Chapter 11

2336 Words
Ko da yaje gida ya samu Dada da bak'in dake zuwa siyan turaren wuta, sallamarshi tasa suka maida hankali kanshi, amsawa sukayi inda Dada ta d'ora da fad'in "Kai jikallen, ya na ganka ka dawo? Ina makarantar kuma?" Saida ya kalli matan yace "Ina kwananku." Amsawa sukayi da "Lafiya lau." Sannan ya kalli Dada yace "Dara nra wani malami ne ya rasu shiyasa aka ce ba ayi." "Allah sarki! Allah ya jikanshi, amma waya dawo da kai gida?" Turo baki ya d'anyi yace "Dada dreban wata yar makarantarmu ya dawo dani." Hararanshi tayi tace "Amma kasan Ayyaka bata so ko?" Marairaicewa yayi yace "Karki hassalata mana, idan ta zo zatayi fad'a ki bata hak'uri." Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um! In nayi me zaka bani?" Dariya yayi yace "Yau zan siyo miki naman miya." Dariya duk suka saka inda wata daga ciki tace "Ai kuwa shikenan yaro, wannan k'ok'ari haka." Kallonshi tayi tace "Shiga ciki to saika cire kayan." Saida suka gama siya zasu tafi ta mik'e ta rakasu wayarta ta fad'i saman jikinta, duk'awa tayi ta d'auka tana dubawa, k'walla kiran Amjad tayi yana fitowa ta bashi wayar tace "Sa min caji fad'uwa tayi, data mutu sai cajin ya fece ya tafiyarshi." Amsa yayi ya koma ciki da wayar yasa caji da niyyar in ta d'auka ya kira, ta jima bata d'auka ba daya kunna saita mutu sai da lokacin tashinsu yayi, hankali tashe ya sake kunna wayar yayi sa'a ta kama ya aika kira. _______________ Fita tayi daga motar tana daf da shiga cikin makarantar mai gadi ya fito rik'e da buta, murmushi ya mata yace "Kai Hajia ce? Sannu da zuwa." Cikin hange hangen inda zata hangeshi tace "Sannu, ban ga yara ba, har an jima da sakinsu ne haka? Naga yanzu ne 12:00 tayi." Aje butar yayi yace "Hajia wai kina nufin bai je gida ba? Ai kuwa nan tunda da safe ya bar nan yace zai koma gida.". A firgice ta kalleshi baki bud'e cikin fad'uwar gaba tace "Ban gane tunda safe ya bar nan ba? Ina ya tafi? Ya akayi ka bar min yaro ya fita?" Cike da rarrashi yace "Yi hak'uri Hajia, wallahi shi da wata yarinya ya fito nan yace zasu tafi gida, kuma da kaina na tare musu adaidaita suka tafi." A tsawace tace "Wace yarinya? Ina suka bi?" Cikin rud'ewa kamar yanda ya ga tayi ita ma ya nuna mata, hannu ta d'aga kamar zata mare shi sai kuma ta sauke hannun ta juya baya, dafe k'ugu tayi tana kallon masu sarrafa katifa ta siyarwa, yanayin da take ciki ne taji ya nunku hawaye sun sake gabce mata, juyowa tayi ta kalleshi tace "Malam taya zaka bari su tafi, me yasa yarona zai tafi? Wacece ita yarinya? Indai gida suka tafi me yasa suka bi ta nan a mamadin wannan hanyar?" "Hajia kiyi hak'uri dan Allah, amma ke daga gidan kike kuma baya can?" Kallonshi tayi da sauri kamar ta tuno wani abu, da gudu ta nufi mota ta bud'e ta lalubo wayarta, a daidai lokacin kiran Dada ya shigo wayar da alama ma akwai appel manqu*. Da sauri ta d'auka ta d'ora a kunne tana fad'in "Oui Dada, Amjad ya zo gida ne?" Cikin tattausan muryarshi yace "Ayya ni ne, Ayya kiyi hak'uri na tayar miki da hankali, dan Allah ki zo gida nima tun d'azu na dawo." Kashe wayar tayi ta ma rasa me zatayi, cije leb'e tayi tana jinjina kai, juyowa tayi ta hangi mai gadin tace "Kayi hak'uri, yana gida." "Ya je gidan ko? To Alhamdulillah." Juyawa yayi ya koma ciki ita ma ta shiga mota ta d'auki hanya, tana zuwa gida ta fita a motar ta tunkari shiga ciki da sauri rai b'ace, tunda yaji tsayawar motar ya fito da gudu tarbenta. Tana shiga shi kuma yana fito sukayi karo, rumgumeta yayi da murna, b'amb'areshi tayi daga jikinta taja hannunshi zuwa ciki, Dada dake zaune tana kallo ta wuce dashi d'aki, mik'ewa tayi ta bi bayansu tana fad'in "Faduma dan Allah karki dake shi, saurare ni kiji abinda ya faru." Tunda ta ga bata kula ta ba tasan yau fa abubuwan sun motsa, babu abinda zai hana Amjad gane kurenshi. K'ofar d'akinshi ta tsayar dashi ta kalleshi rai b'ace tace "Yaushe ka fara sab'a umarni na? Yaushe ka fara kunnen k'ashin da har zan maimaita maka magana sau biyu? Ni ce zan fad'a maka ga yanda nake so amma ka kasa yi saboda kana so kaga na tashi hankalina akan ka a tsakiyar t**i ina bilayin nemanka kamar wata yar iska?" Yanda ta k'arashe maganar da d'aga murya yasa shi fashewa da kuka ya had'e hannaye biyu yace "Ayya kiyi hak'uri, kiyi hak'uri ba zan sake ba, ba ayi karatu bane shiyasa dan kar na zauna na jiraki na taho." Jinjina kai tayi tace "Yayi kyau, had'e min hannayenka anan ka tsaya har sai na gama tunanin abinda zan maka." Juyawa tayi zata shiga d'akinta yace "Ayya Dada Aisho tace na gaisheki." Da wani irin sauri ta juyo tana kallonshi, yanda ta firfito da ido zai tabbatar maka maganar ta girgiza ta, da sauri ta k'arasa kusanshi ta sunkuya daidai tsayinshi tace "Aisho? Ina ka santa? Ina kuka had'u? Ya akayi ta sanka?" Cikin nutsuwa ya shiga fad'a mata yanda akayi, yana labarta mata komai tana sake shiga d'imuwa da zautuwa, har saida ta kai ta rufe bakinta da hannun hagu tana girgiza kai da ziraro hawaye, numfashi ta dinga saukewa tana kallon k'wayar idonshi, durk'ushe tayi ta rik'oshi tana fad'in "Kuma ka ganshi a hoton?" Jinjina kai yayi yace "Na ganshi Ayya? Amma me yasa ko hoto d'aya ba zaki aje ba dan na dinga ganinshi? Ayya ba dan na gani ba yanzu da bansan wa nake kama dashi ba, ke ma ya kam..." Da sauri ta kuma k'wak'umeshi jikinta duk sai b'ari take tana rawar murya tace "Amjad..., karka yarda da kowa, Amjad ni ce mahaifiyarka ni kad'ai, babu wanda yake sonka sama dani, karka sake yarda da kowa akan maganar mahaifinka, mahaifinka baya raye a duniya baya raye kaji, idan kuma ka bari suka ganeka wallahi zasu rabani da kai, kai kana so a rabaka dani?" Girgiza kai yayi a hankali yace "Ayya su waye zasu rabaki dani?" Kai tsaye tace mishi "Dangin mahaifinka?" Langab'e kai yayi yace "To Ayya idan su suna son rabani dake, danginki fa? Suma zasu rabamu ne?" Hawayen da suka malalo mata ne suka sa ta sake rufe bakinta dan bata so sautin kukanta ya fita, durk'ushe yayi shima yana share mata hawayen yana fad'in "Dan Allah Ayya ki daina kuka? Kiyi shiru kinji." Matsowa Dada tayi ta kalleshi tace "Tashi ka fita waje kayi wasa." Mik'ewa yayi zai fita da sauri Faduma ta kalleshi tace "A'a karka fita, shiga d'akinka ka zauna." Juyawa yayi ya shiga d'akin, tashi tayi ta kama hannun Dada suka shiga d'akinta, saida ta mayar da k'ofar ta rufe ta zaunar da ita bakin k'aramin gadon suna kallon juna, a nutse Owwo ta kalleta tace "Faduma akwai matsala ne? Naga duk kinyi wani iri dake? Me yake faruwa ne?" D'aga kai tayi tace "Dada akwai babbar matsala." Hankali tashe tace "Me ya faru?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Dada yau dai Tagur yasan akwai d'ansa a wuri na, kuma nasan cikin k'ank'anin lokaci zai san komai a game dani da Amjad." Da tsananin mamaki tace "Ya san shi? Ya akayi ya sani kuma?" "Hummm! Dada bana fad'a miki Hindu nan bata min ba? Ko rantsuwa nayi nasan ba zanyi kaffara ba cewa ita ta fad'awa matarshi, ita kuma matarshi haushin na tona asirin baya haihuwa shine ta min wannan tereren a cikin kotu har tana kirana da sunan wai karuwarsa ce ni." Mik'ewa tayi tsaye cikin b'acin rai tace "Karuwa? Wacece ita? Ina zan same ta? Dan an fad'i gaskiya har zata fad'a miki haka?" Jawota tayi ta koma ta zauna tana fad'in "Zauna Dada, ita ba matsalata bace zanji da ita daga baya." Zaune tayi tana huci sai kuma ta kalleta tace "Yanzu miye abunyi? Dan alamu sun nuna sirrin nan da aka jima ana b'oyewa daf yake da fitowa fili, duba kiga ta yanda yau yaje gidan nan, ya kike gani da ya had'u da Tagur ko Hatimi?" Girgiza kai tayi tace "Ba zasu had'u yau ba kam, sai dai nasan zuwa yanzu ya fito, tunda yana da kud'i ba lallai ya kwana a magark'ama ba kamar yanda alk'ali ya umarta." Ajiyar zuciya ta sake saukewa tana kallonta tace "Dada kinga ni da yamma zan d'auki hanyar Zinder, nasan waye Tagur Dada, tabbas ba zai iya bacci ba yau har sai ya nemi inda nake dan ya k'arasa sanin abinda ya fara tambayata a kotu, bana son had'uwata dashi yanzu saboda har yanzu ina da rauni idan na tsaya gabanshi, kin sani k'aramin aikinshi ne ya tara mana jama'a a unguwar nan, shiyasa nake so na bawa Aminu Amjad ya tafi dashi gidansu, ke saiki zauna kafin na dawo koma meye ya faru." A hankali ta kalleta tace "Amma shi Aminu kina ganin ba zai samu matsala daga gidansu ba?" Girgiza kai tayi tace "Dada ba za'a samu ba insha Allahu, karki manta irin taimakon da Aminu ya min, ya zama kamar wani garkuwata ne shi tsaka a filin dagar da babu bil'adam sai bak'ak'en hallitu masu shan jini." Jinjina kai tayi cike da gamsuwa tace "Gaskiya ne Faduma, wannan alfarma ba zata gagareshi ba." Rik'o hannunta tayi tace "Amma Fati ya kamata ki cire tsaron Tagur d'in nan a zuciyarki, kin san shi ya sanki bai kamata ace har yanzu kina shakkarshi duba da abinda ya faru." Wani murmushin takaici tayi tace "Dada, kinsan da yau har fuskar Tagur na mara cikin rawar jiki?" Murmushi Owwo tayi tace "Ni kam nasan sai dai a rawar jiki zaki iya marinshi, amma duk da haka kin min daidai." Mik'ewa tayi tana fad'in "Bari na shiga na shirya Dada, zan had'a kayan Amjad ma." Mik'ewa tayi ita ma tana fad'in "Bari na had'a masa kayan nasa, kije ki shirya kema." Wucewa tayi tana fad'in "Nagode Dada." _______________ Yau ma da safe shi ya kai yaran makaranta da tunanin sake had'uwa da tattausan fuskar murmushinshi, shiyasa ko da mai adaidaitarsu ya zo ya bashi hak'uri yace ya tafi zai kaisu, amma sai dai kash ko da aka ce ba'a karatun kuma ya zauna har kusan lokacin sai yayi tunanin ta yiwu har sun zo sun koma suma, sai kawai suka koma gida ya maida yaran ya aje. Abinda ya jima baiyi ba yau sai gashi yayi, kai tsaye babbar masana'antarsu ya wuce, masu gadi biyu da kayansu iri d'aya ne suka bud'e mishi ya shiga suna gaishe shi, a daidai harabar ajiye motoci ya paka, yana tsayawa masinjanshi ne yayi saurin bud'e masa murfin, saida ya kashe yana sauke ajiyar zuciya kafin ya zuro k'afarsa mai d'auke da takalmi na fata kalar ja mai duhu, k'arasa fitowa yayi yana mik'awa matashin daya zube k'asa yake gaishe shi, kuma wannan ladabin na d'aya daga cikin dalilin da yasa bai d'auki babban mutum ba, karb'ar wani babban littafi yayi mai kama da kundi ya mik'e yana bayanshi shi yana gaba. Duk da rashin maganarshi ga matashin hakan bai sa yaji ba dad'i ba, yanda ya sanshi dama yasan ba mutumin surutu bane, a hankali yake take masa baya har suka isa k'ofar shiga ciki, wani mai gadin ne da irin kayan waccen ma'aikatan na k'ofar, bud'e musu yayi suka shiga yana gaishe dashi shima, da hannu kawai ya amsa yana kallon katafaran kampanin, mutane ne birjik ta ko ina kuma kowa da aikin da yake wanda yasha mishi kai, wanda suka ga shigowarshi ne kawai suke gaishe shi daga inda suke yana amsa musu da kai, a haka har ya shige ofishinshi ya nemi tanfatsetsiyar kujerar dake ofishin ya zauna ta zaman mutum uku, madadin yayi zaune saiya cire takalmin daga k'afarshi ya aje makullin mota ya kwanta yana kallon sama ya d'ora hannunshi saman goshi ido rufe, duniyar tunani ya fad'a, daidai da wucewar kowani sakan (second) fuskarta gifta mishi take, abune mai wuyar fassarawa yake ji a game da ita, *daga kallo d'aya* yaji abun ya shige shi, a yanzun sai yake ji kamar wata jarabta ce a gareshi, duba da Saudat ma daya mata irin haukan son nan yanzu gashi tana gasa mishi aya a hannu, yana tsoron ita ma ta zama hakan kuma ma babu tabbacin zai same ta, ko sunanta bai sani ba bare inda take rayuwa. K'wank'wasa k'ofar akayi tare da turowa aka shigo, duk da yaji amma bai bud'a ko ido ba bare ya ga wanda ya shigo, saida ya k'arasa kusa dashi ya zauna kujerar mai zaman mutum biyu yana fad'in "Elhaj ashe ka shigo? Tashi ka gani to." Numfashi kawai ya sauke yana jinjina lallai Mukhtar baka da hankali, banza ya mishi har saida ya sake cewa "Elhaj." Hannunshi na dama dake kan cikinshi ya d'ago ya k'yastashi ya mishi alama ya tashi ya fita, murmushi yayi yana fad'in "Yau yan arzik'in ke bisa kai kenan?" Tab'e baki yayi ya aje masa takardun daya shigo dasu yace "To idan ka sauko saika duba wannan zanen, idan yayi ko a waya ka kira ka sanar dani, ina so ne na bayar da oda a bugasu, wani boutique ne ke buk'atar atampopin." Juyawa yayi ya fita duk da haka bai bud'a idonshi ba har yaji fitarsa, ajiyar zuciya ya sauke ya laluba hannunshi ya ciro wayarshi a aljihu, sai lokacin ya bud'e ido yana dannawa, lambar ya nemo ya kafe da ido, murmushi kawai ya saki saboda kallon sunan daya saka a lambarta, sai ya danna ok zai kira sai kuma yayi saurin katse kiran. _______________ Ko da suka dawo gidan Aisho ta tarbe su, amma yanda yanayinsu yake ya tabbatar mata da ba lafiya ba, saida ta kawowa Hatimi ruwa tasha cike da kulawa ta kalleta tace "Ayya lafiya? Ya naga duk kunyi sanyi? Ko dai bakuyi nasara bane?" Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleta tace "... *Yawan sharhi yawan rubutu*
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD