kirkirarren labari ne•••
>bissimillahi rahamanir rahim<
__duk abinda zaka samu a rayuwa zaka iya rasasa atare
da wannan rayuwar.
Rayuwa abace mai cike da farin ciki da kuma bakin ciki
a wani lokacin.
Dangi wani ginshi kine na farin ciki atare da wanda yake
da su.
Wato kamar ni sunana ishaq amma anfi sanina da prince.
Gidan mu ba wani babban gida bane domin umma na ce
kadai da abba na sai kuma nida kanwata fatema.
Banda matsala daya dake tinkarar wannan gidan namu
bayada wata matsala ita wannan matsalar ba kowa ce
irin matsala bace face.
Nida kanwata fatema domin babu jituwa atsakanin mu ko
kad'an da zaka tareni a hanya ka tambaye ni wanda na
tsana a rayuwa kaina a tsaye zance mata kanwata
fatema.
Domin a irin yadda zuciya ta take nunamin zanma iya
zama sanadiyar mutuwar ta.
Fatema yarinya ce mai ilimin boko da Arabic gata da
farin jini ga kuma kyawon fuska da zuciya.
Wanda ko wanne mutun yana ganin hakan amma banda
ni.
Na tsani fatema fiye da yadda rayuwa zatayi tunani.
Wanda nakasa boyewa domin saida abba na da ummar
mu suka fahimci hakan.
__________•••••
•••••
Wata ranar Monday koda na farka bacci misalin karfe
8:30 am.
Da sauri na fito dakina na nufi dani tabel domin yin break
fast.
Koda na iso wajen danin d'in sai naci karo da baba da
umma da kuma fatema suna break batare da furta ko
kalma ba.
Na zauna domin fara cin abinci wannan abun baima basu
mamaki ba domin sunsan akidatace duk wajen da fatema
take zaune toko ma waye a wajen bana masa magana.
Haka muka gama cin abincin lokacin da zan tashi ne abba
na yace ishaq yau inaga saura sati uku kufara s s c e ko
wata jarabawar kammala matakin secondary school.
Ko kallon sa banyi ba domin gudun kada na d'ago fuskata
naci karo data fatema.
cikin fushi umma tace ai malan ka hitabatun wannan
shashan yaron kawai ka tambayi kanwar sa.
In banda shashanci irin na prince kaida kanwar ka ciki
daya uwa daya uba daya .
Amma ka dauki tsana irin wannan ka Dora mata.
lokacin da tazo karshe da wannan maganar.
Sai fatema tace eh abba saura sati uku batare da na Ida
kammala cin abincin ba na tashi na bar wajen naje na
sako kayan mkr ta na.
Ganin nayo waje ne sai umma tace ma fatema maza kema
kitashi ko baki koshi ba ki diba kije school kici domin
kesan wannan mai banzar rayuwar ba jiranki zai yiba.
Koda na iso g*n mota saiga fatema aguje muka bude
muka wuce school.
Da isarmu school bayan nayi packing sai na fito na rigata
shiga class.
Bayan kamar 10 minutes da shigata class saigata ta shigo..
Gun wurin zamanta ta nufa domin ta zauna.
Da zamanta saiga malamim dake muna English dama ya
bamu home work.
Ganin yazo karbar sane farin ciki ya cikamin rayuwa
domin nasan na Riga na dauke littafin fatema na boye
agida.
Bayan kowa ya bayar sai ya lura da fatema tana neman
nata.
Cikin fushi ya Kira sunan ta fatema wannan wane irin
wulakanci ne kefa nake jira idan baki ganshi ba come
and leg down.
Haka fatema tazo tayi yadda malamin yace nan take
wannan malamin yasa aka kirawo masa displine master
yayiwa fatema bulala 20.
Kawai sai naga wasu hawaye na kwararowa idanuwan ta
ba karamin farin ciki nake shiga ba a duk lokacin da
naga hawaye a idanuwan fatema.
Bayan mun taso daga makarantar ne akan hanyar mu ta
dawowa sai motar mu tayi faci daidai da wurin zaman
wasu yan iskan gari.
Wato a wani kangon gidan dake yamma ga unguwar mu.
Wannan lokacin ne nacema fatema to malama ai sai ki
fito ki tafi da kava ko tinda motar tayi faci.
Nan take ta fito domin tsananin tsorona take kawai kulle
motar nayi na fara tafiya.
Bamuyi nisa da tafiya ba saiga mai mashin yazo wucewa.
Kawai tsaida sa nayi na hau domin ya iyar dani wannan
lokacin ne fatema tace min habah yaya prince Ashe zaka
iya tafiya kabarni a wannan hatsararren wajen cike da
damuwa a fuskata.
Nan take na sauko akan mashin din.
Ke harke samu bakin gayimin magana to dan babanki ki
hanani tafiya.
Zan juya kenan ta rikeni duk a wannan lokacin wa'yannan
yan shaye shayen suna kallon mu kawai ture ta nayi
nahau kan mashin din nayi tafiya ta.
Da isata gida iske nayi mama ta akan kujera a zaune
daga nina ni kadai prince ina kanwar ka fuskata a
turkune nace tana baya.
Na wuce daki na kawai fadawa nayi akan gado..
Daganan ban farka ba sai wajen 2:00 daidai da mama
tazo ta tasheni.
Budar bakin mama waikai ina kabaro kanwar ka harfa
yanzu bata dawo gida ba...
Cikin fushi natashi kamar ni da kanena ko kanwata habah
mama wannan wane irin nunamin rashin sone.
Toni meye ruwa na data dawo da kar tadawo intaga
dama ma ta mutu acan nine da kafafun ta.
Kawai bargo na na jawo na rufa Sannan na dauko waya
ta naci gaba da chat dina nida kawaye na da abokanaina.
A rayuwa ta abu daya ne nafi damuwa dashi fiye da
kowa da komai a rayuwa ta wannan abun kuma shine
wayata.
Domin idan ina tare da waya ko yunwa banaji balle
kasala atare dani atakaice dai ban hada kowa da wayata
ba.
Sakamakon wasu abubuwa da waya take tare dasu
kamar.
Facebook
Istergram
WhatsApp
Ban masan lokacin da umma na ta fito a dakin ba.
Ganin na shafe 2 hours ne a dakin yasa na fito domin
gudanar da sallar azahar.
Naci karo da umma na a zaune a falo tana sharar kuka.
Wanda hakanne ya kara tabbatar min da fatema bata
dawo gida ba.
Daf da isata kofar da zan fita sai umma na ta kiri sunana
prince dan Allah dan annabi.
Kagayimin idan wani mugun Abu ka aikatawa kanwar ka
fatema domin bata saba kaiwa hakan ba.
Fuska ta asake na kalli mama na nace habah mama wai
so nawa kk son na fada maki tana baya motar muce tayi
faci Toni bawan tane da zan goyo ta na kawo maki ita.
Kawai ficewa nayi daga gidan lokacin da nake kokarin
daukar mashin Dina domin yawon zagaya gari.
Sai mahaifina ya dawo daga aikin sa wato na likitanci a
wata assibitin kudi dake garin mu wato abuja.
Bayan na gaishe shine sai yake tambaya ta ina fatema.
Kafin nabasa amsa sai umma na dake baya na ta fa she
da kuka tace ai alhaji prince ya Riga ya cika burin sa
akan fatema domin tin sadda suka je school shi kadai ya
dawo haryanzu ita bata dawo ba.
Nayi tambayar sa ina ya kaita amma amsa daya yake
bani tana baya.
Nan take mahaifina ya daga waya yakira police domin
sukama ni saina bayyana masu fatema.
Nantake kamar ma ni ba dansa bane ya saka police
sukayi ram dani kamar wani barawo.
Budar bakin sa g*n jami'an tsaron duk abinda yakama
suyimin domin na bayyana fatema domin inada yakinin
zai iya aikata komai agunta.
Ganin zanji jiki ne a hannunsu yasa nace nasan inda na
baro ta.
Domin a rayuwa ta abu biyu nake tsoro police da kuma
rashin data a waya ta.
Nan take na kaisu g*n da na baro ta koda mukaje wajen
hatta yan shaye shayen dake gurin basa nan balle
kanwata.
Muna wajen ne sai wani saurayi kimanin dan 25 years
yazo.
Budar bakin sa g*n jami'an tsaron wata budurwa kuke
nema cikin sauri nace eh dan Allah ina take.
Ai motar kwana kwana ce tazo ta dauke ta wato
ambulance cikin mawuwacin hali.
Inaga assibiti mafi kusa zasu je da ita.
Nan take naji wani farin ciki ya mamaye ni domin nasan
fatema zata iya rasa rayuwar ta.
Koda muka isa assibitin kawai sai naga wasu 'yan alorori
ne aka yimata tare da karamata ruwa.
Kafin 'yan sandar sufara yimata tambayoyi sai ta kalleni
tace yaya prince dama nasan zaka dawo.
Kuma meye ya hadaka da jami'an tsaro.
Budar bakin wani dan sanda dake gurin muna arrested
nasa ne abisa zargin cutar dake.
Domin mun samu duk labarin alakar ki dashi akan
zamantakewar ku.
Amma yanzu zamu samu cikakken bayani akanki.
Budar bakin fatema ni wlh yaya na bayada sa hannu akan
wannan abun daya faru dani.
Kuma abbana bai fahimci zaman mu bane kawai ai tsabar
soyayyar dake tsakanin mu ne yasa hakan take faruwa
agare mu.
Sabida haka bayada laifi bakaramin farin ciki naji ba a
lokacin duk da hakan baisa naji son fatema araina ba
hasalima kara tsanar ta nayi.
Bayan mundawo gida ne ta kara wanke ni agun abba da
umma duk da umma bata yarda da maganar fatema ba.
Amma babu yadda ta iya haka tabar maganar ta wuce.
Bayan kwana uku da faruwar hakan wata ranar talata na
farka bacci.
Dama akida tace dana farka bacci aiki na na farko kafin
nayi alwalla nayi sallah.
Shine ciro waya ta a chaji na bude datar waya ya domin
duba shafin f*******: dina.
Wannan ranar ma haka nayi bayan budewar data sai naga
an turomin da bukatar sako.
Wato request message ganin hakan ne yasa na bude
wajen.
Sai naci karo da sunan wata yarinya kamar haka
# meenal_meenal
Tayomin message kamar haka:
Assalamu alaikum yaya Prince ina daya daga cikin
member na f*******: group naka dama w******p ina jin
dadin littafan ka ba karamin sone nake yimaka ba.
Duk da nayi nesa da kai amma ako da yaushe zuciya ta
cikin tunanin ka take idanuwa na basada abin kallon daya
wuce fotunan ka domin a duk sa'adda ka Dora pic nama
a story saina dauka.
Prince wlh akanka yanzu hakan na rabu da mama na
abba na da duk wani dangi nawa.
Harda ma ubangiji na na rabu dashi akanka.
Ahalin yanzu ina gayimaka wannan maganar ne domin na
mallaka maka kaina.
Dan allah ka tausawa rayuwa ta ka karbe ni wlh prince
idan kayi banza dani zan kashe kaina kuma kaine da
alhakin.
Nabaka nan da 5 hours kazo sabon gari bakin babbar
makaranta ka dauke ni.
Domin ayanzu kaine kawai kasan inda nake duk duniyar
nan.
Wlh ba karya nake ba zan kashe kaina idan baka zoba.
Lokacin dana kammala karanta wannan sakon sai naji
wani gumi ya cikamin ko wane lungu dake cikin jiki na.
Nan take sai jiki na ya dauki rawa nasaki waya akan
gado na na kura mata idanu..
Nan take sai jiki na ya dauki rawa domin ba karamin
firgici na shiga ba.
Da sauri na gyara jiki na sannan Nayi sallah koda 7:00
am.
Nakamo hanyar address din data bani.
Kamar yadda tabani kuwa haka akayi domin anan na
sameta ita da jakar kayanta.
Meenal yarinya ce fara doguwa ba mai irin kafrin jikin
nan ba.
Da isa ta wajen ta mike tsaya yaya prince wlh daka bata
koda 1 minute ne a yadda nace zan kashe kaina.
Nidai duk a wannan lokacin hankali yakasa kwanciya da
wannan yarinyar.
Budar bakina g*n Meenal dan Allah meye dalilin ki na
baro gidan ku kizo guna.
Bakya tunanin halin da iyayenki suke ciki yanzu.
Yaya prince kada kadamu da iyaye na nidai kawai yanzu
kakaini mazaunin ka dan Allah wato inda zaka rayu dani
domin wlh idan ba kaiba bazan iya zama da ko wanne
namiji ba.
Cikin alamun rashin yadda na Kira aboki na wato imran.
Bayan ya daga wayar imran zanzo da wata yarinya gidan
ka dan Allah idan babu damuwa ina son tazauna anan na
d'an wani lokaci.
Budar bakin imran habah aboki na Karka damu wlh ai
babu abinda bazan iya yimaka ba.
Amma yanzu bana gari naje kaduna ne d'aurin auren
aboki na.
Jiya ma aka daura auren dama yanzu nakeda niyyar naje.
Nayi masu bankwana shida amaryar sa saina dawo.
Amma kaje g*n hajiya ka karbo key ok shkn aboki na
adawo lfy.
Bayan nakai Meenal ne a gidan ta girka muna abinci
munci.
Domin gidan babu abinda babu na dangane da abinci.
Saina bukaci da neman sanin labarin Meenal da kuma
dalilin ta na rabuwa da iyayen ta akaina.
Budar bakin Meenal habah yaya prince banada dalilin
daya wuce sonka shin kai ko baka so nane.
Kwatsam sai ji Nayi ta Kama hannaye na ta jawo ni ajikin
ta.
Tana mai fara shasshekar kuka cikin alamun tausaya
nace shkn Meenal nima ina sonki amma kinsan aure bazai
taba yiyuwa ba.
Idan babu sa hannun iyaye na da naki ko sabida haka doli
zamu koma g*n iyayen ka domin neman yardar su akan
auren ki.
Ni anawa iyayen babu wata damuwar su akan zabi na.
Budar bakin Meenal yaya prince kenan baka yarda da na
guji iyaye na akanka ba.
To kasani yadda na baro iyaye na koda gawata aka
mayar masu inada tabbacin bazasuyi bakin ciki ba.
Domin nasan ma ahalin yanzu bakunan su tsinewa suke
turomin.
Jin wa'yannan kalaman ne a bakin Meenal yasa jiki na
yayi sanyi Budar baki na Habah Meenal daganin ki anga
wayayyiyar yarinya mai kamala da tarbiya gami da ilimi
domin yanayin shigar ki ya bayyana hakan dan Allah
akan mi kikayi wannan ganganci.
Kan Meenal tsaye bude idanuwan ta tace wlh prince duk
akanka.
Domin wlh zan iya rabuwa da kowa akanka.
A daidai wannan lokacin sai mama na takira wayata
bayan na dauka ne.
Wai kai prince yaushe zakayi hankali kasan fa kanwar ka
bazata iya zuwa school ba idan babu ka.
Kuma meye ya fitar da kai gida tinda safen nan?
Batare data bari na furta ko kalma ba ta yanke wayar.
A wannan lokacin ne nagayiwa Meenal zanje gida tare da
bata wa'yan su kudade da zata bukaci koda kayan
makulashe ne idan tafita waje.
Sannan tace dan Allah na dawo gunta misalin 2:00Am.
Nan mukayi sallama sannan na shigo gida wannan lokacin
ma ahaka mukaje school nida fatema.
Koda fuska bama iya had'awa.
Wani lokacin ma idan ina tuka fateema a mota sai Naji
kamar Nayi hatsari duk in mutuwa zamuyi mu mutu.
Kwatsam sai naga wasu hawaye na zubowa a fuskar
fatema.
Wanda hakan ya nunamin nine silar kukan ta domin
fatema ba karamin so take min ba.
Ni kuma haka kawai Naji na tsaneta arayuwa.
Hardai muka dawo gida babu abinda ya had'ani da
fatema koda magana ne.
Da isowar mu gida sai wayar imran Nagani bayan daukar
wayar tawa.
Aboki na koka dawo gida ne.
Eh wlh nadawo cikin sanyin murya.
Lfy aboki na Naji muryar taka kasa kasa eh wlh aboki na.
Kasan nace maka d'aurin auren aboki na naje ko.
To wlh amaryar tasa ta kashe sa ta gudu.
Kuma ita da kanta tabar wasikar hakan domin kada ma a
zargi wani.
A wasikar ta rubuta wai dama da a kwai wanda take so
kuma zata shiga duniya neman sa.
Kai aboki na allah dai ya zab'a muna mata nagari masu
son mu.
Budar bakina cikin alamun firgici nacewa imran dan
Allah kai kasan fuskar amaryar?
Kafin ya bani amsar na kara da cemasa wanda tace tana
so meye kuma sunan sa?