
kirkirarren labari ne•••
>bissimillahi rahamanir rahim<
__duk abinda zaka samu a rayuwa zaka iya rasasa atare
da wannan rayuwar.
Rayuwa abace mai cike da farin ciki da kuma bakin ciki
a wani lokacin.
Dangi wani ginshi kine na farin ciki atare da wanda yake
da su.
Wato kamar ni sunana ishaq amma anfi sanina da prince.
Gidan mu ba wani babban gida bane domin umma na ce
kadai da abba na sai kuma nida kanwata fatema.
Banda matsala daya dake tinkarar wannan gidan namu
bayada wata matsala ita wannan matsalar ba kowa ce
irin matsala bace face.
Nida kanwata fatema domin babu jituwa atsakanin mu ko
kad'an da zaka tareni a hanya ka tambaye ni wanda na
tsana a rayuwa kaina a tsaye zance mata kanwata
fatema.
Domin a irin yadda zuciya ta take nunamin zanma iya
zama sanadiyar mutuwar ta.
Fatema yarinya ce mai ilimin boko da Arabic gata da
farin jini ga kuma kyawon fuska da zuciya.
Wanda ko wanne mutun yana ganin hakan amma banda
ni.
Na tsani fatema fiye da yadda rayuwa zatayi tunani.
Wanda nakasa boyewa domin saida abba na da ummar
mu suka fahimci hakan.
__________•••••
•••••
Wata ranar Monday koda na farka bacci misalin karfe
8:30 am.
Da sauri na fito dakina na nufi dani tabel domin yin break
fast.
Koda na iso wajen danin d'in sai naci karo da baba da
umma da kuma fatema suna break batare da furta ko
kalma ba.
Na zauna domin fara cin abinci wannan abun baima basu
mamaki ba domin sunsan akidatace duk wajen da fatema
take zaune toko ma waye a wajen bana masa magana.
Haka muka gama cin abincin lokacin da zan tashi ne abba
na yace ishaq yau inaga saura sati uku kufara s s c e ko
wata jarabawar kammala matakin secondary school.
Ko kallon sa banyi ba domin gudun kada na d'ago fuskata
naci karo data fatema.
cikin fushi umma tace ai malan ka hitabatun wannan
shashan yaron kawai ka tambayi kanwar sa.
In banda shashanci irin na prince kaida kanwar ka ciki
daya uwa daya uba daya .
Amma ka dauki tsana irin wannan ka Dora mata.
lokacin da tazo karshe da wannan maganar.
Sai fatema tace eh abba saura sati uku batare da na Ida
kammala cin abincin ba na tashi na bar wajen naje na
sako kayan mkr ta na.
Ganin nayo waje ne sai umma tace ma fatema maza kema
kitashi ko baki koshi ba ki diba kije school kici domin
kesan wannan mai banzar rayuwar ba jiranki zai yiba.
Koda na iso g*n mota saiga fatema aguje muka bude
muka wuce school.
Da isarmu school bayan nayi packing sai na fito na rigata
shiga class.
Bayan kamar 10 minutes da shigata class saigata ta shigo..
Gun wurin zamanta ta nufa domin ta zauna.
Da zamanta saiga malamim dake muna English dama ya
bamu home work.
Ganin yazo karbar sane farin ciki ya cikamin rayuwa
domin nasan na Riga na dauke littafin fatema na boye
agida.
Bayan kowa ya bayar sai ya lura da fatema tana neman
nata.
Cikin fushi ya Kira sunan ta fatema wannan wane irin
wulakanci ne kefa nake jira idan baki ganshi ba come
and leg down.
Haka fatema tazo tayi yadda malamin yace nan take
wannan malamin yasa aka kirawo masa displine master
yayiwa fatema bulala 20.
Kawai sai naga wasu hawaye na kwararowa idanuwan ta
ba karamin farin ciki nake shiga ba a duk lokacin da
naga hawaye a idanuwan fatema.
Bayan mun taso daga makarantar ne akan hanyar mu ta
dawowa sai motar mu tayi faci daidai da wurin zaman
wasu yan iskan gari.
Wato a wani kangon gidan dake yamma ga unguwar mu.
Wannan lokacin ne nacema fatema to malama ai sai ki
fito ki tafi da kava ko tinda motar tayi faci.
Nan take ta fito domin tsananin tsorona take kawai kulle
motar nayi na fara tafiya.
Bamuyi nisa da tafiya ba saiga mai mashin yazo wucewa.
Kawai tsaida sa nayi na hau domin ya iyar dani wannan
lokacin ne fatema tace min habah yaya prince Ashe zaka
iya tafiya kabarni a wannan hatsararren wajen cike da
damuwa a fuskata.
Nan take na sauko akan mashin din.
Ke harke samu bakin gayimin magana to dan babanki ki
hanani tafiya.
Zan juya kenan ta rikeni duk a wannan lokacin wa'yannan
yan shaye shayen suna kallon mu kawai ture ta nayi
nahau kan mashin din nayi tafiya ta.
Da isata gida iske nayi mama ta akan kujera a zaune
daga nina ni kadai prince ina kanwar ka fuskata a
turkune nace tana baya.
Na wuce daki na kawai fadawa nayi akan gado..
Daganan ban farka ba sai wajen 2:00 daidai da mama
tazo ta tasheni.
Budar bakin mama waikai ina kabaro kanwar ka harfa
yanzu bata dawo gida ba...
Cikin fushi natashi kamar ni da kanena ko kanwata habah
mama wannan wane irin nunamin rashin sone.
Toni meye ruwa na data dawo da kar tadawo intaga
dama ma ta mutu acan nine da kafafun ta.
Kawai bargo na na jawo na rufa Sannan na dauko waya
ta naci gaba da chat dina nida kawaye na da abokanaina.
A rayuwa ta abu daya ne nafi damuwa dashi fiye da
kowa da komai a rayuwa ta wannan abun kuma shine
wayata.
Domin idan ina tare da waya ko yunwa banaji balle
kasala atare dani atakaice dai ban hada kowa da wayata
ba.

