Chapter 2

872 Words
A bangaren da manya ke ajiye motarsu, ya ajiye motarsa ne, yana fitowa daga mota sakatariyarsa mai suna Anita John, ta amshi jakar dake hannunsa, har zai wuce kenan sai ya kalli bangaren da shugaban kamfani ke ajiye motarsa wanda da bangaren sirikinsa ne Alhaji Ahmed Naira, amma bayan rasuwarsa sai wajen ya kasance ba komai, sai bayan anyi zaɓe, ya tuna lokacin da yake masa nasiha a lokacin da yake ciwon ajali, yace" ka kasance mutum mai mafarki, ta hakane kaɗai zaka cimma burinka, sannan karka kasance mai baƙin ciki ko hassada, sae kaga kana cigaba a rayuwarka. Ka kasance mai kulawa da iyalinka, ka fita duk wani hakkinsu, sai kaga Allah na buda maka na ko'ina". Ya cigaba sosai shi kuma ina sauraronsa. Sai yake jin kamar yanzu suke maganar, murmushi yayi sannan suka wuce zuwa ofishin sa. Gabatarwa sai karfe 10am na safe za'a fara, yana da awa daya da rabi, ya samu kujerar zamansa ya zauna, sannan yayi umarnin a kawo masa shayi. Wayarshi ta hau ruri, ba sai ya duba ba domin daga karar yasan abar kaunarshi ce, kalar takenta daban dana kowa. "Mijina kaje lafiya?" ta fada cikin soyayya "Lafiya lau abar kaunata" murmushi fal a fuskarsa. Sun sha hira ta soyayya wanda dama kullum haka abin yake in basuyi waya ba za'ayi messages, wataran a hada duka biyun, inda sabo wanda suke tare dashi sun saba. Ta masa fatan alkhairi sannan suka katse wayar. Yana juyawa suka hada ido da abokinsa wanda ya kasance PA ( maitaimaki na musamman) dinsa, yana masa dariya. "Dan sa ido kawae, a nemi wata sana'ar dai" Deen ya fada yana harararsa "Haba Romeo koya mana kake fa" Sadiq ya amsa, sun kasance aminai tun daga sakandare, daya samu dama sai ya janyo shi a jiki. "Sai kuyi tayi ai" ya fada yana dariya "Naga ka kammala aikin ai, kayi kokari sosai" Sadiq ya fada yana sake duban aikin a cikin na'ura "Wannan duk aikin Zainab ne, itace tayi komai, kadan na taimaka" ya fada tare da jinjina ga matarsa "Ba irin namu matan ba wanda ko shirya suna a file ka saka su sai ranka ya ɓaci" ya fada yana dariya mai kama da yaƙe. "Ka godewa Allah dai, in ba haka ba ka godewa azabarsa" ya fada tare da murmushi "Hakane kam, Allah mun godema" ya fada yana dariya Anita wacce take gefe tana kallonsu bata san me suke cewa ba, kawae ta bisu da murmushi, a Hausa banda "zo" ba abnda take fahimta. Shiyasa wani lokacin suke hirarsu a gabanta ba tare da fargabar wani abu ba. Ita kuma abotarsu na birgeta, a office suna yaro da oga, amma ana fita toh abokaine wanda suka shaƙu sosae. Suka sake bitar aikin, basu daɗe da kammalawa ba aka musu maganar su fito xa'a fara gabatarwar, suka dauki duk wani abu da suke bukata sannan suka nufi dakin da ake babban taro. Suna shiga dakin taron sai yayi arba da abokin takararsa wanda ya kasance ɗa ne ga Mataimakin chairman na kamfanin, Alhaji Nasiru Naira, wanda yasa suka zama yan uwa da Zainab, tare sukayi rayuwar makarantar jami'a, sunyi aji ɗaya. Rashin jituwarsu ya samo asali ne akan soyayyar da sukewa Zainab, bayan Zainab ta auri Deen sai ya hakura, amma kuma baya shiga wata sabga ta Deen, lokacin da suka sami aiki a Albarka Group of Companies sai rashin jituwarsu ta karu, amma basu taba yin abinda zai kawo naƙasu a kamfanin ba, bayan da aka sayi Karamci Investment sai Alhaji Ahmed Naira ya mayar da Yusuf can domin ya kula da bangaren kasuwancin, shi kuma Deen ya kula da na Albarka Group of Companies. Daga nesa suka ɗagawa juna hannu, sannan Deen ya karasa inda zasu zauna shi da mukarrabansa, shima Yusuf suka sami wuri suka zauna suna jiran a fara. Basu daɗe da zama ba sae ga shugaban ƙasa da da jama'arsa suka shigo, kowa ya miƙe saboda girmamawa, bayan ya zauna sae kowa ya koma ya zauna. Sakataren gwamnati ya miƙe yayi jawabi sannan aka fara, kamfanoni biyar ke neman kwangilar, kowanne kamfani yana da awa daya domin gabatarwa. Daya bayan daya aka dinga zuwa ana gabatarwa in aka kammala sai a tafawa wanda ya gabatar, bayan anyi na kamfanoni guda uku sae aka bada hutu wasu mintuna da kuma ayi sallah a dawo. Ana dawowa Yusuf yayi nashi gabatarwar wanda ya ƙayatar sosai, har ragowar kamfanonin suka ji basu da laka a jikinsu, yasha tafi daya kammala, har takai shugaban ƙasa sai daya jinjina masa. Bayan ya sauko sai Deen ya hau ya fara nashi wanda shima ya ƙayatar yanda ya kamata, nan aka sakawa mutane kokwanto akan a tsakaninsu waye zai nasara, yasha tafi da jinjina sannan da fatan alkhairi. Nan aka tashi akan za'a fadi wanda yayi nasara sannan taro ya tashi. Deen da jama'arsa suka tafi bangaren da ofishinsu yake, suna shiga duk suka samu kujerar suka zauna, saboda gajiya, wayar Zainab ce ta tasheshi, ya daga yana bata labarin abin da ya wakana, ta fada masa maganganu masu karfafa gwuiwa sannan sukayi sallama. Ya rufe idonsa yana tuna irin rayuwar da yasha kafin yazo wannan matsayi da yake, rayuwa wacce inda an fada masa zai zo wannan matakin zai musanta maganar.
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD