bc

Fauzuddeen

book_age16+
0
FOLLOW
1K
READ
confident
inspirational
straight
city
abuse
friendship
friends with benefits
gorgeous
passionate
shy
like
intro-logo
Blurb

Wannan labari ne akan saurayin da yake so ya kula akan mu'amala da mata, sakamakon gurbacewar tarbiyya, yanaso ya riqe mutuncinsa sae yaxo aure.

chap-preview
Free preview
Chapter 1
Yau tun da wuri ya farka daga barci saboda rana ce mai mahimmanci matuka a gareshi. Saboda mahimmancin ranar kasa barci yayi domin shirye shirye. Tun tsakar dare ya gama hada presentation dinsa tare da taimakon abar ƙaunarsa. 4am ya tashi ya dinga jera nafiloli yana fadawa Allah damuwarsa, saboda yasan shi kadai ne zai iya wanke masa, bayan an kira asuba sae ya fita masallacin dake kusa dasu yayi nafilarsa sannan ya dauki Al quran yana biyawa, har dai liman yazo akayi sallah, ya koma gd. Yana komawa ya shiga yayi wanka, sannan ya shirya, cikin suit ɓaka. Fauzuddeen Ahmad kenan wanda ake wa laƙabi da Deen, yana aiki da Albarka group of companies, yana da matarsa kyakkyawa wacce yanzu shekarunsu na aure 15, sunanta Zainab Ahmad, ƴa ce ga shahararren dan kasuwar nan Mai suna Alhaji Ahmed Naira. Sun hadu ne a lkcn da yake karatunsa na jami'a, soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu har sukayi aure. A yanzu suna da yara hudu wanda duk twins ne, Fatima da A'isha wanda yanzu shekarunsu na haihuwa 13, suna JSS 3, sae kuma AbdulHakim da AbdulHalim wanda shekarunsu ma haihuwa 9, kuma suna aji 5 na primary. Ya dauko laptop dinsa yana duba aikin saboda kar a samu wata matsala, akan haka ma sae da yayi copying aikin a wurare har 4 saboda kar matsala ta auku. Yana cikin duba aikin sae yaji peck a kumatunsa, murmushi yayi wanda ko ba'a fada masa ba yasan Madam ce da kanta kamar yanda yake kiranta. "The virgin boy" ta fada da murmushi a fuskarta, al'adar gidan ne magana da harshen turanci, musamman lokacin aiki. "really?" ya amsa mata, wanda sunan ya samo asalinsa tun yana makarantar sakandare har zuwa jami'a. "How is the preparation" ta tambaya idonta cikin yanayi na lumshewa saboda tare sukayi aikin har tsakar dare, sai bayan angama sannan ta kwanta barci. "Still not quite sure" ya fada alamar ba confidence a tare da shi, ta juyo ta kalleshi ido cikin ido tace "ka tuna irin ƙalubalen daka fuskanta kafin kazo wannan matakin, meyasa kuma sae da nasara ta kusa samuwa zaka karaya, ka sani a kowanne yanayi muna tare dakai, kuma nasara na tare da kai" Murmushi yayi na jindadi sannan yana godewa Allah daya bashi mata wacce take bashi ƙarfin gwuiwa, ta zamar masa bangon da zai jingina duk lokacin da yake buqata. A shekarun da sukayi na aure kullum fahimtar su ƙara ƙarfi take, sannan shaƙuwarsu na ƙara ƙarfi. "I will do my best to make our family proud" ya fada da confidence a maganarsa. "I know you will" ta fada sannan ta sumbaci goshinsa, tayi hanyar waje tana cewa" bari na tashi yaran nan suyi sallah karsu makara" "muje na rakaki" ya fada tare da tasowa ya riqe hannunta suka fita daga dakin. Ta dakin Fatima suka fara, suna shiga sae shock ya kamasu, domin ganin yaran sukayi tare sun gama karatun Alkur'ani mai girma suna addu'a Fatima na addu'a tana cewa "Ya Allah kayiwa iyayenmu albarka, ka biya musu dukkanin buqatunsu, Ya Allah yau babban ranace ga maifinmu Allah kasa ya samu abin da yake nema, Allah ka buda masa domin ya kula damu, ya Allah kasa mu zama masu biyayya gareshi, ka kara mana sonsa a xuciyarmu, mahaifiyarmu ya Allah kasa ta rayu cikin farin ciki, ka sakata cikin matan aljannah, ka bata hakurin xama damu baki daya, Allah kasa ka mu a aljanna baki daya. Mu kuma ya Allah ka shirye mu ka buɗa mana kwakwalwar mu, ka bamu lafiya ka shirye mu" haka ta cigaba da addu'a mai tsayi, iyayen na gefe ita Madam har da hawaye domin jindadin da take, shi kuwa Deen amin kawae yake cewa ya daga hannunsa sama, farin ciki mara misaltuwa a ransa, suka rufe da salatin Annabi SAW sannan suka shafa. Suna juya suka ga iyayensu, mamansu harda hawaye, sae suka taho suka rungume su, Fatima dama yar abbanta ce, suka dawo gefen gado suka zauna Fatima take cewa " Ummi wannan duk idea din dukkanninmu ne, sbd munji dadin abin da kuke mana, yau tare mukayi jam'i, AbdulHakim ne ya ja sallar. "Allah ya muku albarka yarana" iya abinda suka iya cewa knan, sai suka shiga shirin makaranta domin kar a makara. Tare akayi breakfast sannan ya daukesu zuwa makaranta, wanda mafi yawan lokuta Zainab ke kaisu ta dauko, ta koma full housewife tun bayan data mayar da duk abnda ta mallaka wurin mijinta. Shi wannan kwangilar in yaci shi zai zama shugaban kamfanin gaba ɗaya na Albarka Group of Companies shiyasa ya dauki kwangilar da mahimmanci sosai, sannan banda haka kamfanin su zai zama cikin goman farko a Afrika in suka samu kwangilar. yaran sunyi murna sosae da samun mahaifinsu ya kaisu makaranta, kuma gashi yau basu makara ba, sae murmushi suke, bayan ya ajiye su sae duk suka zo ya rungume su kafin su shiga class. Bayan duk sun tafi ya rage saura Fatima sae yace mata " Allah ya miki albarka, wannan ya nuna ko bayan mi xaki kula da yan uwanki" "Ameeeen Abbana" ta fada tana murmushi, ta rungume shi itama sannan ta nufi class saboda lokacin assembly bai ba. Sai ya shiga motarsa ya nufi hanya da zai tafi kamfaninsu, a hanya secretary dinsa ta kirashi a waya tace "We're ready Sir" yana murmushi ya katse wayar.

editor-pick
Dreame-Editor's pick

bc

Unscentable

read
2.0M
bc

He's an Alpha: She doesn't Care

read
824.0K
bc

Claimed by the Biker Giant

read
2.1M
bc

Holiday Hockey Tale: The Icebreaker's Impasse

read
1.0M
bc

A Warrior's Second Chance

read
381.8K
bc

Not just, the Beta

read
360.9K
bc

The Broken Wolf

read
1.2M

Scan code to download app

download_iosApp Store
google icon
Google Play
Facebook