"Ayya, wai wa nake gani hakane? Kamar Faduma?"
Ita ma cikin firgicin daya fi na Gomboy tace "Nima dai abinda nake gani kenan? Duba mana da kyau."
K'anwarsa dake danna wayarta hankali kwance kallo d'aya ta mata tayi k'asa da kanta ta tana fad'in "Ita ce, baku ganeta bane ko me?"
A tare suka kalleta sai dattijuwar da tace "Ke *Rahila* da gaske? Ya naga ta canza haka kamar ba ita ba?"
Haushin tambayar yasa ta jan d'an guntun tsaki tace "To dama zata zauna nan ne babu ci gaba? Shekara nawa kukayi rabon da ku ganta."
Muryar Tagur d'in ne ta katse musu maganar da cewa "Muje."
Da sauri ta *Hatimi* ta kalleshi tace "Kai Tagur da gaske Faduma ce can na gani?"
Saida ya bi inda ta nuna da kallo sannan ya kalleta yace "Eh Ayya, ita ce."
Baki bud'e ta shiga jinjina kai tana fad'in "Lallai duniya, yanzu Faduma ce ta wuce ta gabanmu ko kallon arzik'i babu bare gaisuwa."
Ajiyar zuciya ta sauke tana sake rik'e jakarta da kyau, Rahila ce tace "To Ayya me kika mata na alkairi da zaki samu wannan girmamawar daga gareta bayan rabuwarku?"
A hassale ta kalleta tace "Ke bana son iskanci, ki rufe min bakinki kinji ko."
Gomboy ce tace "Ki rabu da ita Ayya, kinsan dama ko acan ita yar tsagin Faduma ce ai, watak'ila asiri ta mata kuma har yanzu bai sake ta ba."
Harara ta dalla mata tana fad'in "Aikin kenan, komai sai kince asiri, shikenan ke babu abinda ke iya tasiri a tare da d'an adam saida sihiri? Mtssss!"
A hassale tayi kanta kamar zata kai mata duka tana fad'in "In ban ci uban..."
Bata k'arasa ba saboda kallon da Tagur ya musu, duk da a gaba take dashi da shekara d'aya, amma kasantuwarshi ya amsa sunan namiji yasa bata haye mishi, tana shakkarshi yana mata kwarjini sosai kamar shi ke gaba da ita, jinjina kai tayi tana jan k'wafa tayi baya tana hararenta. Kallonshi ya mayar kan Rahila yace "Kar na sake jin bakinki a wurin nan, marar kunya kawai."
Hatimi ce tace "To me ya kawota nan?"
Saida ya tunkari shiga yace "Ni na d'aukota aiki." Da mamaki suka shiga kallon juna, suna son k'arin bayani amma babu mai basu.
Wuce yayi suka rufa masa baya sai Hatimi data rik'e hannun Gomboy tana fad'in "Kiyi hak'uri ki k'yaleta har kuje gida, da kaina zan baki tsumagiya ki zaneta."
Ba tace komai ba sai kumburo baki da take, ita kuma Hatimi fushin nata ne bata son gani, 'ya'yan kishiyarta ne data rasu ta barsu a hannunta, su biyar ne duka mata Tagur kad'ai ke namiji, da yake Gomboy ce ta tashi a hannunta shiyasa tafi sonta a cikin yaran, tafi shak'uwa da ita fiye da yanda ta shak'u da nata yaron data haifa a cikinta.
Suna daf da shiga taji an kira sunanta da "Trozzonur (K'awata)."
Da sauri ta waiga b'angaren da taji muryar Atta, da sauri ta k'arasa da murnar ganinsu, tana k'arasawa ta kallesu tace "Trozzonur har kun iso kenan?"
Saida Atta ta kalli Hatimi da ita ma take kallonta da mamakin fitsararta yanda take kallonta cikin ido, ko ba komai dai a tsakaninsu yanzu ai ta auri d'anta, amma wai tana kallonta ido cikin ido babu gaisuwa, tab'e baki Hatimi tayi ta shige, hararar da Atta ta banka mata tana jan tsaki Rahila ta gani, zata nufi kanta cike da masifa Hatimi ta juyo tace "Ke muje."
Juyawa tayi ta kalleta hakan yasa ta jinjina kai tana cije leb'e, amma ta sani bashi ta ci kuma zata biya. Kallon Gomboy tayi tace "To me zamu jira?"
Zaleeha ce tace "Amma sai naga shegiyar lauyar can a gabanku, ina fata dai ba tare da ita kuke ba?"
Juyawa tayi ta kalli k'ofar shiga sannan ta sake kallon Zaleeha tace "Wai Faduma kike nufi?"
Hindu ce tace "Kin ma santa kenan?"
Da murmushi a fuskarta tace "Na santa kuma? Farin sani ma."
Kallon Atta tayi tana yamutsa fuska tace "Ai tsohuwar budurwar mijinki ce wacce ya so aura suka rabu."
Duk zaro ido sukayi suka kalleta, baki hard'ewa Zaleeha tace "Tagur dai?"
D'aga mata gira tayi alamar eh, tab'e baki Hindu tayi tace "Humm-umm! Da gaske wai ko wasa?"
Had'e gira tayi tace "Ya zan muku wasa a yanzu? Kunga ku zo mu shiga."
Da sauri Atta ta rik'e hannunta tana fad'in "Ke tsaya dallah, da gaske wai ita wacce naji ana fad'a sunyi soyayya har an saka musu rana?"
Cike da tabbaci tace "Wallahi ita ce, Faduma ba."
Zaleeha ce tace "Yo me yasa bai aureta ba?"
Sake tab'e baki tayi tace "Ke sharri fa ta masa, cewa tayi tana da ciki har da kawo iyayenta gidanmu, shi kuma yace bai yarda ba k'arya ta masa, shine aka fasa auren kowa ya kama gabansa."
"La'ilaha illalahu, Muhammad rasulullih sallalahu alaihi wasallam." Atta da Hindu suka fad'a a tare, Hindu ce ta d'ora da fad'in "Shi d'in ne yace k'arya ce?"
D'aga kai tayi tana kallon Atta da ita ma ta jefo mata magana da cewa"Shima ashe d'an iska ne shine harda cewa wani wai ya gane ni yar iska ce? Amma dai wallahi baya da mutumci."
Tsaki tayi tace "Kunga ku zo muje dan Allah." Ta fad'a tana wucewa, har Atta zata bi bayanta Hindu ta rik'o hannunta tana fad'in "Ke tsaya."
Tsayawa sukayi suna kallonta, cikin rad'a tace "Nifa ina tunanin anya kuwa yaron nan na Faduma ba shine d'an data haifa ba."
Zaro ido Zaleeha tayi sai kuma ta k'ank'ancesu tace "Kuma fa biri yayi kama da mutum, tabbas zai iya yiwu wa, duba da ai ba yanzu bane abun ya faru."
Jinjina kai Atta tayi tace "Ashe haukan banza nake, ina ganin na hifi yaron da zai cinye dukiyarshi, ashe yana can da gabjejen yaro wanda ya haifa a yawon ta-zubar d'inshi."
Cike da masifa Zaleeha tace "Kai amma maza bakuyi ba wallahi."
Kama hannunsu Hindu tayi suka shiga ciki tana fad'in "Dama sun fad'a miki sunyi ne? Ai mu dasu kallon kallo ne, k'iris ya rage mu fara musu jifar shed'an."
Kowa ya samu wuri ya zauna shigowar alk'ali ake jira, duk hangenta suke ita yi duk da yanzu ta cire lafayarta ta d'ora rigarta ta lauyoyi da hularta, hayaniya ake tayi ko da alk'ali ya shigo ta k'ofar gabansu duk aka mik'e dan girmamawa, saida ya zauna kowa ya koma ya zauna ana kama jiki tare da yin shiru. Magatakarda ne ya fara aikinsa ta hanyar shelanta rana mai k'ara da wanda ake k'arar, alk'ali ne ya bayar da izinin lauyoyi su gabatar da kansu, namijin ne ya fara gabatar da kanshi kafin Faduma.
Shi aka ba dama ya fara gabatar da abinda kenan, saida ya kira Tagur ya masa tambayoyi kafin ya nunawa kotu yaron ya cancanci ya zauna wajen mahaifiyarsa duba da k'arami ne wanda komai sai an masa. Saida ya gama alk'ali ya bata dama ita ma ta mik'e, hannayenta a had'e tana mummurzasu ta kalli alk'ali tace "Ya mai shari'a ina neman alfarmar kotu data gabatar min da malama Atta?"
Coke da dattako yace "Kotu ta baki dama." Magatakarda ne ya mik'e yace "Malama Atta Angr Shilli ta fito."
Mik'ewa tayi ta isa inda ake tsayawa ta tsaya tana kallonta, cikin yatsina fuska da dubara ta tab'e baki a ranta tace "Hummm!"
Maysawa tayi kusanta tace "Malama Atta lafiyarki k'alau?"
Cikin jin haushin tambayar ta harareta ta wutsiyar ido tace "Eh, k'alau nake."
Lumshe ido tayi ta d'ora da cewa "A gidanku nawa ke rayuwa?"
Idonta cikin nata tace "Mu biyar ne, ni da mama da baba na sai yayuna biyu maza."
Da murmushi tace "Kina aiki ne na gwamnati ko wata sana'a?"
Kai tsaye tace "Bana yi?"
D'an sosa gaban goshinta tayi tace "D'anki Ridwan lafiyarsa k'alau?"
A hankali tace "A'a, yana da asma."
Jinjina kai tayi tana wani murmushin mugunta tace "Malama Atta kinsan da cewa me yasa ba kya sana'ar komai? Ko kinsan cewa kotu ba zata d'auki yaro ta baki haka kawai baki da abinda zaki rik'eshi?"
Da sauri kuma kamar wacce ta tuno wani abu sai tace "Au! Yi hak'uri fa, na manta yaron yana da gara ashe."
Kallon alk'ali tayi tace "Ya mai shari'a, ina neman alfarmar kotu ta gabatar min da malam Tagur?"
Ba b'ata lokaci shima ya hallara gabanta, bata yarda ta kalli idonshi ba, dan sosai take jin ta takura sakamakon kallon da yake mata, saida ta tsaya gabanshi tace "Malam Tagur me yasa kake son karb'ar yaronka a hannun matar da kuka d'auki tsawon shekara shida a tare? Shin baka yarda da ita bane? Ko kuma baka so d'anka yayi nisa da kai ne?"
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Duka biyun."
Kallonshi tayi tace "Duka biyun kamar ya? Ka fad'awa kotu dalla dalla."
Lumshe ido sukayi a tare, hakan yasa sukayi saurin sakin sautin gyaran murya shima a tare "Egyhemm!"
Da sauri suka kalli juna sai ita da tayi nasarar yin k'asa da nata idon, numfasawa ya sake yi yace "Ban yarda da kalar tarbiyar da zai samu a wajenta ba, sannan ina son ya zauna tare dani dan zaifi samun kulawa."
Cikin motsa hannayenta da kwatance dasu tace "Shin akwai wani hali ne da take yi wanda kale ganin d'anka zai iya d'auka?"
D'aga kai yayi alamar eh yace "Gaskiya ne." Jinjina kai tayi tace "Wane irin aiki kake?"
Saida yayi k'ok'arin saka idonshi a nata yace "Ni d'an kasuwa, kuma d'an kwangila."
Saita ta langab'ar da kai tace "Kana yawan tafiye tafiye ba?"
D'aga kai yayi yace "Gaskiya ne?"
"Kamar ina da ina kenan?"
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Kamar China, France, Africa ma ina zagayawa sosai."
Matse baki tayi tace "Tsawon wane lokaci kake d'auka kafin ka dawo?"
Iska ya feso yace "A k'alla wata d'aya ko sati uku."
"Kasan yaronka na da asma chronique?"
"Na sani, kuma ina bashi kulawar data dace ta b'angaren maganin daya dace dashi."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Zan iya sanin rukunin jininka?"
Kai tsaye yace "AB+."
"Shin ka tab'a wata rashin lafiya data sa aka maka k'arin jini?"
Girgiza kai yayi alamar a'a, jinjina kai tayi tace "Kenan baka tab'a doguwar jinyar data kwantar da kai ba?"
Jim ya d'anyi kafin yace "Na tab'a yi, amma shima had'ari ne nayi a mota."
Kallonshi tayi kamar kallon tana neman inda yaji ciwo tace "Wane lokaci ka d'auka a asibiti?"
"A k'alla wata hud'u."
"Duk tsawon lokacin ne su waye ke kula da kai? Ko kuma ba ka hayyacinka baka san me ke faruwa ba?"
Girgiza kai yayi yace "Na sani, wanda suke tare dani kullum yan uwana ne sai kuma mahaifiyata, sai kuma abokina dake yawan zuwa duba ni."
Jinjina kai tayi tace "A rahoton rashin lafiyar babu bayanin wani had'ari ko matsala?"
Girgiza kai yayi yace "Gaskiya babu, da akwai kuma nasan da an bamu rahoton."
Tarrr ta sauke ido cikin nashi da murmushi tace "Nagode, zaka iya zama."
Kallon mai shari'a tayi ta sake neman alfarmar a gabatar mata da Hatimi, tana zuwa ta kasa d'auke ido a kanta ita mamaki ma take bata, sai kuma tsoronta da wani kwarjini da taji yarinyar ta mata, kamar ba ita ce yarinyar nan mai shekaru *sha hud'u* wacce suke ganin tayi k'ank'anta da zama matar d'ansu.
Kusan tambaya akan had'arin da yayi ne ta mata har ta tambayeta "Kina nufin har ranar da za'a sallameku babu likitan daya buk'aci ya ga wani? Ko kuma ya bayar da wata takarda ko da ta siyan magani ko? Ko irin yace wani ya zo zai fad'a mishi yanda zaisha maganinshi?"
Shiru tayi tana tunani sai kuma tayi saurin cewa "Na tuna, a ranar dai yace yana son ganin d'aya d'aga cikinmu da zasuyi magana, sai abokinshi *Omar* ya tafi tare da yar uwarshi Gomboy."
Wani shegen murmushin ta saki jin ta kawo inda take son kawowa, kallonta tayi tace "Me ya fad'a musu kenan?"
Girgoza kai tayi tace "A gaskiya babu wanda ya fad'a mana, dan suna fitowa ma Omar yace yaje ya siyo magani, gomboy kuma ta dawo da takardar sallamar."
Cikin jin dad'i da tsaiko tace "Hakan na nufin Gomboy ce kad'ai zata iya fad'a mana me ya faru a d'akin ko?"
Da sauri ta d'aga mata kai, da wani irin murmushi ta juyo ta kalli inda Gomboy ke zaune tuni jikinta ya d'auki ruwa sai zufa da take.
Tana kallon alk'ali duk da ido suka yi zaurance magatakarda ya mik'e ya kirata, wani irin tari suka ji da k'arfi sosai hakan yasa duk wanda ke kotun aka juya inda aka ji tarin, Zaleeha ce ke wannan tari da iya k'arfinta kamar ta k'ware, duk'e kanta tayi cikin dubara ta rufe bakinta da gyale tace ma Hindu da Atta dake kusanta "Wallahi fita zanyi, wannan tonon asirin ba za'a yi shi dani ba na tsaya ana nuna ni ana cewa ni ce k'awarki, shegiyar yarinyar can saita tono mana wuk'ar yankanmu wallahi."
Ganin Gomboy ta taso yasa Faduma juyawa tana kallon takardun dake gaban table d'in data tashi, sulalewa Zaleeha tayi ta k'asa ta fita babu wanda ya hanata.
Kallon kallo akayi tsakanin gomboy da Faduma, takawa tayi a hankali hakan ya haifar da bayar da sautin takalminta k'was k'was har ta k'arasa gabanta, numfashi ta sauke tace "Malama gomboy ko?"
D'aga kai tayi alamar eh, jinjina kai tayi ita ma tace "Ke ce a gaba da Tagur Sugui ko kuma shi ne a gaba dake?"
Cikin nutsuwa tace "Ni ce babba, amma duka shekara na bashi."
Jinjina kai tayi tace "Cikinku d'aya dashi?"
Cikin had'e fuska tace "A'a, Abanmu ne d'aya, amma ni kamar ciki d'aya muka fito haka nake gani."
Jinjina kai ta sake yi tace "Kina da aure ne?"
"A'a." Yanda ta fad'i maganar da k'arfi zai tabbatarwa da mai sauraro ta hassala, bata damu ba sai d'orawa da tayi da "An ce kina d'aya daga cikik biyun kuka amsa kiran likita a waccen ranar, dan Allah zaki iya fad'a mana abinda kuka tattauna?"
Kamar zata rufeta da duka ta kalleta tace "Shari'a ake akan yaro fa ba jin abinda ya shafi iyayen ba."
Wani murmushi tayi tace "Amma yaron ba daga iyayen ya fito ba? Dole mu tabbatar da sahihancin lafiyarsu dan musan wanda ya dace ya rik'e shi."
Cikin jin haushi ta kalleta tace "Kawai ya bamu shawarwari ne akan yanda zamu k'ara kula dashi, sai magunguna daya ruba Omar yaje ya siyo."
D'an had'e fuska tayi tace " Malama Gomboy, ya kamata ki tabbatar duk abinda zai fito daga bakinki gaskiya kike fad'a."
Cikin d'aga murya tace "Me kike nufi Faduma? Har yanzu kina jin haushi na ne?"
Kallon mamaki ta mata tace "Akan me kike magana? Karki nemi canza mana maudi'unmu, kina bani amsa me kuka tattauna da likitan?"
"Gaskiyar kenan." Ta fad'a tana d'auke kai daga kallonta, juyawa tayi wajen alk'ali tace "Ya mai girma mai shari'a abinda malama gomboy take fad'a a yanzun sam bai zo daidai da wanda shi likitan ya bamu rahoto ba, idan kotu ta min izini zan gabatar da rahoton lafiyar malam Tagur wanda na same shine a hannun likitan daya duba shi, wanda ba dan aiki ba ma na so ya zo kotun amma bai samu dama ba."
Da hannu cikin dattako yace "Bismillah."
Sunkuyawa tayi alamar girmamawa ta nufi gaban table d'in, d'aukar takardar tayi a jakar ordi. d'inta ta k'arasa kusa da magatakarda ta bashi, mik'ewa yayi shima ya juya ya ba alk'ali ya koma ya zauna, yana cikin duba takardar ita kuma cikin d'aga murya tace "Ya mai shari'a wannan rahoton yana d'auke da jinyar da yayi da kuma wata matsala da shi likitan ya fad'a mana sun d'auki tsawon wata biyu suna son shawo kanta amma Allah bai yi ba, daga k'arshe dole basu da wani zab'i daya wuce su fad'a musu abinda ke faruwa, gomboy tana daga cikin wanda likitan ya fad'a ma cewa sakamakon k'arfen daya sokeshi a mara ya tab'a wasu jijiyoyinshi da suke iya isar da maniyi zuwa inda ake buk'ata har ya shiga ta gaban mace ya isa mahaifa, hakan kuma yasa inhar ba wani ikon Allah ba to malam Tagur ba zai iya haihuwa ba har sai in k'asar waje ya fita, kuma a cikin bayanan daya bamu bai fad'a mana yayi wata jinya ba da har ya fita waje bayan kasuwancinshi."
Sausauta murya tayi tace "Idan kotu na buk'ata zan iya samun lokacin likitan dan ya gabatar da kanshi da kuma tabbatarwa, amma a zahirin gaskiya wannan shine abinda ya faru, kuma yar uwarsa ta sani amma duk alamu sun nuna daga shi kanshi har mahaifiyarshi bata fad'a ma kowa ba, idan har zata sauk'ak'a mana to ya kamata ta gasgata abinda na fad'a da kuma rahoton nan, ba abinda muke magana akai bane bare mu tirsasa malama Atta ta fad'a mana Ridwan *d'an waye*, sai dai mun san malam Tagur ya barranta daga yaron nan Ridwan, baya da wata alak'a dashi ta nesa bare ta kusa."
Ahiyar zuciya ta sauke tace "Nagode mai shari'a." Komawa tayi kan table d'in ta zauna, kururuwar da kotun ta d'auka yasa ta dafe gaban goshinta, wasu matasa ne daga can baya d'aya yace "A tirsasata ta fad'a mana d'an waye? Macuciya kawai."
D'aya ne yace "Da tasan wuk'ar yankanta zata tono da bata kawo k'arar ba ai."
Cikin tashin hankali da fitar hayyaci Atta ta daka ihu tana fad'in "K'arya ne, wallahi k'arya take sharri ta min d'an shi ne."
Gomboy ma dake ta firfita da bakin mayafinta ne tace "Eh k'arya ta fad'a, saboda akwai wani abu tsakaninsu ne."
Duk babu wanda ya ankara sai ganin Tagur sukayi ya shak'i wuyan Faduma ta baya da hannu biyu, mik'ewa tayi tana k'ok'arin b'amb'are hannayensa duk ta rufe idonta tana son yin tari amma ya shaketa sosai yana fad'in "Abinda ya faru tsakaninmu har yanzu baki manta ba shine zaki rama, kamar yanda na kunyata ki a waccen ranar shine ke ma zaki kunyata ni a bainar jama'a? D'ana na sunna da shi kad'ai nake da zaki nuna banda alak'a dashi ta nesa bare ta kusa? Za..."
Lauyan Atta da magatakarda ne suka kama shi da k'yar suka rabashi da ita, da k'yar alk'ali ya samu suka nutsu akayi shiru bayan ya gama bubbuga table d'in gabanshi da guduma, saida wurin yayi shiru cikin fad'a alk'ali ya kalli Tagur dake ta huci yace "Abisa tozarta lauya da yi mana hauka a kotu zaka biya tara tare da kwana d'aya a gidan yari domin horo, dan a kiyaye gaba."
Faduma da har yanzu hannunta ke kan wuya tana shafawa sai numfashi take saukewa, ita kam ba tayi mamaki ba dan tasan waye shi. Muryar alk'ali suka ji ya kalli Gomboy yace "Malama gomboy ga rahoton likita nan ya nuna abinda ta fad'a, shin da gaske ne haka ta faru?"
Shiru tayi tana rarraba ido hakan yasa yace "Malama gomboy ki sani kotu bata lamuntar k'arya, za'a iya yafewa wanda yayi hargagi a kotu, sannan ana sauk'ak'a hukunci ga mai laifi idan har ya fad'i gaskiya ba tare da wahalar da kotu ba, amma yin k'arya babban laifi ne."
Hannayenta ta had'e tana murzawa idonta cike da k'walla, cikin muryar kuka tace "Gaskiya ne, dan Allah kuyi hak'uri ku yafe min."
Wani sabon hayaniyar ne ta tashi, saida ya bubbuga table aka yi shiru, Tagur ne ya kalleta har zaiyi magana sai kuma yayi shiru ya cije leb'e ya damk'e kujerar da yake zaune a kai, Hatimi tuni ta fara kuka tana salallami, daga baya Atta ta mik'e tace "Mai shari'a wallahi k'arya suke yi Ridwan d'ansa ne, Faduma ta fad'i hakane saboda tana kishi dani."
Kallonta alk'ali yayi yace "Na k'arshe kenan da zaki sake magana kotu bata baki dama ba, koma ki zauna."
Cikin jin haushi tace "To akan me zan zauna a b'ata min suna? K'azafi ta min saboda ita d'in karuwarsa ce har *d'a* ta haifa masa."
Da sauri ta dafe kanta tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."
Mik'ewa tayi tsaye ta juya ta kalli Atta da tayi maganar, sai kuma taga ba anfanin biye mata ma a kotun kawai, komawa tayi ta zauna sai dai tuni Tagur ya koma kallonta.
Duk yanda abun ake tunaninshi ya wuce nan, kamar kasuwa haka kotun ta zama kowa abinda ke ransa yake fad'a, alk'ali yayi bugun table d'in har ya gaji ya kallesu na d'an lokaci, saida ya ga abun baida niyyar k'arewa ya sake bugawa, da k'yar akayi shiru aka koma kallonshi, ganin lokacin yayi yasa alk'ali cewa "Kotu ba zata ja shari'ar nan ba, amma duk da haka ana buk'atar k'arin bayani daga bakin likitan, dan haka kotu ta d'aga wannan zama zuwa 11/10/20."
*Yawan sharhi yawan rubutu*