruciya ta hana ta gane kama ne suke, a hankali yace mata "D'aukata ake zuwa."
Cike da wayo tace "To yanzu wa zai zo d'aukarka? Kaga babu wanda yasan ba za ayi karatu ba."
Kallonta yayi yace "Shiyasa na zauna na jira Ayyata."
"Amma ai zaka jima anan, ko zaka bini gidanmu?"
Kallonta yayi kamar wani babba yace "Me yasa? Ban sanki ba fa."
Murmushi ta masa ta nuna masa class d'in dake kusa da tasu tace "Ga class d'inmu nan, sunana *Khairat Aji Sugui*."
Da mamaki ya sake kallonta yana murmushi yace "Lah, sunan kakanmu d'aya, ni kuma ga class d'inmu nan, sunana *Amjad Tagur Sugui*, ke ma Abanki batube ne?"
Juya harshenta tayi cikin tubanci tace "A'a, Ayyata ce, gaskiya naji dad'i, zaka bini gidanmu?"
Jim yayi sai kuma yace "Ayyata ta hana ni tsallaka ko da t**i ne idan ba ita ta zo ba, bana so na b'ata mata rai."
Cike da yarinta tace "Me yasa Abanka shi baya zuwa d'aukarka?"
Da sauri ya girgiza kai bai ce komai ba, mik'ewa tayi tana gyara zaman jakarta a bayanta tace "Kaga ina da kud'i, kuma basu da yawa bare mu raba kowa yaje gida, amma ka zo muje gidanmu in muka je sai driver ya kaika gida, amma karka zauna anan kai kad'ai kaji."
Kallonta yayi yana jujjuya kalamanta, shawara ce mai kyau ta bashi kam, jinjina kai yayi ya mayar da littafinshi a jaka ya goya ya tashi, a hankali suke tafiya suna hirarsu ta yara har suka k'arasa bakin k'ofa, mai gadi na ganinsu yace "Ina zaku ba'a zo d'aukarku ba?"
Amjad ne yace "Obdo (kawu) adaidaita zamu shiga mu koma, idan naje gida zan kira Ayya saina fad'a mata na koma gida."
"Ka tabbata?" Cewar mai gadi, d'aga masa kai yayi alamar eh, hannunsu ya kama duka yace "Muje to na tsayar muku da mai adaidaitar."
Bakin t**i suka k'arasa suka samu adaidaita, saida suka shiga yaga tafiyarsu sannan ya koma bakin k'ofa.
Sun d'an jima a hanya dan can nesa suke, a k'ofar gidan da suka rsaya yasa Amjad kallon gidan gabanshi na fad'uwa, gidan ya had'u k'arshen had'uwa, suna shiga ciki b'angare biyu ne sai wata k'ofa kuma da zaka bi ka isa wani falon mai zaman kansa, shiga sukayi inda Amjad ke ta doka sallama har suka shiga falon.
Ita kad'ai ce a gidan da alama bayan mai gadi da suka wuce da wani mutum na wanki, ganinsu yasa ta zaro ido tana fad'in "Khairat, ya na ganki kuma? Ba'a karatun ne?"
Cire kallabin kanta tayi ta cire jakar ta jefar a k'asa ta k'arasa gareta tace "Ba ayi Ayya, shiyasa muka dawo."
Sunkuyawa Amjad yayi ya d'auke jakarta da kallabin ya aje saman kujera ya kalli matar, ba zata wuce tsarar mahaifiyarsa ba, sai kawai ya zauna k'asa yana fad'in "Legye?"
Da sauri ta kalleshi da mamaki, kallon Khairat tayi tace "Khairat waye wannan? D'an makarantarku ne shima na ganshi da tenue (uniforme)?"
D'aga kai tayi ta nufi wajen fridge dan d'aukar ruwa, kallon Amjad ta sake yi tace "Lagye?" Cernuma wuna (me ye sunanka)?"
Da murmushi cike da kunya yace "Amjad."
Kallon kayan Khairat tayi daya d'auke mata, kallon Khairat tayi dake d'aukar ruwa tace "Kinga yanda ake yi ko? Abinda nake fama dake kenan kullum."
Kallon matar yayi yana murmushi yace "Dada, idan kina so ta gyara ta dinga d'aukewa ki daina d'auke mata, wani lokacin ma ki takasu da k'afarki zaki ga taji zafi ta d'auke, to gobe ko ta jefar zata dawo ta d'auke dan kar a taka mata kaya."
Da wani tsadadden murmushi ta tara masa hannu tace "Zo nan Amjad." Mik'ewa yayi yaje gareta yana shirin sunkuyawa ta rik'eshi, rumgumashi tayi a jikinta tace "Ka koyar dani darasin da zan bi da yarinyar nan, ina mamanka?"
Saida ya sauke ajiyar zuciya saboda k'amshin turarenta daya shak'a kafin yace "Dole yanzu Ayyata tana kotu."
Waro ido tayi tace "Ayyanka lauya ce?"
D'aga kai yayi alamar eh, jinjina kai tayi ta sake shi tana fad'in "Bari na samo maka abinci ko."
Da sauri ya girgiza kai yace "A'a Dada, na k'oshi ai bana jin yunwa."
Jinjina kai tayi tace "Shikenan, amma anjima zaka ci."
Da sauri ya kalleta yace "A'a Dada, ina so na koma gida dan na kira Ayyata na fad'a mata ina gida, yau na mata laifi dole na nemi afuwarta, bata so ina fita daga cikin makaranta, amma yau gashi na fito har na zo wani wuri."
Kallon k'auna ta ma yaron, ko ma wacece mahaifiyarshi tasan tayi k'ok'ari wajen tarbiyarshi, taji tana son sanin mamanshi har tayi k'awance da ita, ko ba komai zata k'aru dan alamu ya nuna mutuniyar kirki ce, wayarta ta d'auka tace "Kira Ayyaka saika fad'a mata."
Girgiza kai yayi yace "Dada ina kira da lambar da bata sani ba kuma taji muryata, ba zata tsaya saurare na ba zata shiga tambayata, hankalinta zai tashi saboda bata da kowa sai ni."
Murmushi tayi tace "Idan na fahimta dai yaron nan yana matuk'ar son mamanshi."
Dariya yayi yace "Fiye da yanda take so na."
Hararan wasa ta mishi tace "Anya kuwa zaka so ta fiye da yanda take son ka?"
Kallonta yayi yace "Zan iya mana, ita nake gani kullum, da ita na bud'e idona kuma da ita nake gauraya numfashi na kullum."
Kallon Khairat tayi dake dhan ruwa tace "Ke baki iya bawa bak'o ruwa ba?"
Mik'ewa tayi ta d'auko mishi ta kawo tana fad'in "Ayya ina su Haja?"
A tak'aice tace "Suna justice (kotu)"
Juyowa tayi daga can tace "Ayya saida suka tafi? Har da kawu ma?"
"Har dashi mana, ai shine gayyar tafiyar ma."
Da sauri ta dawo a tare data d'auko ruwan ba ta zo ta kama hannun Amjad tana fad'in "Yawwa fad'awa Ayyata sunanka da sunan Abanka, Ayya bari kiji sunanshi."
Duk ido suka zuba mishi, rarraba ido ya fara yi shi kuma saida *Aisha* tace "Fad'a min naji."
A hankali cikin rawar murya yace "Amjad Tag..ur Sugui."
Da k'arfi ta dafe k'irjinta da taji ya doka mata da sauri, zaro ido tayi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, d'ansa ne kai? D'an Tagur ne kai?"
Duk tsoro ne ya kamashi sai yaja baya kad'an kamar zaiyi kuka yace "Haka dai Ayyata ta fad'a min, amma ban san komai akan Abana ba, dan Allah Dada kisa a kaini gida."
Mik'ewa tayi tsaye ta nufeshi da sauri ya sake ja baya yana neman yin kuka, durk'ushewa tayi ita ma tana kukan tace "Tsaya Amjad babu abinda zan maka, ni sunana Aisha amma anfi kirana Aisho, dan Allah fad'a min sunan Ayyanka."
Cike da rashin yarda yace "Fatima." Ya fad'a mata hakane dan kaf garin nan da Faduma suka santa, yasan kafin a fahimci wa suke nufi da Fatima zasu wahala, dab'ar ta k'arasa yin zaune tace "Lallai kai d'an Faduma, kamanin mahaifinka da yarenka sun tabbatar min da haka, tabbas kai d'an d'an uwa na ne."
Kallonshi tayi tace "Amma ina mahaifin naka? Ka tab'a ganinshi?"
Wani kallo ya mata yace "Ya rasu, idan mutum ya mutu kuma ba'a ganinshi."
Da wani mamaki ta kalleshi, ya mutu kuma? Abinda ta fad'a masa kenan! Ba zata k'aryata ta ba dan ko ita aka ma abinda aka mata abinda zatayi kenan, murmushi ta k'ak'aro tace "Amma ko a hoto baka tab'a ganinshi ba?"
Girgza kai yayi, mik'ewa tayi tana share hawayenta tace "Kana so ka ganshi?"
Da sauri ya d'aga kai alamar eh, juyawa tayi ta d'auki wayarta ta shiga dannawa, ba jimawa ta matsa kusanshi tace "Zo ka ga Abanka, kana kama dashi sosai."
Matsowa yayi a hankali, karb'ar wayar yayi daga hannunta ya sauke idonshi akan kyakyawan mutumin, wani irin ziiiiiiii yaji abu na ratsashi yana gauraye jinin jikinshi da mamaye zuciyarshi, da sauri sauri yaji zuciyarshi na harbawa, take k'walla ta cika mishi ido, murmushi ya saki a hankali ya furta " *Aba na*"
Kallon Aisho yayi hawayen na saukowa kan kumatunshi yace "Shine Aba na? Wacece ke?"
Nuna kanta tayi tace "K'anwarsa ce ni, ni nake bi masa, ubanmu d'aya dashi, nan gidansa ne nima ina zauna ne saboda mun rabu da mijina, kuma bana da kowa daya fisu shiyasa."
Sake kallon hoton yayi yace "Amma me yasa Ayya ta bata da hotonshi?"
Kasancewarta uwa yasa tace mishi "Ayyarka tana son Abanka sosai, ba zata juri ganin duk wani abu daya shafe shi ba, hakan zai sa ta dinga zama a cikin damuwa, ina ga shiyasa ta rabu da komai nashi."
Ajiyar zuciya ya sauke yana ci gaba da kallon hoton, kamar yanda mahaifiyarshi ke duhun fata ba sosai haka shima fatarshi take, amma da alama akwai tsafta da kula da jiki, ga wani saje daya keyawa hab'arshi bak'i wulik dashi, maysakaitan idonshi masu sirkin ja da yalwar gashin girar ido.
Murmushi ya saki dan shi ma duk da yana yaro yasan kama da mutumin nan ne yayi, kallonta yayi yace "Dada kisa a kaini gida dan Allah, bana so Ayya taje bata same ni ba."
Jinjina kai tayi tace "Shikenan, muje sai nasa dreba ya kai ka, da zan so na kaika da kaina, amma Ayya ta bar min gida na kula dashi."
Jinjina kai yayi ya mik'a mata wayar, karb'a tayi tana fad'in "Kana son hoton Abanka?"
D'aga kai yayi yace "Ina so nayita kallonshi?"
Murmushi tayi tace "Shikenan, insha Allahu yau zan sa a wanko maka shi saina ba Khairat ta kai maka."
Murmushi yayi shima ta shiga d'aki d'aukar makullin mota ta ba dreba, bin bayanta Khairat tayi wacce ba sosai ta fahimci hausar ba dan hausa ce sukayi ita kuma tafi jin tubanci sosai, tana shiga tace "Ayya, d'an Obdo Tagur ne?"
Jinjina mata kai tayi tace "Eh Khairat, amma ki min alk'awarin ba zaki fad'a masa Abansa yana raye ba, kinji?"
Baki bud'e da mamaki tace "Lah Ayya! K'arya?"
Girgiza kai tayi tace "Ba k'arya bace, zan fad'a masa amma ba yanzu ba."
Jinjina kai tayi sai kuma tace "To in fad'awa Haja?"
Girgiza kai ta sake yi tace "Karki fad'a, nace miki ni zan fad'a ko."
Jinjina kai kawai tayi ta d'auki makullin ta fita, tare suka fita farfajiya ta ba dreba ta nuna mishi Amjad tace "Ka kaishi gida dan Allah, yasan gidan sosai zai nuna maka."
Da girmamawa ya karb'a yana fad'in "To Hajia, muje ko?" Ya k'arashe da kallon Amjad, d'aga musu hannu yayi sai Aisho da tace "Ka gaida min Faduma kaji, ka ce Aisho tana gaisheta."
Jinjina kai yayi suka nufi wajen mota biyun dake wurin, da kallo ta bisu har mai gadi ya bud'e musu k'ofa suka fita, ajiyar zuciya ta sauke tace "Da mahaifinka baiyi waccen kuskurenka ba da girmanka ya kai a dinga tuk'aka cikin mota irinsu benz, hilux, honda da sauransu."
_______________
Tana tayar da motar kwana ta shiga ta tsaya daidai katangar wata makaranta a baya, had'a kanta tayi da sitiyarin motar ta fashe da kuka sosai, kuka take sosai da bubbuga kanta akan sitiyarin, ji take kamar ta kashe kanta ta huta, ba zata lamunci jin sunan Amjad daga bakinshi ba, ba zata so ta zama mak'aryaciya a idon d'an data haifa ba, ba zata tambayi yanda akayi Atta tasan tana da d'a ba tunda har ta ganta tare da Hindu, rashin kunyarshi dai take jinjinawa da har yake iya kallonta wai yace ina d'anshi? Ta jima nan tana kuka kafin ta tayar da motar ta k'arasa makarantar su Amjad, ganin da sauran lokaci yasa ta ciro wayarta ta kira Aminu, yana ganin kiran ya d'auka yana fad'in "Wayyo Faduma ki gafarceni dan Allah, wallahi na so kiranki naji yanda shari'ar nan ta wakana, amma ina bureaux Alhaji ya kirani na zo shago duba wasu kaya da ake sauke masa."
Da k'yar cikin dakusashiyar murya tace "Ba komai, yanzu kana shagon ne?"
Cikin nutsuwa yace "Eh ina shago, amma yanzu za'a gama saina koma."
Numfashi ta sauke tace "Zaka iya samu na gida Aminu?"
Cikin sanyin jiki yace "Muryarki ba yanda na saba jinta bane, Faduma ina fatan mutumin nan baya dawo rayuwarki bane dan ya sabunta zubar da hawayenki, me ya faru kuma yanzu?"
Saida ta lumshe ido wasu hawayen suka fito kafin tace "Ba komai, idan da hali ka zo gida dan Allah zamuyi magana."
Cikin tsananin damuwa da kulawa yace "Fadumaaa! Shikenan zan zo insha Allah da nayi sallah azahar."
"Shikenan." Ta fad'a tana yanke kiran.
*Yawan sharhi yawan rubutu*