CHAFTER 2&3&4

5000 Words
Cike dgajuya da maganar da ta k'i ci ta k'i cinyewa ya sunkuyar da kanshi k'asa, babban limamin da suka saka a maganar ne ya sake kallon wani matashin da ba zai gagara shekara *talatin* a duniya ba, cikin jin hushin taurin kai irin na *Mujaheed* ya nuna shi da yatsa yace "To bari kaji Mujaheed, maganar nan na yanketa kuma ta yanku, wannan gidan ya zama mallakinsu *Salima* da *Halima*, tunda sun maka kara cewa zaka iya zama a ciki har sanda ka so to, in kuma kaga ba zaka iya ba ka tattara kayanka ka fice, amma bana son sake jin wata magana kuma a kan gidan nan, ka jini ko?" Cike da iskanci ya wani jijjiga kai yana hararen duk wanda ke d'akin yana fad'in "Ka fad'i haka mana tunda ai na samu labari kai d'in tsohon saurayinta ne, to kar kuga ni kad'ai uwata ta haifa wallahi ban yarda da rabon gadon nan ba, haka kawai sai a tattare duk wani abu mai daraja a bawa yan d'akin *matar so*, ni kuma da aka d'auka shege bare sai a bani wani banzan gida da yan kud'ad'e, tab' lallai ma." Kowa kallonshi yake da mamakin rashin kunyarshi, *Mukhtar* dake ta cika yana batsewa ne a hassale yace "Kai Mujaheed, liman d'in kake fad'awa haka? Wacece yake tsohon saurayinta? In ce dai ba uwata kake nufi ba?" Kallonshi yayi yana tab'e baki yace "Tunda ka sani me ye na saika tambaye ni to? Ita nake nufi mana, ko baka san labarin ba kai?" A sukwane ya mik'e zaiyi kanshi matar mai matuk'ar dattako da rashin son hayaniya ta d'aga mishi hannu cikin sanyin murya tace "Ya isa haka Mukhtar, bana so, karna sake jin maganarka." Komawa yayi ya zauna yana hararenshi tare da yin k'wafa mai k'arfi, liman d'in ne yaja numfashi ya sake kallonshi yace "Ina da iko da zanyi maganin rashin kunyarka, amma ni babba ne kuma mai hankali, k'aramin tsagera irinka bai kai na b'ata lokaci na kanshi ba, amma kamar yanda na fad'a maka zan sake maimaita maka, wannan gida gadon Salima da Halima ne, idan kuma akwai wanda ka isa ka turo ya k'watar maka to ina jira, takardun na hannuna ka aiko shi na gani." Mik'ewa tayi tsaye yana gyara babbar rigarsshi irin ta malamai mai bud'add'en gaba babu wuya sai hannaye kawai bak'a, kallon *Maryama* yayi yace "Mari ni zan tafi, ku ci gaba da hak'uri kamar yanda kika saba, sai anjima." A hankali ta amsa mishi da "Sai anjima liman, mun gode sosai." Kallon wannan matashin yayi wanda har yanzu kanshi ke sunkuye yana ta juya zoben hannunshi, saida ya tsaya gabanshi ya dafa kanshi yace "Ni zan tafi *Hasheer*, kuyi hak'uri kaji? Allah ya muku albarka." A hankali ya d'ago kanshi ya zuba cikin na liman, d'auke hannunshi yayi daga kanshi yana sake kallon idonshi da sukayi matsanancin ja sosai, inda ya kama leb'enshi na k'asa ya cije gam har rawa rawa yake, bai ce komai ba ya sake sunkuyar da kanshi yana d'an jinjina kai alamar to, saida liman ya sauke ajiyar zuciya dan b'acin rai tsagwaronshi ne ya hango a cikin idon Hasheer d'in wanda ke nuni da komai zai iya faruwa ya bar gidan nan a haka. Cikin dubara ya sunkuya ya kamo hannunshi yana fad'in "Muje ina son magana da kai." Saida ya had'e wasu yawu masu nauyi da suka tokare mishi mak'oshi sannan, cikin sanyin jiki ya mik'e ba tare daya had'a ido da kowa ba ya shige gaba ya fita a falon, da tsaki Mujaheed ya bi shi yana fad'in "Aikin banza, banda jan idon me ka iya? Sakarai lusari." Suna fita Maryama ta mik'e tsaye ta kalli Salima da Halima dake zaune da hijabansu tace "Ku tashi ku wuce d'akinku." Da sauri duk suka mik'e suka nufi d'akin nasu, wata uwar harara Mukhtar ya sake watsa mishi yana fad'in "Wallahi ka kiyayi ranar da zamu had'u da kai, saika manta da cewa k'asa nake da kai idan na maka jina-jina." Mik'ewa yayi ya nufo kanshi yana fad'in "Kai ni kake wa rashin kunya? Ko waccen yayan naka me kaga yayi dani? To zanyi maganin rashin kunyarka wallahi." Tsaki yayi yace "Dallah can malam, ai saboda shi baida lokacin ka ne, idan yace zaiyi da kai a k'ank'anin lokaci tarihinka zai k'are." Da sauri ya k'araso yana fad'in "Kai ni zaka fad'a ma haka? Zanyi maganinka yanzu kuwa." A hassale Mujaheed ya shak'i wuyan rigarshi, shima baiyi k'asa a gwiwa ba ya ci tashi kwalar rigar dan duka bai wuce watanni ne Mujaheed ya bawa Mukhtar d'in, jin dukansu sun kawo k'arfi sun kuma matse junansu sosai har idonsu sun fara raina fata musamman ma Mujaheed, dan Mukhtar ya fishi zubin k'arfi hakan yasa yafi jigata, ganin dai shi zai mutu a banza yasa shi cewa "Sake ni to." Wani kallon raini ya mishi yace "Ni ma sake ni." Sakeshin kam yayi yana fizge rigarshi shima yana fad'in "Sake ni to." Sakinshi yayi shima yana murmushi yace "Na fad'a maka ai ka kiyaye, wallahi ranar daka bari na rik'e mak'ogwaronka saina raba wuyanka dashi." Gyara rigarshi yayi ya nufi k'ofar fita yana fad'in "Marar kunyar banza." Cike da borin kunya yace "Kai ni kake fad'awa haka? Zaka gane kurenka yaro." Bin bayanshi yayi shima ya fita yana ci gaba da bubbutai. Tunda suka fita da liman ba komai ya fad'a masa ba sai sake jadadda masa hak'uri da kuma falalar yin shi da ribar da yake janyowa, saida yaga yana sauke ajiyar zuciya kawai idonshi sun fara washewa sannan ya mishi sallama, dawowa yayi cikin gidan ya nufi nashi b'angaren yana jin zuciyarshi na mishi sanyi na kalaman liman. Yana yaye labulen da sallama murya k'asan mak'oshi ya shiga, bai kula da yanda falon yake ba dan tun shigowar farko haka ya same shi, kai tsaye d'akinshi ya nufa da niyyar shan maganin ciwon kai ya kwanta, yana tsaka da neman maganin yaji an shigo d'akin, bai juya ba dan tunda bai ji sallama ba yasan wacece, a hankali bai ankara ba yaji an kwanta a bayanshi ana rumgumeshi ta baya ana fad'in "Abban *Sharfudeen* shine ka shigo baka nemeni ba ko?" Wani murmushin da baisan lokacin da ya zo mishi bane ya kubce mishi, rainin hankalin mutane dayawa yake, abinda ya ayyana a ranshi kenan, shi dai yasan haka kawai *Saudat* ba zata zo inda yake har da wannan salon a banza ba, dan haka ya warware hannayenta data mishi sakata dasu ta baya ya juyo ya fuskanceta, kallon fuskarta yayi sosai tasha kwalliya kam tayi tsaf, shigowar d'azu da rigar bacci tun ta kwanan jiya ya sameta, amma yanzu harta shirya da wani abu kenan, ganin yanda ya tsareta da ido sai kawai gabanta ya fad'i ta sunkuyar da kai, bai daina kallonta ba har saida ta gaji ta sake d'agowa, shagwab'e fuska tayi sosai kalar d'aukar hankali ta marairaice ta kama mab'allin rigarshi tana gyara mishi tana fad'in "Abban Sharfudeen, wallahi na manta ban fad'a maka ba tun jiya wata k'awata ta haihu har yau ake suna, shine yanzu *Murja* ta kirani take tambayata har na tafi? Shine nace mata ni na manta ma amma yanzu zan taho." Gani kawai tayi ya d'anyi wani murmushi mai ban mamaki da saka mutum tunanin murmushi, amma da yake ba hankali ne da ita ba sai kawai ta turo baki gaba tace "In je?" Jinjina mata kai yayi alamar eh, murmushi ta saki ta dafe fuskarshi da hannayenta ta sumbaci kumcinshi, juyawa tayi ta fita da sauri tana fad'in "Saina dawo." Wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi tare da dafe k'irjinshi da yaji ya mishi nauyi yanzun, da yasan abinda zai tarar kenan da bai shigo gidan ba ma, zaune yayi bakin gadon ya dafe kanshi da hannu biyu ya ma manta da neman maganin da yake, tunani ya shiga yi na irin yanda Saudat ta mayar dashi a gidan nan, ya rasa me take nema a duniyar nan? Me ta d'auki zaman aure? Ya take girmama al'amarin k'awayenta da fita? Wace irin uwa ce ita? Murza fuskarshi yayi sosai yana jan wani tsaki, fad'awa yayi kan gadon yana kallon sama amma idonshi rufe yana jin yanda kanshi ke sarawa. Da yamma ta samu ta shirya taje gidan matar nan ta nuna ita abokiyar aikin Aminu ce, ta samu had'in kanta sosai sai dai matar akwai sakin baki, hakan kuma ya samo asali ne saboda son da take dole mijinta ya saketa, daga yanayinta da d'abi'unta zaka san akwai dalili mai k'arfi da take son su rabu da gaggawa, amma tsaf ta gama karantarta har ta mata sallama ta tafi. daga nan asibitin tantali ta tsaya dan sanin wani abu a game da matar nan, ta kuma yi sa'ar samun k'awarta a bakin aikinta, cikin farin ciki suka gaisa inda k'awarta take fad'in "Faduma ana ganinki? Gaskiya matar nan kirkinki yayi yawa." Dariya tayi tace "A gafarce ni k'awata dan Allah, ke fa kinsan komai aiki shine matsalar, ke ma yanzu ba gashi akan aikin na same ki ba, nima yanzu haka wani aikin ne ya kawo ni wajenki." Cikin hararar wasa tace "Oho! Kenan da ban ganki ba idan ba aikin ya biyo ta kaina ba." Cikin murmushi tace "A'a ba haka nake nufi ba, amma na miki alk'awari insha Allahu zanje gidanki, yanzu fad'a min yaushe zan same ki gida." Hararanta ta sake yi tana gyara zamanta kan kujerarta ta nuna mata kujerar da suke fuskantar juna tace "Hum! Ni dai zauna kinji, yau na sanki ne Faduma?" Cikin dariya k'asa k'asa taja kujerar ta zauna tana d'ora jakarta akan teburin tace "Allah da gaske nake k'awata..." Da sauri ta dakata daga maganarta tana juyawa d'akin da taji ana ihu, kallon k'awarta tayi tace "Kuwar me nake ji?" Cikin jimami tace "Wallahi mai nak'uda a ciki, tun jiya muke ta fama har yanzu." Cikin tausayawa tace "Ayya baiwar Allah, Allah ya sauketa lafiya." Sake juyawa tayi inda taga mutane cirko cirko da gani kasan danginta ne, namijin ta kalla wanda taga damuwa sosai shinfid'e akan fuskarshi duk yayi wani iri. Lumshe ido kawai tayi saboda tausayin kanta da taji, lallai rayuwa wasu na samun gatan da sanda zasu haihu uwa da uba da miji da kuma dangi sukan kasancewa tare da kai, wasu kuma basa samun wanan damar. K'awarta ce tayi saurin cewa "Ina jinki Faduma zan tashi ne ga mai cikin nan." D'an zabura tayi ta dawo kanta tana fad'in "Ah yi hak'uri." Cikin nutsuwa ta mata bayanin yanayin data gani da kuma abinda ya d'aure mata kai duk ta tambayeta abinda take son sani, cikin k'warewa da sauri ta mata dalla dalla, kama daga abinda ke iya kawo hakan har yanda ake ganewa da sauransu, cikin jin dad'i ta d'auka a takarda ta saka a jakarta tana fad'in "Nagode k'awata, kije ga aikinki insha Allahu zan zo gidanki." Saida ta mik'e tace "Da gaske zaki zo?" Cike da tabbaci tace "Wallahi zan zo, ni na fad'a miki." D'aga mata hannu tayi ta nufi d'akin tana fad'in "Sai anjima to, ina jiranki." Ita ma tana had'a kayan ta fita, tunda ta fito kanta k'asa yake saboda maza ne a face asibitin dake zama anan, tana shiga motar ta tayar ta bar wurin cikin sauri, tana isa islamiyyar yayi daidai da fitowarsu, bud'awa yayi ya shiga yana fad'in "Ayya." Cikin kafeshi da ido tace "Na'am, ya kake? An gaji ko?" Saida ya mik'a mata takardar hannunshi ta karb'a yace "Na gaji Ayya." Ko da ta duba taga ta biyan kud'in wata ce, kashe motar tayi ta bud'a zata fita tana fad'in "Ina zuwa bari na biya na dawo." Cikin shagwab'a yace "Ayya ki bari har gobe mana, antashi fa yanzu." Saida ta rufo k'ofar tace "Amma ai malaman suna nan." Da kallo ya bita harta shiga cikin nutsuwa, ajiyar zuciya ya sauke, yanzu ne ya shiga shekararsa ta *takwas*, amma tunda ya bud'a ido ita yake gani tare dashi kullum, ita ce kullum ke d'awainiya dashi take hidima dashi, bai tab'a ganin mahaifinshi ba ko jin labarinshi daga bakin wani, bai san ya kammaninshi suke ba dan ko a hoto babu wanda ya nuna mishi, abunda ya sani kawai a game da mahaifinshi shine sunan *Tagur Sugui* sannan ya rasu tun kafin a haife shi. Cikin girmama juna ya mata izinin zama ta zauna suna sake gaisawa, hannu tasa jakarta ta fito da kud'i ta abe mishi gabanshi tana fad'in "Ga kud'in watan Amjad, ya bani takardar yanzu nace bari na biya tun yanzu kafin na manta kuma." Cikin jinjina al'amarin matar nan yana fad'in "Alhamdulillah, Allah ya saka da alkairi, Allah ya biyaki da aljanna." Wani babban littafi ya d'auka ya shiga dubawa a tsanake ya ga sunan Amjad d'in ya kuma mishi alama da an biya, rufewa yayi ya kalleta yace "Madame Amjad yaro ne mai hazak'a da k'ok'ari, ko da baki zo yanzu dama zamu nemeki a lambar wayarki, saboda munga shiru baki zo kan maganar ba kuma baki ce komai ba, sannan gashi lokaci ya matso sosai." Cikin fad'uwar gaba tace "Malam lafiya, me ya faru haka? Wani abu Amjad yayi?" Da mamaki yace "Kar dai kice bai fad'a miki sak'on dana bashi ba?" Da mamaki ita ma tace "A'a, wane sak'o?" Girgiza kai yayi yace "Subhanallahi, har takarda na bawa Amjad ya baki, kuma na fad'a masa baki da baki." Gaba d'aya ta bayar da hankalinta kanshi tace "Malam lafiya? Wani abu ne ya faru?" Girgiza mata kai yayi yace "Ba komai madame, akan gasar musabak'a ne da za'a gabatar dama, hazak'arshi da k'ok'arinshi ya cancanci ya wakilci yan ajinshi, ina tabbatar miki daga shekara bakwai zuwa goma zai iya zama zakara a ciki." Wani farin ciki ne ya bayyana a fuskarta tace "Masha Allah, naji dad'i sosai malam, Allah ya saka da alkairi, yanzu miye abunyi?" Girgiza kai yayi alamar ba komai tare da fad'in "Ba komai madame, kawai dai za'a ci gaba da k'arfafa masa gwiwa ne, sannan ya dinga samu isashen lokacin bita da kuma nutsuwa." Da sauri tace "Naji kace lokacin ya kusa? Yaushe ne? Ni bansan ya akayi bai fad'a min ba." Cikin kallon fuskarta yace "Rana irin ta yau ne fa." Cikin damuwa tace "Lokaci ya matso malam, kana ganin zai iya kuwa?" Murmushi yayi yace "Ni ma na yarda da Amjad bare ke mahaifiyarshi, kin fini saninshi ai, kuma tun sati biyu daya wuce a islamiyyar nan abinda muke ta karantar da masu gasar kenan, dan haka kar kiji komai madame, insha Allahu ba zai bamu kunya ba." Cike da gamsuwa tace "Mun gode sosai malam, Allah ya saka da alkairi." Jinjina kai yayi yace "Ba komai nagode nima." Mik'ewa tayi ta fita ya bi bayanta da kallo, yana jinjina ma k'ok'arinta sosai akan yaronta, shekara hud'u kenan daya santa kullum ita ke zaryar zuwa kawoshi da d'aukarshi, babban abun birgewa a game da ita shine yaronta bai tab'a jiranta na minti d'aya ba, duk da tana aiki sannan akwai yanayi na yau da kullum, amma kullum tana zuwa kan lokacinta, baka tab'a ganinshi yana jiranta ba. Sai dai abinda ya lura a game da ita babu maganar aure a gabanta, tunanin yanda zata kyautata rayuwar d'anta kawai take yi, hakan kuma baya masa dad'i shi kam duba da yanda Allah yayi ta babu tayawa, kyakyawa sosai ga tsarin hallita da zai birge kowane namiji mai ido, ga kuma tsafta da kama jiki, uwa uba kuma har yanzu yarinya ce tunda gaba d'aya shekarunta basu haura *ashirin da uku zuwa da hud'u* ba. Data same shi a mota ta kalleshi tace "Amjad me yasa baka fad'a min maganar musabak'arku ba?" Saida yayi k'asa da kanshi cikin ladabi yace "Kiyi hak'uri Ayya, sanda aka bani takardar ance kowa ya kira mahaifinsa ne, ni kuma sai aka ce na kira Ayyata." Lumshe ido tayi cikin k'unar zuciya kafin ta bud'e ta kalleshi, a hankali cikin taushin murya tace "Amjad kana jin kunyar nuna ni ne a matsayin uwarka? Ko kuma kana kallona ne a tauye shiyasa baka d'aukeni uwa da uba ba?" Girgiza kai yayi yace "Kiyi hak'uri Ayya, naga kowa cewa ake ya turo Abbansa." Cikin sakar masa ido tace "Shiyasa kake jin kunyar turo ni?" A hankali ya sake cewa "Kiyi hak'uri." Tayar da motar kawai tayi suka d'auki hanya bata sake ce mishi komai ba har suka isa gida ana ta sallah magriba. Bacci ya samu daga kwanciyar nan da yayi sai kiran sallah la'asar ne ya tashe shi, saida yayi wanka a gaggauce dan ya samu k'warin jiki kafin ya fita masallaci, yana idar da sallah kuma ya juyo ya dawo dan yunwa yake ji, bai ma fara tunkaren b'angarenshi ba dan yasan babu abinda zai samu na ci daya wuce bredi da sauran kayan da basa iya rik'e mutum na tsawon lokaci. Da sallama ya shiga falon da suka bari d'azu wajen tattaunawa, duk da kan kujera take amma da carbi a hannunta tana ja, k'arasawa yayi ya zauna nesa da ita yana fad'in "Barka da yamma Umma." Saida ta kai k'arshen istigfarin da take sannan ta kalleshi fuskarta d'auke da murmushi tace "Barka Hasheer, ka tashi kenan?" Saida ya d'an murza ido yace "Um Umma, bacci ne ya d'auke ni." Murmushi ta sake sakar masa tace "Ai tunda yan rigimar nan suka shiga suka ce bacci kake." Waigawa yayi ta d'akin Umma yana fad'in "Suna ina ne Umma? Sun dawo kenan?" Jinjina masa kai tayi tace "Ai yanzu suka tafi islamiyya tare da Salima, *Izzadeen* ne ma ya so yaje ya tasheka Salima tace ba zata jirasu ba." Jinjina kai kawai yayi yana shafa cikinshi, shiru ne ya biyo bayan zantawar, kamar babu wanda zai sake cewa komai sai kuma ta kalleshi a tsanake tace "Na zubo maka abinci ne?" Kallonta yayi cike da kunya da kuma rashin jin dad'i ya d'aga mata kai alamar eh, murmusawa tayi tare da girgiza kai ta mik'e tana fad'in "Allah kyauta." Madafa ta nufa tana cike da tausayin babban d'an nata, shekara da shekaru da aure amma har yanzu babu kwanciyar hankali, ba wai kwanciyar hankali na fad'a ba, A'a! Rashin samun kulawar mata, ita kullum a biki take da kuma waya da kallo, in anyi sa'a tana gidan bata fita ba to hankalinta na kan wayarta ko kuma tv tana kallon abinda take so, shiyasa har yanzu ya gagara yin gaba sai baya da yake yi. Abinci ta zubo masa ya zauna k'asa yasa hannu ya ci sosai ya k'oshi, hamdala yayi tare da godiya ga Umma kafin ya mik'e ya fita, saida ya kalli b'angaren nasu da tunanin ko ta dawo yanzu duba da tun lokacin data fita, amma yana yanda ya barshi sai kawai ya fice shima. _______________ Ta idar da sallah magriba tana zaune kan salayar wayarta tayi k'ara, zura hannu tayi ta d'auka tana duba mai kira, da sauri ta mik'e tsaye tana k'ok'arin cire hijabinta jikinta har rawa yake dan ta d'auki kiran, kiran mahaifiyarta ne da a shekara d'aya da k'yar take yin sa'ar samun ta kirata sau biyu ko sau uku, ita ta hanata ta kirata sai indai ita ce ta kirata, dan haka kullum cikin tsumayin ganin kiranta take. Tana d'auka tare da rangad'a sallama aka amsa mata a dak'ile, cikin bege da k'auna tace "Ayya ina wuni, kina lafiya? Ayya nayi ta jiran kiranki sai yanzu kawai kika kirani." Ba yabo ba fallasa daga b'angaren aka amsa mata da "Lafiya lau, yanzu ma na kiraki ne naji yaushe zaki zo bikin d'an uwan naki? Ko kin manta da bikin ne?" Da sauri ta dafe goshi dan har ga Allah yanayin aikinta yasa ta manta ma, a hankali cikin fargaba tace "Ayya bikin har ya kusa ne?" Da mamaki aka amsa mata da "Ban gane ba *Fati*, kina nufin har kin manta lokacin ne? Saboda baki damu da ja min magana ba ko." Da sauri tace "Yi hak'uri Ayya, wallahi n..." Shiru tayi sai kuma tace "Ayya dan Allah fad'a min yaushe ne saina taho?" Ajiyar zuciya taji ta sauke har taji sautin a kunnenta kafin tace "Alhamis ne insha Allah." Ita ma ajiyar zuciyar ta sauke tace "Shikenan Ayya zan zo insha Allahu, ina so na ganki da Abbah ma da sauran yan uwa." Ba wani karsashi a tare da ita tace "Ki zo, amma kar ku zo tare dashi." Tana fad'an haka tayi k'it ta kashe wayar, sororo tayi da wayar a hannu tana kallo, duk jikinta ne yayi sanyi ta zauna bakin gadonta, idonta taji sunyi taf da k'walla amma saita kawar dasu ta saki murmushi kawai ta mik'e ta fito falo. Har suka kwanta bacci ba ko Dada bata wa maganar ba bare Amjad, sai mai aikinta data shiga yi dan yanzu shine mai mahimmanci gerata da bata wasa dashi. ________________ Ana magriba ta shigo gidan a gajiye sosai, mayafin data cire da jakarta duk a saman kujerar data zauna ta diresu, d'an kwalinta ma haka ta aje shi tare da buda datar wayarta, hotunan bikin da suka d'auka ta shiga d'orawa a saman statu, sam tartsatsin girman kalmar Allahu Akbar da ake fad'a a masallacin dake jone a gidan bai fargar da ita ko ya shiga kunnuwanta ya buga a k'asa ba bare ta damu dashi, har akayi aka idar bata san anyi ba saida taji agogo ta alamta mata k'arfe 07:00 na yamma, da sauri ta kashe datar ta d'auki remonte ta kunna tashar da take so a daidai lokacin an fara wani s**** da take matuk'ar so mai sunan *Avenida brazil*, kallo ta shiga yi hankali kwance tana jin dad'in kallon sosai. Da gudu yaran suka shigo saboda ganin d'akin bud'e ya tabbatar mamansu na ciki kenan, suna shiga suka tunkareta da murnarsu amma basu kai gareta ba ta daka musu tsawa tana fad'in "Dallah ku min shiru, miye haka? Kun zo kenan zaku hana ni sakewa ko? Daga shigowarku sai tashin hankali? Mtssss." Gyara zama tayi ta nuna musu kujera tace "Maza ku zauna wurin nan, kar naga uban daya tashi, in ba haka ba ranku zai b'ace wallahi." Duk jikinsu ne yayi sanyi babu wanda yace k'ala, inda ta nuna musu Sharfudeen ya nufa zai zauna sai Izzadeen daya nufi hanyar fita, kallonshi tayi tace "Kai baka ji me nace ba kenan?" Juyowa yayi yana kumburo baki yace "Ni wajen Kaka zani." A tsawace tace "Wuce kayi ta tafiya, ai dama an gama hure muku kunne a kaina, je Allah raka taki gona." Tsaki ta kuma ja ta sake mayar da kallonta kan tv, tana cikin kallon wayarta tayi k'ara hakan yasa ta laluba ta d'auka ta d'ora a kunne ba tare data san waya kira ba, daga can b'angaren aka ce "Kin dawo ne?" Jin muryar yasa tasan waye, wani far tayi da ido tana yamutsa baki irin jin haushin nan tace "Na dawo mana, zanyi ta zama can ne?" Daga b'angarenshi yace "Me kika dafa mana?" Cikin jin haushi sosai tace "Wai kai Abban Sharfudeen baka da magana saita abinci ne? Daga kirana ba ko tambayata kina lafiya ko wani abu? Sai tambayar me na dafa kawai, to idan ban dafa ba kuma fa?" Cike da gatse yace "Saina tambayeki me zaki ci na siyo miki." Sakin fuskarta tayi daga d'aurewar data mata tana turo baki tace "Uhum! Komai ma ka siyo mana, wallahi na gaji ne ba dan haka ba dana mana girki." Rasa abin fad'a mata yasa shi kashe wayar kawai, wani haushi da takaici ne ya taso masa, kullum rok'on Allah yake ya k'ara masa hak'urin zama da ita, yana ta hak'uri ne saboda akwai zuri'a tsakaninsu, amma ita ta kasa fahimtar hakan. Shareta kawai yayi har yayi sallah isha'i a waje ya wuce majalisarsu, yana so ya koma gidan amma tunanin abinda zai tarar kawai ke hanashi, saida ya ga lokacin da yake da tabbacin yaranshi suna daf da yin bacci sannan ya d'auki hanyar komawa gidan da siyayyar daya musu. Yasan duk da taji shigowarshi tun daga bud'e gidan har fitowarshi a mota, dan gashi ma Sharfudeen ya tarbeshi da gudu tare da d'an uwan shi, tunda ta dawo har yanzu tana nan yanda take, hana rantsuwa ta shiga ban d'aki tayi fitsari ta dawo, tunda ya kai kallonshi kan teburin cin abinci ya d'auke sau d'aya baya fatan sake kallonshi, dan har yanzu kwanukan abincin safe ne a kai, kujerar kusa da ita ya zauna yana ta magana da yaran, ledar hannunshi ya mik'a musu yace "Ba wa mamanka." Karb'a yayi ya mik'a mata ta karb'a, ba tare data kalleshi ba ta mik'e ta je ta d'auko faranti ta juye, tana zuwa ta aje k'asa ta zauna tana kallon yaran tace musu "Ku zauna mu ci ba zan jira kowa ba dan yunwa nake ji." Suma yaran duk da basa jin yunwa dan sun ci abinci wajen Kakarsu, zaunawa sukayi suka saka hannu tare, saida ya gama mata kallon tsaf sannan ya saka hannu yana fad'in "Sannu." A take ta d'aga ido ta kalleshi tace "Uhum! Sannu." Bud'a ciki tayi sosai ta ci ta k'oshi yana kallonta yana ayyana albarkacin yaranshi ta ci, ba dan haka ba da bai siyo ba saidai ta kwana da yunwa, suna idawa ta d'auke faranti ta fitar waje, wanda ya zuba k'asa bata damu data share shi ba ko tattare wurin da kyau ta d'auki jakarta da mayafi ta nufi d'aki tana fad'in "Sharfudeen kuje d'akinku ku kwanta dare yayi." Da kallo duk suka bita har ta shige ciki, kallonsu yayi a tsanake cikin sanyin murya yace "Kunyi karatu ne?" D'aga kai sukayi sai Sharfudeen daya k'ara da cewa "Munyi tare da aunty Salima." Jinjina kai yayi ya mik'e ya nufi d'akinsu dasu, suna shiga yace "Kuje kuyi fitsari to." Ban d'aki suka shiga da d'aya d'aya suka fito ya canza musu kaya, saida ya musu addu'a sannan ya kwantar dasu ya rufe d'akin ya barsu. D'akinshi ya shiga ya cire kaya ya shiga wanka, ya jima yana tsaftace kanshi kafin ya fito ya shafa mai ya saka doguwar riga ya fesa turare ya tsefe sumar kanshi da ba wani yawa ne da ita ba ya fito ya nufi d'akinta, tunda ya sani ita dai ba zata zo ba, dama daka ganta d'akinshi musamman da dare to kud'i ko sutura ko fita take so. Yana shiga d'akin ya sameta zaune jingine a jikin gadon da waya a hannu da kayan bacci har ta kwanta, sai dai alamu sun nuna ba tayi wanka ba saboda kwalliyar fuskarta har yanzu na nan, cire doguwar rigar yayi ya aje ya kashe wuta, siririn tsaki tayi na jin haushi dan ita ma tunda ta ganshi d'akin tasan me zai faru, aje wayar tayi ta juya baya ta gyara kwanciyarta, tana gungunin "Yanzu yasha min kai, shi kullum baya gajiya da abu guda, haba ni na tsani jarabar nan wallahi." Karaf a cikin kunnenshi abinda ta fad'a, jim yayi kamar zai tashi daga abinda yayi niyya, sai kuma ya ga shi zai cutu dan sati uku kenan babu abinda ya shiga tsakaninsu na mu'amular aure, haka ya daure ya k'ara matsawa kusanta sosai ya kwanta bayanta, hannunshi ya d'ora kan cikin ya d'aga rigar yana shafawa yana sauke numfashi, d'an tsaki taja wanda har ya fito fili tana fad'in "Wai Abban Sharfudeen miye haka?" Saida ya taushe abinda ke taso mishi sosai yace mata "Uhum! Kamar me fa?" Cikin amon murya na rashin tausayi da ladabi tace "Bacci zanyi fa, dan Allah ka kwanta kai ma." Cikin sauke mata wani zazzafan numfashi a fuska yace "Um um! Ba zan iya ba Saudat, ina buk'atarki sosai, kinsan nayi hak'uri ko." Wani tsakin ta kuma yi cikin haushi wanda yasa shi d'aga kanshi ya kalli fuskarta duk da duhu ke akwai, cikin muryar gargad'i yace "Saudat ki daina min tsakin nan, kinsan bana so ko? Bana so ki kaini mak'ura fa, gwara ki zage ki ko ki mareni da ki zauna kina min tsakin nan." A ganinta k'ofa ce da zata sake hassala shi ya bar mata d'akin, sai kawai ta zabura ta mik'e zaune tana fad'in "To in hakane ka koma d'akinka mana ka k'yale ni, ai nima kasan bana son takura." Gyara zamanshi yayi ya zuba mata manyan idonshi masu yalwar gashi yace "Saudat bana son fad'awa halaka, bana son aikata abinda bai dace dani ba, me yasa ba kya tunanin haka?" Kawar da kai tayi irin ko a jikinta ma ba tace komai ba, kallonta ya sake yi yace "Ba zaki ji tausayi na ba kenan?" Kallonshi tayi tana turo baki tace "Kayi hak'uri na yau kawai har gobe, kaga idan ban kwanta da wuri ba ina makara wajen shirya yara." Sauka yayi daga kan gadon yana girgiza kai ya d'auki doguwar rigarshi ya rik'e a hannu ya fita daga d'akin, da harara ta bishi saida ya fita kuma sai taji har ya bata tausayi, da sauri ta lalubo wayarta da ko datar bata kashe ba ta ci gaba da duba sak'onni, tana son Hasheer sosai tana kuma kishinsa, tana jin dad'in zama dashi da kuma son ta ci gaba da zama dashi d'in, kawai dai tana kama jikinta ne saboda karta lalace ta zama baiwar miji, shiyasa ba a cikin shekarunsu *tara* da aure har yanzu take da yaya biyu, magani take sha ba k'akk'autawa shiyasa da Sharfudeen ya shekara *shida* saida Hasheer yayi da gaske kafin ta daina sha har Allah ya bata cikin Izzadeen, yanzu shima zata mishi k'ane bayan ya shekara shida ko bakwai saita tsaya, dan yara uku take da burin haifa a duniya. _______________ *Litini* Da safe ta fito cikin shirinta tsaf na shiga kotu dan gabatar da shari'arta, tayi kyau sosai cikin farar lafaya da bak'ak'en takalmi k'afa ciki masu d'an tudu, Amjad ma ya gama shirinsa tsaf suka karya kafin suka fita Owwo na binsu da addu'a, tana aje shi makaranta kamar yanda suka saba ta gargad'eshi kan maida hankali akan karatunshi da kuma fad'a, mik'a masa abincinshi tayi wanda yake tafiya dashi kafin taga shigarshi ta wuce ita ma. Aminu ne ya kiranta bayan sun gaisa yake fad'in
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD