CHAFTER 1
Cike da kissa da k'warewa cikin salo mai birgewa ta kalleta tace "Malama Farida, kin tabbatar bayan alak'ar aiki dake tsakaninki da mai gidanki babu wata alak'ar?"
Cike da rashin gaskiya murya k'asa k'asa tace "Eh babu."
Faffad'ar takardar hannunta ta nuna mata tace "Wannan takardar na d'auke da jerin bayanan kiran wayar dake shiga da fita tsakaninki da Alhaji Sunusi, zaki iya fad'awa kotu akan me kuke tattaunawa haka da a k'alla kullum kukanyi waya sama da sau goma sha biyar?"
Rarraba ido ta shiga yi cikin rashin gaskiya tace "Mafi aksari munfi tattaunawa akan abinda ya shafi aiki, matsayina na sakatariyarshi (secr******) yana kirana a waya ko ni na kirashi kan wani abu da yake son umartata ko kuma ni na tambayeshi."
Jinjina kai tayi tace "Kina da masaniya akan kowace doka cewa ba'a yarda wata haramtacciyar alak'a na shiga tsakanin ma'aikaci da ubangidansa ba?"
Saida ta had'e fuska alamar jin haushin tambayar sannan tace "Eh na sani."
Jinjina kai tayi tare da kyab'e baki tana sake had'e hannayenta tana mitsitsikasu tace " Ranar 26 ga watan 11 shekara ta 2020 kinje ofishin Alhaji Basiru, zamu iya sanin me ya kaiki?"
Da sauri kamar yanda aka horeta akai tace "Ni banje ofishin shi ba, ban je ba."
Cike da son tabbatarwa tace "Baki je ba?"
"Eh." Ta fad'a tana sake gimtse fuska, murmushi tayi ta nufi teburinta ta d'auko wasu hotuna ta dawo gabanta ta mik'a mata tare da fad'in "Kin gane wacece a jikin hoton nan?"
Tana kallon hoton ta d'ago tana wuk'il wuk'il da ido ta kasa cewa komai, jin shirun yasa ta karb'ar hoton ta juya ta kai wa magatakarda tare da fad'in "Ya mai shari'a wannan duk da tace bata je ba amma ga zahiri nan, a ganinta da kuma tunaninta shigar dare tayi tare da b'atar da kammaninta dan haka babu mai ganeta, amma inda asirinta ya tonu shine akwai cctv cam*** a wani kampanin sarrafa leda dake kusa da ofishin Alhaji Basiru inda tanan ne muka samu damar ganinta."
Da sauri lauyen dake kare gwmnati ya mik'e yana fad'in "Objection, ya mai shari'a wannan ba hujjar da zata gamsar bace duba da yanzu babu abinda computer batayi, za'a iya had'a wannan hotunan dan ganin an cimma buri akansu."
Da sauri ita ma ta kalli alk'ali tace "Babu wannan nufin a tsarinmu, babban mutum ne da aka ci zarafinshi wanda ta kai har iyalinshi na kallonshi da abun, b'ata dare nayi da rana wajen ganin na tabbatar da mai gaskiya dan a mishi adalci ko da kuwa shi kanshi Alhaji Basiru ne."
Da hannu kawai ya mata alama da zata iya ci gaba, sunkyyawa tayi tana rik'e da gefen gefen rigarta bak'a ta lauyoyi wacce ta mata kyau, sake juyawa tayi kan budurwar dake tsaye ta taka gabanta yayin da sautin takalmanta ke fitar da k'ara mai dad'in sauraro wacce ke tabbatarwa da mai sauraron an iya sarrafasu, kafeta tayi da ido "Malama Farida a duk sanda wata ya zo k'arshe ma'aikata da dama sukan je poste poste wasu kuma wajen casher na masana'antarku dan samun kud'in aikinsu, amma abu guda dake da d'aure kai shine, sanda ma'aikata ke ta shan gumi da zafin rana da turmutsutsu dan samun hakk'insu, ke kina gida kwance kina hutawa kike jin naki alerte d'in ta account d'in da daga ke sai mai gidanki ne ke da iko shiga ko fitar da kud'i ta asusun, me yasa?"
Sunkuyar da kai tayi kamar zatayi kuka ta rasa abin fad'a, cikin muryar rashin wargi tace "Ke nake sauraro malama Farida."
A hankali ta d'ago idonta taf da k'walla tace "Kamar yanda na fad'a miki ne babu komai tsakani na dashi, ni ban san komai ba wallahi."
Kallonta tayi tace "Ba amsar tambayata kika bani ba."
Kallonta tayi kamar ta kifa mata mari dan haushi tace "A kullum yana yaba k'wazona da hazak'ata, hakan ne yasa bana bin layi yayin karb'an albashi na."
Wani murmushin takaici tayi tare da juyawa ta nufi inda take zaune, wasu takardu ta bud'a tare da d'auko wasu a takardu, nufa tayi wajenta ta nuna mata wani hoto tace "Kin gane a i'na aka d'auki hoton nan?"
Tana d'ora idonta akan hoton take taji tasu ta k'are, rarraba ido ta shiga tana hangen tululen Alhajin dake zauna sai gumi yake shima yana k'yak'yabta mata ido alamar kar tayi magana, juyawa kawai tayi ta nufi gaban teburin da magatakarda suke tana nunawa alk'ali tana fad'in "Ya mai girma mai shari'a wannan hoton tabbaci ne na alak'ar dake tsakanin Farida da ubangidanta Alhaji Sunusi."
Mik'awa magatakarda tayi ya mik'e ya karb'a shima ya juya ya mik'awa alk'ali inda ta sake nuna wata takarda ta mik'awa magatakarda tare da fad'in "Wannan takardar ita zata fallasa mana sirrin dad'ewarsu a tare, ba jiya ko shekaran jiya bane bare a danganta alak'arsu Alhaji Basiru, domin kuwa wannan takardar shaidar zubar da ciki ne da aka ma ita Farida da kuma saka hannun Alhaji Sunusi da amincewarshi shekara uku baya."
Bayan ya karb'a ya sake bawa alk'ali inda ta ci gaba da fad'in "Bayan rayuwar da sukeyi da kuma aikin zahiri akwai na b'oye wanda ba kowa ne ya sani ba, a duk sanda wani ya so takara dashi a cikin harkarsu ko kuma ya nemi kawo masa cikas a tafiyarshi Alhaji Sunusi ya kan saka Farida ta ribaci mutumin, da irin haka sunyi nasara akan mutane da dama, daga ciki kuma shine Alhaji Basiru."
Nuna d'aya Alhajin tayi dake tsaye gefe d'aya cikin damuwa ta ci gaba da fad'in "Tabbas Alhaji Basiru ya bayar da rahoton ingancin kayan da gwamnati ta siya a kampanin Alhaji Sunusi, sai dai abisa tilas ne yayi haka da fin k'arfinshi da akayi."
Lauyan gwamnati ne yayi saurin mik'ewa har da buga tebur yana fad'in "Objection, mai shari'a babu ta yanda za ayi ace tirsasashi ne akayi, babban mutum kamarshi da yake cikin tsaro zaiyi wuya hakan ta faru dashi ba kuma tare da an fahimci hakan ba."
Kallonshi alk'ali yayi yace "K'orafi bai karb'u ba, muna gaf da jin k'arshen shari'ar ne."
Zaune yayi cikin rashin jin dad'i inda ta juya ita kuma tace "Nagode mai shari'a."
Kallon Basiru tayi ta kuma kalli Farida tace "Mai shari'a malama Farida tayi anfani da damarta na kasancewarta mace ta ja ra'ayin Alhaji Basiru har ya biye mata, bayan ta samu abinda take kuma sai tayi anfani da hoton data d'aukesu tare saboda daman an shirya hakan, da wannan hotunan ta dinga mishi barazana dole ya saka bayanin da suka dace akan kayan nan, shi kuma tsoron karya rasa mutumci da kimarsa yasa shi rubuta kayan masu kyau ne, wanda gashi yanzu sanadiyar haka gwamnati ta shigar da k'ararshi tana neman tara mai yawa bayan kuma ta koreshi a aikinshi, ya mai shari'a a duba wannan lamarin a bi mishi hakk'inshi, nagode."
Ya d'auki tsawon minti biyar yana rubuce rubuce kafin ya d'an tattara takardun gabanshi ya d'ago yana waina biron hannunshi yace "Abisa shedun da duka lauyoyin b'angarorin suka gabatar, kotu tayi dogon nazari tare da fahimtar cewa Alhaji Basiru baya aikata laifin nan bane da son ranshi, uzurin magud'i da *zanba cikin aminci* ne suka haddasa haka da kuma son zuciya, saboda haka kotu ta wanke shi, sai dai zai biya tarar da gwamnati ta buk'ata ba tare da b'ata lokaci ba, dalili kuwa yana da hannu a cikin asarar da gwamnati ta tabka wajen rugujewar ginin da take ginawa, sannan hakan zai iya zama darasi a gareshi ko dan gaba domin kiyayewa."
Ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon Basiru da shima ya sauke tashi ajiyar zuciyar, a tare suka sake mayar da kallonsu kan alk'alin daya ci gaba da fad'in "Siyar da gurb'ataccin kaya da basu da inganci, tilastawa jami'in gwamnati wajen saka hannu yayin da aka ribace shi da mace, hakan yasa kotun nan ta samu Alhaji Sunusi da laifi dumu dumu, abisa haka kuma kotu ta yanke mishi hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekara hud'u tare da biyan tara ta jumallar kud'i million 25. Farida kuma kotu ta yanke mata hukuncin zama a gidan yari na shekara d'aya sakamakon taimakawa da tayi."
Gudumar gabanshi ya buga sau uku wanda yasa mutanen ciki mik'ewa, ta k'ofar baya ya shige sannan mutane suka fara fita kowa bakinshi cike da tsegumi, tunda aka kamasu zasu tafi kowa ke hararenta, ko a jikinta sai ma hanzari da take na ganin ta tafi sabgarta ta gaba.
Tana barin nan gidan wani alk'ali taje wanda ke ma wasu shari'a a gidanshi akan sulhun bashi, ko da taje nan ma ta samu d'aya lauyen yaje, bata b'ata lokaci ba wajen fito da wasu takardu a jakarta ta ordinateur (computer) d'inta ta shiga mik'awa dattijon tana fad'in " Alk'ali wannan takarda tana d'auke da yarjejeniyar da sukayi kafin gabatar da harkar, idan ka duba zaka ga *Lawan* ya karb'i kaya na million biyar a hannun *Usman*, amma a cikin rubutun da sukayi akwai abinda Lawan ya fad'a cewa ya karb'i kaya a hannun Usman zai rarrabawa mutane, yayi alk'awarin zai biya bayan wata uku, sannan Usman ya rubuta cewa ya amince Lawan zai biyashi bayan wata uku."
Wasu re** re** (r****) ta fito ta mik'a mishi ya karb'a tana fad'in "Wannan re** na shaidar kayan daya bawa mutane ne, a shagonshi na samo su a hannun yarenshi, alamu sun nuna ya bawa mutane kayan shima amma ba'a biyashi ko sisi ba."
Marairaicewa tayi da cewa "Da wannan nake neman alfarma a wajenka daka saka hannu a sallami mutumin nan, dan ta hakane kawai zai samu damar da zai karb'o kud'ad'en a hannun mutane shima, amma kama shi da akayi aka rufe bashi ne zaisa ya fito da abinda baya da shi ba, sannan shi ma Usman d'an kasuwa ne, kuma kowa yasan k'alubalen da ake fuskanta yanzu a cikin kasuwa, nagode alk'ali."
D'aya lauyen da tunda ta fara magana yake hararenta ta wutsiyar ido, baisan a gidan uban wa ta samo hujojjin da yake tunanin duk ya karb'esu ba? Baisan ya akayi ta same su ba har ta gabatar, a tsarin shari'ar wanda ya shigar da k'arar yana so ne a kasa samun belin Lawan, ta yanda a k'arshe za'a d'aga babbar kadarar Lawan d'in ta wani fili daya siya ya kuma tsonewa Usman ido, amma gashi ga dukan alama zasu samu belinshi.
Bayan rubutun da yayi ne ya mik'a mata wata takarda yana fad'in "Lauya Faduma an baki belinshi, sai dai yanzu yana da wata d'aya da rabi na biyan bashin."
Da farin ciki ta karb'a tana mik'ewa da fad'in "Nagode alk'ali, sai anjima."
Tana shiga mota da sauri ta isa commissariat, tana isar da takardar aka bata shi, suna fitowa ta kalleshi tace "Dan Allah Lawan kayi k'ok'arin biyan kud'in nan akan lokacin da aka bamu, alamu sun nuna kamar Usman baya nufinka da alkairi, dan lokacin da naje shagonka bincike yaren sun fad'a min wani lauya ma ya zo yace shine mai kareka, dan haka ka kula sosai kaji."
Jinjina kai yayi yace "Insha Allah Faduma, nagode sosai."
Saida ta kama murfin motarta tace "Ba damuwa, ina sauri zan je na d'auki yarona a makaranta, ba dan haka ba dana ajeka gida."
Murmushi yayi yace "Ba komai wallahi, kije Allah ya kiyaye hanya."
Shiga tayi tana tayar da motar tana kallon agogon hannunta, gudu take sosai dan bata so ya jirata sosai. Ai kuwa tana isa bakin ***** d'in *Wangari* ta hangeshi a cikin gomannin yara, murmushi ta saki sanda ta paka motar gefe ta sauke gilashi tana kallonshi. A hankali kyakyawan yaron ya shiga duba kowace kusurwa na titin, saida ya tabbatar babu hatsari kafin ya tako cikin nutsuwa.
Bud'e motar yayi ya shigo yana fad'in "Ayya sannu da zuwa?"
Kallonshi tayi tana tayar da motar tana murmushi tace "Yawwa yarona, Nukoy (Ya kake)?"
Da murmushi shima ya amsa da "Leyge (lafiya lau) Ayya."
Cikin farin ciki da hira har suka isa quartier zaria 2, matsakaicin gida ne ginin zamani daidai rayuwar mai k'aramin k'arfi, wuri ta samu ta paka suka fita yana rik'e da jakar ordi. d'inta suka shiga ciki, da sallama duka a bakinsu suka shiga inda matar gidan ta amsa musu ita ma da farin ciki. Gaisheta sukayi ita ma tana musu sannu da zuwa, kallonta tayi tace "Ki shiga kiyi wanka saiki fito ga abincinku nan."
Da murmushi ta wuce ciki tana fad'in "To Dada (Tanti), yau me kika dafa min?"
Kallonta tayi tace "Me na dafa miki ko me na dafawa shalelen angona?"
A hankali yaron ya kalleta cikin nutsuwa sosai yace "Me kika dafa min dara nra (masoyiyata)?"
Dariya tayi tace "Ka fara shiga ka cire kayan saika zo ka duba da kanka."
Shigewa sukayi ciki, a d'an k'aramin falon yana d'auke da d'aki hud'u a kowane b'angare sai ban d'aki daga d'aya b'angaren a nesa da sauran d'akunan. Bayan wasu mintuna ta fito cikin riga da siket na atamfa, masha Allah tubarkallah lallai kaya rufin asiri ne, kyawun Faduma da tsarin hallitarta ya kai matakin da kowane namiji ya kalleta a zahirancenta zai tsaya bawa idonshi hakk'insu.
Doguwa ce mai diri da direwa sosai, komai na jikinta daidai yake da ita da tsarin hallitar fuskarta, duk da ba fara bace amma bak'inta mai kyau ne, idan kayi duba da yanayin gidansu da aikinta kasan ba majiya dukiya bane, amma kasancewar al'adarta tsabtarta da kuma kulawa da kanta da take yasa fatarta take wani shek'i da d'aukar ido.
Kasancewar babu d'an kwali a kanta kitson kanta ya bayyana, lahaula kawai zata tofa dan gudun baki, gashin kanta bak'i sid'ik mai yalwar gashi tsayi da yawa, gashi kuma yasha kutso k'anana mai bala'in kyau da birgewa ga mai kallo. Zaune tayi tana jawo kwanon da Dada ta aje mata ganin ta fito, tank'washe k'afafunta tayi ta bud'e kwanon, hannu tasa ta fara ci bayan tayi bismillah, *Amjad* ne ya fito shima ya canza kayanshi, zaune yayi ta bashi nashi abincin shima ya bud'e, kallonta yayi yace "Nagode dara nra."
Kallonshi Faduma tayi ta jawo kwanon, tana gani tayi murmushi ta kalleta tace "Dada lallai abinda angonki yafi so kika dafa masa."
Cikin murmushin ita ma tace "Abinda ke kuma kika tsana ba."
Murmushi kawai ta sake yi tace "Humm."
Shiru sukayi babu mai magana har saida Amjad ya riga idawa ya tashi yana fad'in "Ayya zanje na kwanta kafin ayi sallah azahar ki tashe ni."
Da murmushi a fuska ta kalleshi tace "To."
Da kallo tabi bayanshi har ya shige, saida ya b'acewa ganinta ta saukr ajiyar zuciya, ta mayar da dubanta kan kwanon sai taga Dada na kallonta, saida ta kai loma baki ta kalleta tace "Ya dai Dada?"
Murmushi ta shiga yi tan girgiza kai na wani lokaci kafin tace "Faduma kenan, saboda k'iyayyar da kike masa fa kika hana kanki cin biski da miyar taushe mai busashen kifi, sai gashi kuma d'anki ya fi son wannan abincin fiye da kowane."
Ba tare da damuwa ba tace "Dada Amjad shi ya so wa kansa, saboda ya had'a jini dashi ne shiyasa, ni kuma babu abinda na had'a dashi."
Cikin murmushi tace "Gaskiyarki kam."
Tana idawa ita ma ta tashi ta koma d'akinta ta kwanta, ordi. ta d'auka tana daddawa dan ci gaba da binciken aikin dake gabansu yanzu da basu da adadi har bacci ya d'auketa.
K'arfe biyu ta farka ta d'auro alwala tayi sallah, saida ta d'ora farar lafaya kan riga da wandon data saka sannan ta fito, a falon ta samu Amjad cikin shirin makaranta yana duba littafin makarantarshi, saida ta nufi k'ofa tace "Muje ko."
Kallonta yayi yana mik'ewa yace "Ayya tun yanzu? Na shirya ne fa dan karki jirani dayawa, da sauran lokaci har yanzu."
Juyowa tayi ta tsaya tana kallonshi tace "Amjad akwai inda zanje ne, idan na barka wa zai kai ka? Muje kawai jiran minti nawa ne zakayi?"
Saida ya d'an turo baki yace "Ayya gaskiya ni..." Shirun da yayi yasa ta kallon fuskarshi tace "Uhum?"
Girgiza kai yayi alamar ba komai, fitowa sukayi inda Dada ke zaune, kallonta tayi tace "Dada zan kaishi makaranta, daga nan zan wuce office d'in *Aminu* ne."
Da fara'a tace "To Faduma sai kin dawo."
Amjad ta kalla tace "Angona saika dawo."
Jinjina mata kai yayi alamar to, a daidai k'ofar fita suka tsaya ita da shi, hannayensu suka d'aga inda Amjad d'in ne yayi addua'r fita daga gidan "Bismillah, tawakaltu Allahlah, lahaula walaquwata illa billah."
Yana idarwa suka fita a tare, a hanyarsu ta tafiya kamar yanda suka saba tana tambayarshi a cikin karatun yan aji shida yana bata amsa, suna isa ta aje shi ya fita ya zagayo ta b'angarenta, kallonshi tayi ita ma tace "Allah ya tsare min kai yaro na, ka maida hankali kan karatunka kaji."
Jinjina kai yayi tare da fad'in "Insha Allah Ayya, sai anjima."
D'aga masa hannu tayi har saida ta ga shigewarsa kafin ta wuce, bata jima a hanya ba ta isa bureau d'in, kamar yanda yasan da zuwanta kai tsaye ta shiga ciki, bayan sun gaisa ne take tambayarshi akan matsalar da yake aiki kanta danta taimaka mishi kamar yanda shima yake taimakonta, bayan ta duba takardun daya bata ne tare da k'arin bayanin daya mata ta kalleshi tace "Aminu to me ka fahimta a game da shari'ar ne?"
Gyara zama yayi yace "A gaskiya akwai abun d'aure kai, da fari meye dalilin da yasa ita tace ya daketa shi kuma ya musa akan haka?"
Saida ta d'an buga teburin tace "Tambayar farko kenan, kasan wani abu?"
Girgiza mata kai yayi har saida ta d'ora da "Abinda na lura dashi kamar akwai abinda waninsu ke b'oyewa, amma zamuyi bincike mu gano gaskiyar, tunda dole a cikinsu akwai mak'aryaci."
Jinjina kai yayi yace "Hakane, to ya za ayi kenan yanzu?"
Cikin jinjina kai tace "Ni zan sake bincikawa, amma kana ganin zai yiwu ace mashayi ne kamar yanda matar ta fad'a?"
Murmushi yayi yace "Bamu da tabbbas gaskiya, amma bincike ne zai tabbatar mana da gaskiya."
Da hanzari tace "Yanzu abunyi to ka je ka samu mijin ku tattauna, ni zanje gidan saina sake duba mana wani abun."
Jinjina kai yayi yace "To shikenan."
Saida ta saka k'aramar yatsarta a baki tana d'an cirar akaifa na wasu mintoci kafin ta kalleshi daga bisani tace "Ka lura da komai a tsanake ka fahimci yanayinshi, idan ta kama ka mishi tambayar da zata harzuk'ashi kaga shin zai iya duka idan ranshi ya b'ace ko kuwa."
Jinjina kai yayi yana fad'in "Angama."
Mik'ewa tayi tsaye sukayi sallama ta fita, daga nan hanyar gida ta d'auka tana tunanin abunyi.
Saida ta gabatar da sallah la'asar da taga lokacinta yayi kafin ta fito ta kama girki, k'anwar mahaifiyarta *Owwo* na zaune tana had'a turaren wuta da take na siyarwa abun suna hira, zuwa biyar da rabi ta kammala tayi wanka ta shirya, fitowa tayi cikin wata lafaya mai ja da bak'i wacce ta mata kyau sosai, kallonta tayi tace "Dada zan je d'aukar Amjad."
Da tausayawa ta kalleta tace "Faduma kina k'ok'ari sosai akan yaronki, Allah ya baki ladar d'awainiya da kikayi dashi, Allah yasa mai tausayinki ne shima."
Murmushi tayi tace "Dada kin manta duk kece silar tsayuwata da k'afafuna, Dada kin fini cancantar addu'ar nan."
Girgiza kai tayi tace "Kin cancance ta Faduma, dayawa irinki wasu jefar da yaran ma sukeyi, wasu kuma su kashesu da hannunsu, wasu ma kashesu sukeyi tun kafin su haife su."
Saida ta d'an numfasa tace "Amma ke kin rabu da iyayenki ma saboda ki tseratar da d'anki, sannan gashi kin bawa komai baya rayuwar d'anki kawai kika saka a gaba, ko soyayya ba kyayi bare maganar aure."
Wata irin dariya tayi wacce tasa dumple d'inta fitowa sosai akan kumatunta tare da fad'in "Dada soyayya? Ni Faduma? Haba dai Dada, ya kike maganar soyayya akai na kamar wacce bata san soyayyar ce ta jefa ni halin da nake ciki yanzu ba?"
Tab'e baki tayi ta juya zata fita tana fad'in "Sai dai a lahira kuma idan anayi."
Da sauri Dada tace "A'a wallahi Faduma ba dani ba, haka kawai zaki ce sai a lahira, maza ai suna suka tara, kuma ba duka suka taru suka zama d'aya ba, ko so kuke mu ci gaba da zama a haka ni dake ana zaginmu a gari ana fad'in na d'aure miki gindi?"
Ko juyowa ba tayi ba sai murmushi da ta ci gaba da dokawa har ta fita, cikin nutsuwa da salama ta isa makarantarsu, tana isa yayi daidai da tashinsu kuwa, yana hangota ya zo ya bud'e k'ofar ya shiga ya rufe, kallonshi tayi jin baiyi sallama ba bai kuma gaisheta ba kamar yanda ya saba. A hankali ta shiga fahimtar yanayinshi da kayanshi, saida ta fara tuk'awa sun d'auki hanya tace "Ban hanaka fad'a a makaranta ba?"
Sake rumgume jakarshi yayi ya shiga k'yabta ido yana kumburo baki, bata kalleshi ba saboda cunkoson dake akwai na yan makaranta ta ci gaba da cewa "Amjad da kai nake magana, da wa kayi fad'a? Me ma ya had'aka fad'a a makaranta?"
Cikin turo baki yace "Ayya yaron ne ya raina ni fa, kullum yana tsokana ta dan ya ga ina k'yaleshi bana biye masa, shine yau fa har da keta min littafina yayi da gangan, shiyasa muka cire raini yanzu ba zai koma ja na ba."
Da sauri ta kalleshi tace "Heeyeee Amjad, kana nemana da zaman lafiya kuwa?"
Cikin turo baki yace "Yi hak'uri Ayya."
Jinjina kai tayi tace "Amma ka kula daka keta kayanka ko?"
Saida ya duba wuyan rigarshi daya yage kafin yace "Yi hak'uri Ayya, ba zan sake ba."
Cikin kallonshi tace "Idan na hak'ura ubanka ne zai gyara kayan da suka lalace?"
Kallonta yayi baki bud'e yace "Ayya dama wanda ya mutu yana dawowa ne?"
Jim tayi ba tare data kalleshi na wani lokaci kafin a hassale tace "Kasan da haka kuma kake bani wahala? Yanzu saina siya maka sabbin kaya kenan."
A hankali ya sake cewa "Kiyi hak'uri Ayya." Bata tanka mishi ba har suka isa gida, daf da sallah magriba haramar sallah sukayi dukansu.
Da dare da k'yar ta samu sukayi karatun awa d'aya tare da Amjad kafin suka kwanta, amma ba baccin tayi ba sai binciken yanda za ayi ta gano gaskiyar mutuwar matar da ita dai take zargin mijinta ne silar mutuwarta, dare yayi sosai bata san sanda baccin yayi gaba da ita ba da gilashi a idonta dan rage hasken ordi. d'inta da kuma takardu duk a gabanta zube.
*Faduma kenan*, agogo sarkin aiki, zak'ak'urar lauyar data d'auki aikinta da mahimmanci tamkar yanda take son kasancewar rayuwarta a cikin farin ciki, ta kan hana idonta bacci domin ganin ta zak'ulo gaskiya daga muhallinta ta d'orata a inda ya dace ko da akan wanda ya bata aikin ne, tana da dokoki kafin ta karb'i case d'in ka, idan kuma ta karb'a babu abinda zai hanata kai k'arshenshi. K'wazonta shine sirrin nasararta, hak'uri da dagiyarta kuma sirrin karb'uwarta, bindiddigi da takatsantsan d'in ta kuma sune garkuwar aikinta. dogaro da kad'aita sarkin al'arshi shi kad'ai kuma suka zama linzamin d'aukakarta. Aikinta ba dan kud'i ko suna take yi ba sai dan *so*, tana yinshi ne dan tana son shi da gaba d'aya zuciyarta tun yarintarta har zuwa kawo yanzu girmanta.
Da safe Amjad ya shirya cikin riga da wando na islamiyya masu kyau ya d'auki littafi d'aya a hannunshi suka tafi, duk da akwai makarantu a wurin amma tafi gamsuwa da wacce take kaishi yanzu, ko da ta sauke shi kamar kullum sukayi sallama ta juya ta koma gida.
Suna zaune tare da Dada suna d'ura turaren wutar data gyara jiya a kwalabe Aminu yayi sallama, da sauri Faduma ta shiga waigawa inda zata ga ko da kallabi da zata d'ora a kai, dan ita ba ma'abociyar saka hijab ce ba idan ba sallah zatayi ba, lafaya sune kayanta ita kuma ba hijabi ake d'orawa akai ba. Kafin ta samu abun d'orawar har ya shigo saboda gidan ba bak'onshi bane, dole ta dakata tare da amsa sallamarshi ita da Dada, k'arasawa yayi yana fad'in "Kina gida ashe?"
Ba tare data kalleshi ba tace "Yanzu na dawo, ai na d'auka ba yanzu zaka taho ba."
Bai amsa mata ba saboda gaisawar da sukeyi da Dada, bencin dake kusa dasu ya zauna, sai lokacin ta d'aga kai ta kalleshi tana fad'in "Ya ake ciki Ami..n"
Bata k'arasa fad'a ba kawai tayi shiru ta sunkuyar da kanta, yanda ta ga idonshi a kanta duk sai taji ba dad'i, yanzu haka duk da kanta k'asa yake amma tana iya jin idonshi akanta, gata ita kuma riga da wando ne jikinta da suka kamata sosai, tana dawowa ta cire lafayar ta rataya kan wayar shanya kaya, ta wutsiyar ido ta lura da yana bud'a jakar daya shigo da ita, da sauri ta mik'e ta jawo lafayar a bayanta ta shiga d'aurawa a daidai nan ya juyo ya kalleta yana mik'o mata wata takarda wacce yake aikin wata k'ara a kanta Faduma kuma tana taimaka mishi kamar yanda suka saba yana fad'in "Duk abinda muka tattauna yana ciki."
Saida ta d'aure lafayar ta karb'a tana komawa ta zauna, kallonta Dada tayi kawai tayi murmushi, tana cikin dubawa ya mik'o mata wata takardar yana fad'in "Nayi magana da abokin nan nawa likita, shima dai amsar tana nan, sai kiyi nazari akan duka abubuwan da muka tattauna."
Jinjina kai tayi tana ci gaba da kallon takardun, numfasawa tayi ta kalleshi tace "Yanzu bureau zaka koma?"
Kao tsaye ya amsa da "A'a akwai inda zanje ne."
Jinjina kai tayi tace "Shikenan ba damuwa, nima anjima zanje na ganta muyi magana, amma idan zan tafi zan kiraka saika kaini."
Saida ta kalleshi tace "Ba wata damuwa a game da hakan?"
Murmushi ya mata sosai yace "Ko da damuwar ma ai kinsan babu ita tunda ke ce."
Murmushi ta masa suka mik'e a tare ya ma Dada sallama, bayanshi Faduma tabi har k'ofar gidan yana k'ara mata bayani da baki, cikin mamaki yace "A ganina dai gaskiya banga ta inda mutumin nan ke da kazar kazar d'in duka ba, komai nashi cikin sanyi yake yinshi har da maganarshi ma, duk yanda nake ganin na kai ga zafafa kalamai gareshi dan yaji haushi sai naga duk yanayi d'aya ne a fuskarshi, yanayin tausayin kanshi kamar wani mata-maza."
Dariya tayi sosai har tana sunkuyar da kanta hakan kuma ya sa shi kafeta da ido yana kallonta, saida ta d'an tsagaita tace "Tun a karon farko na fahimci matarshi hatsabibiya ce, duba da yanayin jikinta da nashi zai iya ja masa raini a gurinta, amma zaka iya tuna ranar da aka shiga zaman farko ta fad'a a gaban kotu wai dukan da yake mata duk ya farfasa mata jiki?"
Cike da tanbaci yace "Eh, na tuna."
Jinjina kai tayi tace "Yawwa, yanzu idan kun sake zaman na gaba ka sake tabbatarwa saika nemi ta nuna muku inda ya mata tabo a jiki, bayan nan saika gabatar da duk wannan hujojjin."
Jinjina kai yayi tare da amsar takardun data mik'a masa tana fad'in "Insha Allah nima zuwa gobe zan je na ganta, hankalina ya rabu biyu ne shiyasa ba zan samu tafiya yau ba."
Gyara tsayuwa yayi yace "Kalamanki na nuna kamar ba zamu shiga kotu tare ba ranar litini."
Saida ta juya idonta masu haske sosai tace "Gaskiya ba zamu shiga ba, kaga duka ni da kai kowa yana da aiki, dan haka za dai mu had'u bayan kammala sauraran k'arar."
Ajiyar zuciya ya sauke yana mata wani shu'umin kallo yace "In kuwa hakane na miki alk'awarin zan sanar dake wata muhimmiyar magana amma fa idan nayi nasara a kotu, hakan ne kawai zai bani k'warin gwiwa."
Murmushi tayi sosai ba tare da kawo komai a ranta ba ita ma tace "Nima nayi alk'awarin fad'a maka wani abu idan har na samu nasara akan wannan shari'a, dan ka taimakeni sosai."
"Da gaske?" Ya fad'a yana mai kafeta da kallo, d'aga masa kai tayi alamar eh, murmushi yayi yace "Insha Allah zakiyi nasara ma, ai naga kamar a jininki take tunda baki tab'a fad'uwa ba."
Jinjina kai tayi tace "Sanin daka min kenan kafin mu had'u, ci gabana da nasarata kawai ka gani kuma ka sani, amma akwai tarin k'alubale da matsaloli dana fuskanta kafin nayi nasarar haye tsanin."
Jinjina kai yayi yace "Hakane, Allah yana tare dake a kullum."
Kallonshi tayi ta d'an murmusa tace "Ni zan koma ciki, sai munyi waya."
Da kai ya mata alama shima har ta shige ciki yana kallonta, ko da ta shigo ta zauna Dada ta kalleta tace "Faduma anya kuwa Aminu ba sonki yake ba?"
Cike da rashin jin dad'i tace "Daadaaa, Aminu ne fa, kinsan shi kinsan yanda muke da shi, abokin aikina ne kawai."
Murmushi tayi tace "Duk da haka, amma na fahimci haka ni."
Tab'e baki tayi tace "Ai kuwa ya d'ebo ruwan dafa kanshi, dan zai mutu babu aure."
Dariya Dada tayi tace "Ke ma kinsan fad'a kike."
Kallonta tayi tace "Allah kuwa Dada."
Tsawa ta mata tace "Dallah can daina wannan bak'in bakin malama, haka kawai da k'uruciyarki kina neman kashe kanki, aure bashi ne darajar 'ya mace ba, duk da kina ganin baki da matsalar ci da sha ai ko ba komai kina buk'atar garkuwa."
Shiru tayi ta ci gaba da abinda take bata tanka mata ba, cikin fad'a ta ci gaba da cewa "Baki ga yanzu duk idon dangi ya dawo kaina ba, tunda mijina ya rasu na gama takaba aka ce na koma gida na k'i, ni nayi hakane saboda anan nake samun abinda zan rufawa kaina asiri, nan nake da mutanen arzik'in da muka saba kusuwanci dasu, a gidan kuma banda tsirfa da tsegumi na kishiyar uwa da 'ya'yanta me zaka tarar, amma duk kallon mai zaman kanta yanzu suke min har suna ganin ni ke koya miki ma."
Kallonta tayi tace "Dada karki damu da abinda ake fad'a akan mu, karki manta sanda yan uwan mijinki suka so rabaki da gidan da mijinki ya mallaka miki tun yana raye, dana tsaya miki a kotu cewa ake ai dan muji dad'in karuwanci ne,