Ko da suka isa gida yaran baki bud'e suke fad'a mata "Mama, yau ma mun ga maman abokinmu, kuma tace mu shirya Abbanmu ya kaimu gidanta ita ma saita kawo mana Amjad."
Saida ta nufi t. a manger (d/table) d'in tana aje plate d'in hannunta tace "Wacece kuma hakanan?"
Sharfudeen ne yace "Aunty mai murmushi."
Juyowa tayi dan tambayarshi sai kuma Hasheer ya shigo, kallo d'aya suka wa junansu suka d'auke idonsu, mayarwa yayi a falon ganin yau ya samu gyara daga gareta, sannan yanda ya ga t. a manger d'in ya nuna ta gama abinci, da sauri Izzadeen ya tareshi yana fad'in "Abba ai zaka kaimu gidan aunty mai murmushi ko?"
Shima murmushin ya saki ya d'aga masa kai kawai alamar eh, cikin jin dad'i ya shiga murna sai muryarta da suka ji tace "Je ku cire kayanku ku zo ku ci abinci."
Da gudu suka nufi d'akinsu, yana shirin shiga d'akinshi tace "Zaka ci abinci ne?"
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Me kika dafa?"
Hararan k'eyarshi tayi tace "In ba zaka ci ba ka bari mana."
Juyowa yayi ya kalleta ya d'aga kafad'a alamar shikenan d'in, shigewa yayi d'akin yayi abinda zaiyi ya fito, tana kallo ya fice ya nufi b'angaren Umma, haushi ne ya kamata sosai dan ta b'ata lokacinta sosai wajen girkin nan, in kuma bai ci ba hakan na nuna fa ba zasu shirya yau ba bare ta samu damar samun kud'in ankon bikin k'awarta, tana cikin wannan tunanin yaran suka fito daga d'aki, Izzadeen ne ya matsa yana fad'in "Mama gyara min rigata."
Cikin takaici ta fizgoshi ya fad'a kanta ta shiga k'ok'arin b'alla mishi botir d'in, tana gamawa ta nuna musu abincin tace "Ku zauna maza ku ci."
Zaune sukayi suka shiga cin abincin cike da jin dad'in yau suna cin lafiyayyen abinci daga hannun mahaifiyarsu.
Tunda ya shiga bayan sun gaisa ya zauna yana kallon wayar, yayi nisa sosai Umma kuma na kallonshi ta kasa cewa komai, Mukhtar ne ya fito daga d'akinshi da niyyar fita, ganin Hasheer na kallon waya sai murmushi yake saki yasa shi d'aga murya cikin zolaya yace "Umma ki fara shirin tarban surukarki, dan naga fitilar ta fara kawo haske mai k'yali."
Dariya tayi mai birgewa da nutsuwa tace "Yaushe zaka kawota?"
Saida ya k'araso kusansu yana kallon Hasheer da har yanzu bai d'ago ya kalleshi ya mata alama da ido yana nuna mata Hasheer d'in yace "Baki lura da abinda na lura dashi ba Umma?"
Kallon Hasheer tayi tace "Kai fa yake wa sharri."
Kallonta yayi sai kuma yayi saurin kallon Mukhtar, had'e fuska yayi yace "Lafiya?"
Dariya yayi yana lek'a wayar yana fad'in "In gani wacece?"
Da sauri ya soka wayar aljihu yana fad'in "Mukhtar ina wasa da kai ne?"
K'wafa yayi ya mik'e ya kalli Umma yace "Umma ni zan koma, sai anjima."
Murmushi kawai tayi ta bishi da kallo har ya fita, Mukhtar kuma na ci gaba da dariya da tsokanarshi wai to ya rufe bakin. Yana fita masallaci ya nufa yayi salla, misalin 02:20 ya dawo gidan ya wuce b'angarenshi kai tsaye, yana shiga ya same su sunata wasa a falon amma ita bata nan, zaune yayi yana tambayarsu "Kunyi sallah?"
Kallon juna sukayi sai kuma suka amsa da A'a, umarni ya basu suyi sallah su shirya ya kaisu ***** dan lokaci ya kusa, cikin jin dad'in shi zai kaisu suka tafi a guje dan yin abinda yace. Ya jima zaune yana jiransu kafin daga bisani su fito da kayansu da jakarsu, kallonsu yayi yace "Ina mamanku?"
Nuna mishi sukayi da fad'in "Tana d'aki."
D'orawa yayi da "Kun ci abinci?"
D'aga kai sukayi yace "Me kuka ci?"
Sharfudeen ne yace "Abba shinkafa muka ci da nik'akk'en nama da miya mai dad'i."
Wani murmushi yayi yace "Hum." Mik'ewa yayi yasa hannu aljihu ya fito da kud'i yan goma goma guda uku, mik'awa Sharfudeen yayi yace "Kai wa mamarka."
Da gudu ya juya ya nufo d'akin, yana shiga ya same kwance kan gado da wayarta ta hannu, aje mata kud'in yayi kusa da ita yace "Abba yace na baki."
Da sauri ta zabura ta mik'e zaune tana d'aukar kud'in da fad'in "Na miye?"
D'aga kafad'a yayi yace "Nima ban sani ba yace na kawo miki."
Jim tayi kamar mai tunani sai kuma ta sauko da sauri suka fito, tana ganinshi tsaye yana gyarawa Izzadeen rigarshi ta had'e fuska har ta k'araso, bayanshi ta tsaya tace "Kud'in miye Deen ya kai?"
Yanda tayi maganar murya a cunkushe shima haka ya amsa mata da cewa "Kyauta na baki."
A bazata wani murmushi ya kubce mata dan ba tayi tsammanin kyautar ba, amma da sauri ta basar ta had'e fuska tace "Ba zaka ci abincin bane?"
Ba tare daya juyo ba yace "Alhamdulillah."
Cikin tuhuma tace "Ina ka ci abinci?"
D'agowa yayi ya juyo ya kalleta da mamaki yace "Baki tab'a tambayata ina na ci abinci ba, me yasa yau kike tambaya?"
"Saboda ya dace na tambaya."
Wani murmushi kawai yayi ya juya zai fita, da sauri ta tare gabanshi tana fad'in "Kaga malam tsaya ka fad'a min fa."
Yanda ta tsaya gabanshi yasa shi kallon fuskarta yace "Kau ce min a hanya."
Saida ta girgiza kai tace "Ba zan matsa ba saika fad'a min."
Cikin yamutsa fuska yace "Wai me zan fad'a miki?"
"Inda ka ci abinci." Ta fad'a tana jijjiga, rab'ata yayi zai wuce ta sake shigewa gabanshi, wani dogon tsaki yaja cikin takaici ya daka mata tsawa yana fad'in "Zaki gusa min ko sai na..."
Cije leb'e yayi bai k'arasa ba saboda tuna yaran na tare dasu, kallonta yayi cikin matuk'ar jin haushi ya wurga mata harara ya wuceta, ita kam tunda ya mata tsawar nan ta sunkuye k'asa ta rintse ido, saida taji shiru ta d'aga kai sai taga wayam, mik'ewa tayi ta nufi d'aki tana fad'in "Wallahi zaka dawo ka same ni a gidan, kuma ba zan sake dafa abincin ba saika fad'a min inda ka ci."
________________
Ko da suka je gida sallah suka fara yi kafin suka ci abinci, misalin 02:35 Amjad ya shirya tayi sallama da Dada suka fita, tana aje shi makaranta ta wuce babbar asibiti dan had'uwa da likitan nan. Tayi sa'a kuwa bata b'ata lokaci wajen ganinshi ba, ko da ta sanar dashi abinda ya kawota ya sakar mata fuska sosai, sai dai bai bata takardar data buk'ata ba, wata likita ya had'ata da ita suka tafi tare tayi photocopie takardar ta bata jahun ita kuma ta koma mishi da originale d'in bayan ta sake jadadda mata ta k'ara mishi godiya.
Ko da ta dawo gida tana shiga da sallama ta sale had'e fuskarta sosai sakamakon ganin *Hindu*, sam matar bata mata ba saboda halayenta, kallonta tayi ita ma tace "Sannu Faduma."
"Sannu." Ta fad'a tana zama kusa da Dada, magana bata sake had'asu ba har ta gama siyan turarenta a wajen Dada ta tafi, kallonta Dada tayi tace "Faduma, matar nan bata miki ba ko?"
Saida ta tab'e baki tace "Bata min ba Dada, domin ina ganinta tare dasu Alhaji Sunusi wanda akayi shari'a akan shi waccen satin."
Murmushi tayi tace "Duk da haka Faduma ki dinga sakar mata fuska kuna gaisawa, ko dan hakk'in mak'wabtaka ma."
Sake tab'e baki kawai tayi ta gyara zamanta tana aje jakarta ta kalli Dada da kyau tace "Dada kinsan wa na gani yau? Kinsan wa na karb'i aikinsa yau?"
Girgiza kai tayi lokaci d'aya duk ta zaro ido tace "A'a sai kin fad'a."
Saida ta sauke numfashi ta kalleta yana jinjina kanta tace "Dada Tagur muka had'u dashi yau."
Da k'arfi ta dafe k'irjinta ta k'ara kwalalo ido tace "Wa? Tagur fa kika ce?"
Jinjina kai tayi tace "K'warai Dada, Tagur dai da kika sani."
Ba tare data d'auke hannunta daga k'irjinta ba tace "Dama yana garin nan ne? Ya akayi kuka had'u? Me ya had'aki dashi kuma?"
Girgiza kai tayi cike da rashin karsashi ta kora mata bayanin yanda sukayi, ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tayi k'asa da idonta da suka cika da k'walla tace "Dada da nasan yana garin nan dana jima da raba Amjad da k'asar nan ko ta wane hali, bana so su had'u, bana so su san suna da juna, musamman dana fara hango wani tasku na shirin fad'awa akan shi, dan inhar abinda hasashena yake nuna min gaskiya ne, to tabbas matar Tagur ta ha'inceshi, Ridwan ba d'anshi bane."
Ita ma ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tace "Lallai kam, ni kaina da nasan yana garin nan dana jima da had'uwa dashi."
Da sauri ta kalleta tace "Me zaki masa Dada?"
Sama da k'asa ta harareta tace "Godiya."
Dariya tayi wacce ta tilasta zubowar hawayen da suka mak'ale tana girgiza kanta, kallonta tayi tace "Shiyasa har yanzu nake jin farin cikin rashin kasancewarki a wurin a waccen ranar."
Da sauri tace "K'warai, dan da ina wurin a wannan ranar Faduma da yanzu d'anki maraya ne na gaske."
Wata dariyar ta sake yi tasa hannu ta share hawayen, mik'ewa tayi tsaye tana fad'in "Dada gobe ne tafiyata, zan bar Amjad wajenki amma banda k'arfin halin da zan iya fad'a miki cewa na bar miki shi amana ne, dan har ni uwarshi ke kike kula dani, amma bana so ya fita ko ina har zuwa sanda zan dawo."
Jinjina kai tayi tace "Karki damu Faduma, insha Allahu zan rik'e miki amana."
Dafa kafad'arta tayi cike da jin dad'i da murmushi tace "Nagode Dada." Wucewa tayi d'aki ta bar Dada zaune da tunanin ina ma zata ganshi ido da ido? Hummm! Allah kad'ai yasan me zata mishi.
*Zinder*
Jiki na rawa ta d'auki butar ta sunkuya tana zuba mishi ruwa yana wanke hannun, saida ya gama ya mik'e daga sunkuyan da yayi yana murza hannayen, d'agawa tayi tana kallonshi cike da kunya da kuma fargaba, saida ya gama ya shafi fuskarshi cikin harshen tubanci yace "Alhamdulillah, Hadizey ni zan fita, saina dawo."
Saile sunkuyar da kai tayi tace "Malam, dama..." Shiru tayi saboda gabanta dake ta fad'uwa, dafe k'irjin tayi tana jin yanda yale buga mata, a hankali ta shiga sauke numfashi da k'arfi wanda har ya fahimci hakan, kallonta yayi yace "Ina jinki."
Saida ta sake sauke numfashi sau uku kafin ta d'auke hannunta ta sake sunkuyar da kai tace "Dama...na kirata, ta ta..tace tana nan...tafe gobe."
Yanda ta dire maganar da sake wani numfashin zaka san girman abinda ta fad'a a bakinta, ai kuwa yanda tayi tsammani ne wanda zai tabbatar maka da dalilin tsoronta, cikin kwakwazo da hawan kai da sababi kamar yana fad'awa duk wanda ke layin ya shiga fad'in "Hadizey! Ni zaki wanda baisan abinda yake yi ba? Ni ne zan kafa doka nace ga yadda za ayi kice ba haka ba?"
Saida ya gyara tsayuwa ya juya da kyau yana kallonta da nuna ta da hannu yace "Nace ina buk'atarta ne? Ni na fad'a miki ina son ganinta wajen sabgata? Kiyi sauri ki kirata ki fad'a mata karta zo, in kuma ta zo to ke zaki fita ki barta anan."
Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi hawaye har sun wanke mata fuska, da sauri ta durk'usa gabanshi ta had'e hannayenta tana fad'in "Dan Allah malam kayi hak'uri ka min rai, na tuba ba zan k'ara ba kayi hak'uri, ina so naga 'yata ne saboda tsawon lokacin da aka d'auka ban ganta ba, na d'auka dama ce ta zo da zan iya ganinta shiyasa na kirata, amma kayi hak'uri tunda baka so zan fad'a mata ta zauna kar ta zo."
Shiru tayi ganin shima ya juyar da kai sai cika yake yana batsewa, ci gaba da kallonshi tayi tana godiya ga Allah daya sa ba gida d'aya take da kishiyarta ba, duk da basu da nisa amma dai zaka iya sirri akan abinda ya shafeka, sannan ita dama 'yayanta biyu ne kawai, namijin ne babba sai Faduma k'arama. Shirun da yayi shima fa jinjina abun yake, yana son ganinta bayan shekarun nan da aka d'auka, har k'asan zuciyarshi yake sonta da kuma damuwa akan ta, abinda ta masa ne kawai yake b'ata masa rai da hana shi sukuni, amma shekara tara ai ba kwana tara bace, har yanzu ko mai kama da Fadumarsa bai gani ba.
Juyowa yayi ya kalleta yana shan magani yace "Shikenan na hak'ura, ki bari ta zo, amma da sharad'i?"
Da sauri ta sake kallonshi tana mik'ewa tsaye tace "Da gaske? Nagode malam, amma wane sharad'i?"
D'an basarwa yayi yace "Sharad'in shine idan ta zo gobe washe gari ana d'aura aure zata kama hanya ta koma inda ta fita, kin yarda?"
Kallonshi tayi kasak'e sai kuma ta jinjina kai tace "Ba komai na yarda, Allah ya saka da alkairi."
Ficewa yayi kawai komai bai ce ba, da kallo ta bishi har ya fita ta sauke ajiyar zuciya tace "Hakan ma ba laifi angode."
Juyawa tayi zata koma d'aki tana godiya ga Allah da yasa duk wata hidima da ake ta auren nan a gidan uwar gidanta ake yin shi, kasancewarsu kansu a had'e yake kuma suna zaman lafiya, shiyasa ma duk wani abu da uwa ke yi *Herde* ce ke yin shi kamar d'an data haifa a cikinta, shiyasa yanzu ma tafi ta jin zafin rashin Faduma a gidan nan, kuma shekaran jiya ma ita tasa ta kira Faduma tace ta zo, amma ita tana tsoron tashin hankalin mai gidan, shiyasa dan kar ya musu rashin mutumci idan ya ganta ta zab'i ta fad'a mishi ya sani, inhar yace a'a to sai tayi zamanta, yanzu kuma daya amince taji dad'i sosai.
Daf da magriba angon ya shigo da sauri zai shiga d'akinshi da alama akwai abinda ya kawo shi, da sauri ta mik'e daga alwalar da tayi tana fad'in "Kaji labarin zata zo ne?"
Ko da yaji haka yasan wa take nufi, tunda abun ya faru mahaifunsu yayi hushi yace baya son sake jin ko da sunanta a gidan nan, girgiza kai yayi yace "Ayya bana son kisa kanki a matsala, kinsan ran Aba zai b'ace sosai, ki hak'ura mana da zuwanta."
Harara ta dalla masa tace "'Yar tawa kake cewa na hak'ura da ita? To da amincewarshi zata zo."
Da mamaki ya kalleta yace "Ayya da amincewar Abba? Shine ya yarda ta zo?"
D'aga masa kai tayi alamar eh, jinjina kai yayi yace "Lallai Abba ya sauko, amma me kika fad'a masa da har ya sauko da wuri haka?"
Cikin saurin magana da fad'a fad'a tace "Bana son iskanci Barka, idan ba kayi farin ciki ba ka fad'a min saina sa tayi zamanta."
Tsaki taja ta wuce d'aki tana tab'a hujen hancinta daya mata kyau a fuska, bin bayanta yayi har d'akin ya sunkuya yana kallonta tana saka hijab yace "Kiyi hak'uri Ayya, wallahi ina cikin farin ciki sosai, yanda akayi Aba ya amince ne da sauri haka nake mamaki, amma Allah ya huci zuciyarki."
Tsayawa tayi daga saka hijab d'in tana kallonshi ta fashe da kuka mai ciwo ta fad'a kan gadon ta zauna tana fad'in "Barka kafi kowa sanin damuwar da nake ciki, kafi kowa sanin banda buri a yanzu kamar naga *Fadima*, tunda ya koreta a gidan da ciki har yau babu wanda ya sake ganinta, ya ma kowa shamaki da ita ya kuma gitta mana tsinuwa da fushinsa, ya rabani da 'yata na tsawon shekaru takwas da watanni, gobe zan ganta, zan ganta insha Allahu, ko da ina d'ora ido a kanta ne na yarda a zare raina."
Da sauri ya mik'e tsaye ya dafa kafad'unta ya shiga rarrashinta da kwantar mata da hankali, jin kiran sallah ne yasa shi cewa "To daina kukan Ayya, ki tashi kiyi sallah an kira, nima zanje na d'auki abu a d'aki zan fita."
Jinjina kai tayi tana ci gaba da share hawaye har ya fita, tashi tayi ta kabarta sallah tana ta shashekar kuka.
*Maradi*
Washe gari kamar kullum ta shirya cikin riga wacce ta tsaya iya gwiwarta da wandonta wanda in ba tafiya take ba zaka rantse kace siket ne, takalman data saka masu tsini ya k'awata shirin nata, lafayarta fara tas ta d'auka ta d'ora akai, sallama suka ma Dada suka fita har tana zolayarta ko ta zo su tafi? Ita kuma da tasan halin kayanta sai tace a'a tayi zamanta, tana k'ok'arin fito da makulli a mota ta kai k'ofa bata ankara, da sauri taji ya rik'e lafayar yana fad'in "Ayya addu'a fa?"
Tsayawa tayi ta juyo tana fad'in "Yi hak'uri ban manta ba."
Gyara tsayuwa tayi ta d'aga hannu ya musu addu'a sannan suka fita, suna shiga mota tayi addua'r hawa abun hawa sannan suka d'aga. A hanya ta kalleshi cikin nutsuwa ganin ya mayar da hankalinshi kan littafinshi, murmushi tayi ta kalli gabanta tace "Amjad."
Kallonta yayi yace "Na'am Ayya."
Ba tare data kalleshi ba tace "Kana so na?"
Wani irin kallo ya mata kamar na mamaki sai kuma yace "Ayya, ke ce rayuwata fa?Ko wanda yake da baba yana son Ayyarsa bare kuma ni dake kad'ai nake da, Ina sonki sosai Ayya."
Kallonshi tayi cike da k'auna tace "Zaka iya rabuwa dani?"
Girgiza kai yayi yace "A'a Ayya, mutuwa kawai zata raba ni dake, amma Ayya me yasa kika tambayeni haka? Kina jin kamar bana sonki ne saboda ban fad'a miki gasar musabak'armu ba?"
Dariya tayi ta girgiza kai tace "Ko kad'an, kai ka tab'a ganin Ayyarka tayi hushi da abinda ka mata har ta hukunta ka abisa son ranta?"
A hankali cikin sunkuyar da kai ya girgiza kai, jinjina kai tayi tace "Me ye na fad'a maka ladabin da zaka iya yiwa babban da ka fara had'uwa dashi baka san shi ba?"
Saida ya kalli gabanshi ya sauke ajiyar zuciya yace "Idan naga babba na mishi sallama irin ta addinin musulunci sannan na gaishe gaisuwa irin ta al'ada, idan ina zaune ne shi kuma yana tsaye na bashi wuri ya zauna, idan muna zaune dukanmu ni na koma k'asa, idan yana magana karna katseshi har sai ya gama, idan yayi kuskure karna nuna masa kai tsaye na tunasar dashi cikin hikima, idan ya min kyauta karna karb'a sannan na masa godiya, sannan karna yarda da tafiya da mutum komai kamalarshi in dai ban sanshi ba."
Murmushi tayi ta jinjina kai tace "Da kyau, Oddonur na ne wannan."
Murmushi yayi shima suka ci gaba da tattaunawa irin haka har ta sauke shi, kallon cikin makarantar tayi tace "Ya naga dalib'ai duk a waje kamar lokaci baiyi ba?"
Fita yayi ya zagaya ta k'ofar da take yace "Watak'ila lokacin baiyi ba."
Kallonshi tayi tace "To wuce ciki." D'aga mata hannu yayi yace "Sai anjima Ayya."
Ita ma d'aga masa hannu tayi tace "Ban da fad'a fa."
D'aga kai yayi yace "To." Saida taga shigarsa ciki har mai gadin na d'ago mata hannu ita ma ta d'aga mishi dan ba zata iya d'aga murya ba ta wuce, kai tsaye kotu ta wuce dake kusa sosai da makarantarsu Amjad.
Tunda ta isa ta tunkari shiga taji gabanta na ta fad'uwa, sai dai ta horar da kanta dole ta dake ta jure tayi banza da duk wanda zata had'u dashi, ai kam tunda ta fito a mota idonsu suka sauka akan ta, cikin tashin hankalin ganinta Gomboy ta kalli dattijuwar kusanta tace "....
*Yawan sharhi yawan rubutu*