CHAFTER 5

4708 Words
Cikin hukuncin Allah kam ta samu nasara a kan shari'ar, ta bayyanar da hujojjin da dole aka d'aure mijin daya kashe matarshi saboda tayi fada da budurwarshi, duk da ba yayi ne da niyyar kisa ba amma dai ganganci ne yayi k'arara. Da farin ciki suka fito a kotun dangin margayiyar da wasu daga cikin mutanen garin suna ta tayata murna da jinjina k'ok'arinta, musamman yanda ta fad'i hatta da salon kwanciyar mamaciyar a sanda ya tureta ta fad'i, shi mijin yayi k'aryar ita ta fad'i da kanta, amma sai Faduma ta nuna wa kotu da ita ta fad'i da kanta zai zama tsakaninta da k'ofa akwai tazarar zira'i d'aya da da 3cm, amma dayake tureta ne akayi da k'arfi shiyasa har ta kai 4cm, hakan ya birge gar alk'alin kanshi ya kuma jinjina mata. Tana daf da zuwa ta shiga motarta taji muryar mace a bayanta tace "Ina tayaki murna, amma kiyi hankali ki kuma yi taka tsantsan." Juyowa tayi ta kalleta, dakatawa tayi da bud'e motar ta kalleta da kyau, ba yarinya bace kamarta dan zata iya kaiwa shekara talatin da d'oriya, cikin halin ko in kula tace "Nagode, sai dai kuma ban sanki ba." Matsowa matar tayi tana murmushi tace "Ina fa zaki sanni tunda kullum illa kike min, Faduma wai me na tare miki ne a duniyar nan." Wani wurga ido tayi tana murmushin rainin hankali tace "Na miki wani abu ne?" Jinjina kai tayi tace "Sosai ma, kin min abubuwa da dama, kuma ki sani daf nake da kasa hak'uri wallahi, dan banga dalilin da zaki dinga shigowa rayuwata ba haka kawai." D'aga maya hannu tayi ta dakatar da ita da fad'in "Dallah dakata malama, wacece ke? Me nayi miki kuma?" Rumgume hannaye tayi tana mata wani shu'umin kallo tace "Zaki sani nan gaba, kawai dama dan na fad'a miki ki kula ne." Juyawa tayi zata bar wurin sai kuma ta tsaya tace "Uhum yawwa, karki manta da sunana daga yau, *Zaleeha*." Wani murmushi Faduma tayi ta gyara tsayuwarta ta nuna ta da makullin mota tace "Kinsan da maganar nan zata iya d'aureki? Kuma kinsan da zan iya gabatar da maganar nan taki gaban kotu a matsayin hujja? Ke ma ki kula da kanki." Mirmushin ta kuma saki tace "Karki damu dani, ai kin gama ruguza min komai ta yanda ban damu da duk abinda zai same ni ba yanzu, ganin bayanki shine kawai burina a yanzu." Ita ma rumgume hannaye tayi tana jinjina kai da fad'in "Kafin na shiga karatun lauya saida na fara neman ilimin addini, kuma a cikin addini na akwai garkuwa da runfuna da dama da irinmu ke fakewa a ciki domin nisanta daga kaidin ire-irenku, ki sani babu abinda sharrinki zai min, dan nayi gwagwarmaya da wanda suka fiki sharri kuma sai ido suka zuba min, dan haka ina baki shawara ki shafa wa kanki lafiya da shiga sabgata, inba haka ba abun zai miki yawa, dan a k'arshe wasan za'a tashi baki ga tsuntsu kuma kin rasa tarkon, idan kuma akayi rashin sa'a kika kaini bango matuk'a, to fa shakka babu *ALLURA ZA TA TONO GALMA*." Da makullin ta sake nunata ta juya ta shiga motarta bata sake bi ta kanta ba ta wuce, saida ta ga fitarta kad'ai ta sauke ajiyar zuciya, girgiza kai tayi a fili ta furta "Wallahi Faduma ba zan k'yaleki ba, ki d'aure min uwata, sannan a dalilinki aka karb'e kasuwancinta aka mata biyan bashi, sannan kinsa an rufe wanda muke daf da shirin yin aure, kuma kike so na barki? Ai k'arya ne wallahi!" Tana gama fad'a ta wuce. Kotun da Aminu ke shari'a ta wuce inda zuwanta yayi daidai da suma suna fitowa, fitowa tayi ta jingina jikin motar tana hangenshi yana nufota baki bud'e, yana zuwa duk suka saki murmushi da sauri yace "Kin cinye ko?" Murmushi tayi sosai ta d'aga masa kai alamar eh, cike da jin dad'i da karsashi yace "Dan haka sai ki fad'a min abinda kikayi alk'awari." Girgiza kai tayi tana murmushi mai birgewa tace "A'a fa ba haka mukayi ba, kai zaka fara fad'a min." Shima girgiza kai yayi yace "A'a ban yarda ba, kawai ke ki fara fad'a." Hararan wasa ta wurga mishi tace "To! To shikenan zan fad'a yanzu." Saida ta kalleshi sosai ta shanye murmushin fuskarta sannan tace "Nagode Aminu, nagode da duk taimakon da kake min, Allah ya biyaka." A take shima duk wannan karsashin da farin cikin suka b'ace, a sanyaye yace "Wai dama abinda zaki fad'a kenan?" D'aga mishi kai tayi alamar eh sannan tace "Sai kuma..." Da sauri yana sake matsawa kusanta yace "Uhum ina ji? Fad'i mana." Ajiyar zuciya ta sauke tana hangen k'ofar shigowa tace "Jiya munyi waya da Ayya, nan da kwana biyu bikin yaya *Barka*, dole zan tafi jibi insha Allah." Ajiyar zuciya ya sake saukewa yaja baya yana dafe k'ugu yana gyara zaman ordi. d'inshi, kallonta yayi a kasalance yace "Faduma bana so ki tafi." Kallonshi tayi amma sai taji kunya saboda kallon da yake mata ta sunkuyar da kai murya k'asa k'asa tace "Kayi hak'uri mana, ai ba jimawa zanyi ba, da zaran an idar zuwa lahadi zan dawo." D'an d'aga kai yayi alamar shikenan tare da fad'in "Tare zaku tafi da Amjad?" Girgoza kai tayi ta kalleshi tace "Ayya tace naje ni kad'ai, kai dai kasan komai." Cike da tausayawa ya kalleta yace "Kiyi hak'uri Faduma, insha Allahu komai zai wuce ya zama tarihi kamar ba ayi ba." Ba tare data kalleshi ba tayi wani murmushi mai kama da kuka na son tahowa tace "Kune k'arfin gwiwata Aminu, ku kuka samar da wannan Faduman, ba dan kai da Dada ba da yanzu bansan wace irin rayuwa nake yi ba." Kallonshi tayi cikin ido tace "Ina godiya ssoai gareka Aminu, bansan da me zan iya saka maka ba? Amma ina fatan ranar da zata zo ka nemi taimako na nima, da gaggawa cikin farin ciki zanyi maka." Girgiza kai yayi yana murmushi ya kalleta yace "Muje to, ke kullum ba kya rabuwa da tuna baya." Ajiyar zuciya ta sauke tana bud'a mota tace "Rayuwa tana koya maka hankali ne idan kana tuna baya." Motarshi ya bud'a shima ya kalleta yace "Zan zo anjima na ga yarona Amjad." Da sauri ta kalleshi ido cikin ido, *yaronshi*? Bata san me yasa gabanta ya fad'i ba daya ambaci Amjad da d'anshi, bata san me yasa ya danganta kanshi da Amjad ba yau? Jikinta ne yayi sanyi saida ya k'yasta mata hannu yace "Ya dai? Ko nayi kuskure?" Da sauri ta kalleshi ta girgiza kai, murmushi ta k'ak'aro tace "Sai ka zo." Bud'a motar tayi ta shiga gabanta na ci gaba da fad'uwa, motarshi na gaba tana baya har suka fita daga wurin, makaranta ta wuce saida tayi jiran kusan minti sha biyar kafin aka sallamesu suka fito, tana hangenshi shi da wasu yara biyu har suka k'araso, gaisheta sukayi ta amsa da sakin fuska, Amjad ma gaisheta yayi da tambayarta "Ayya ya shari'a? Kinyi nasara ko?" Murmushi tayi sosai tana fad'in "Muje saina baka labarin yanda mukayi." Da sauri yace "Ayya ko zaki sauke abokina gidansu?" Kallon yaran tayi kyawawa dasu ga kuma kama ta kalleshi tace "Ba'a zuwa d'aukarsu ne?" Cikin nutsuwa ya shiga mata bayani "Suna da mai adaidaita Ayya tun suna kan hanyar tahowa adaidaitar ta samu matsala sai cikin wata adaidaita ya kawosu ta wani, kuma yanzu na so mu karb'i wayar mai gadi su kira Abbansu ko Ayyasu amma sun ce basu san lambar ba, kuma ina tsoron abarsu anan shiyasa." Wani murmushi tayi ta kalli yaran tace "Ina ne gidanku?" Sharfudeen ne yace "Zarya kusan commissariat sabuwa." Jinjina kai tayi tace "To ku shiga muje." Bud'ewa sukayi da sauri suka shiga baya Amjad kuma a gaba, suna tafe tana bashi labarin wasu daga cikin abubuwan da kanshi ke iya d'auka dangane da shari'ar nan, a hanyarsu taga mai siyar da karas ta tsaya ta siya, bawa kowa tayi ta kalli Amjad tana dariya tace "Na fiku buk'atar wannan saboda ni na fara tsufa, ido sun fara bani matsala." Girgiza kai Amjad ya shiga yi yana dariya yana fad'in "A'a A'a Ayya, ni Ayyata sabuwa ce har yanzu, babu abinda zakiyi Ayya." Dariya tayi suka ci gaba da tafiya hankali kwance har saida su Sharfu suka nuna mata k'ofar gidan, tsayawa tayi tana kallon gidan, lallai inhar kana son jin dad'in rayuwa zakayi fatan ace wannan gida mallakinka ne, babba ne wanda kalar da aka mishi ma mai d'aukar hankali ce da birgewa, kalar ba ko ina zaka ganta ba, dan kalar maron ce mai duhu da mai haske sai d'an ratsin fari kad'an, rufe motar sukayi har zasu wuce suna daga musu hannu tace "A'a ban gane ba." Juyowa sukayi hakan yasa ta mik'a musu hannu tana fad'in "Mu gaisa mana." Dukansu hannu suka bata cike da jin kunya, rik'e hannayen tayi tace "Ban ji wanda yace ya gode? Nasan dai ba zaku ce Amminku ko Abbanku bai koya muku yin godiya idan an muku abu komai k'ank'antar shi ba." Izzadeen da yafi surutu ne yace "Mu Mamanmu kullum bata koya mana." Sharfudeen ne yace "Mun gode Aunty." Murmushi ta musu tace "Ku gaida kowa da kowa." Har zasu wuce tace "Baku fad'a min sunanku ba? Ko ba zakuyi k'awance dani ba?" Dariya sukayi dukansu suka fad'a mata sunan, wani murmushin ta sake yi tace "Sunayenku da dad'i, Allah ya muku albarka." Juyawa sukayi suka wuce kafin ita kuma ta tayar suka shiga kwana dan komawa baya su tafi gida suma. Bayan isha'i sun gama cin abinci suna hira take fad'awa Dada tafiyarta, tambayar Dada tayi "Amma zamu je dake ko Dada?" Tab'e baki tayi tace "Ni Faduma? A'a wallahi kije ko, ni ina nan babu abinda zanje na musu." Murmushi kawai tayi dan tasan dama ba zata je d'in ba, tambayarta tayi ita ma da cewa "Amma da Amjad zaku tafi ko?" Girgiza kai tayi tace "Dada tace na je ni kad'ai, dole zan barshi nan." Girgiza kai tayi cikin rashin jin dad'i tace "Amma dai wallahi *Hadizey* na da matsala, saboda kawai farin cikin wasu sai ki dinga tauye kanki." Tsaki tayi na jin haushi k'ala dai Faduma ba tace ba, har suka gama hirarsu kowa ya shiga d'akinshi ya kwanta. _______________ Duk da ya fita da b'acin ranta amma sanda ya dawo gidan ganin yaran na tare da ita yasa shi kallonta yace "Sannu da gida." Saida ta harareshi ta wutsiyar ido yace "Yawwa." Baiyi zaune ba dan yaga hankalinta na kan kallo ya wuce kawai, duk yaran bin bayanshi sukayi zuwa d'akinshi, inda Izzadeen ke fad'in "Abba yau aunty ta kawo mu gida, tana da kirki sosai da dariya, kuma kaga mai kyau da k'amshi." Juyowa yayi da mamaki ya kalleshi yace "Kai Izzadeen, gidan uban wa kake jin wannan kalaman? Kenan k'are mata kallo kayi?" Turo baki yayi ya kama hannunshi yana k'amk'amewa yace "Ai da gaske ne ko Deen? Ko da muka shiga motarta muka ji k'amshi, kuma duk in zatayi magana sai tayi murmushi." Sharfudeen ne yace "Kuma Abba har addu'a ta mana, kaga ai Mammie bata mana addu'a." Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai yace "To wai wacece?" Izzadeen ne yayi saurin cewa "Mamar abokina ce." Hararanshi Sharfudeen yayi yace "K'arya ce Abba abokina ne fa, ya girmeka ai." Shima turo baki yayi yace "K'arya ce abokina ne." Ganin.zasu fara fad'a yace "To naji shikenan, in ce dai kun mata godiya ko?" "Eh Abba." Suka fad'a kusan a tare, cire rigarshi yayi yana fad'in "To ku zauna zan je nayi wanka sai na zo mu ci abinci." Sharfudeen ne yace "Abba ai Mammie bata yi girki ba." Juyowa yayi ya kalleshi sai Izzadeen da yayi saurin cewa "K'arya ce Abba ta gyara mana salade mun ci." Hararanshi Sharfudeen yayi yace "To Abba salade abinci ne, tunda yamma muka ci fa, kuma har cewa nayi muna jin yaunwa tace muje wajen Kaka mu ci." Girgiza kai kawai yayi cike da takaici ya shige ban d'akin, ya jima yana tsaftace kanshi kafin ya fito ya shirya suka fita shi da yaren suna ci gaba da surutunsu, turarenshi ya fara sanar da ita ya fito, amma ita a dole hushi take dashi sai kawai ta k'i kallon inda suke, shima bai kulata ba ya fita tare da yaren suka nufi b'angaren mahaifiyarshi. Da sallama suka shiga dukansu, amsawa Umma tayi tana kallonsu tace "Da yaran nan ka dawo min? Wai ku bana sallameku ba nace sai gobe kuma." Izzadeen ne yace "To ai tare da Abbanmu muka zo." Hararanshi tayi tace "Nasan dai yunwa ta koroka ko?" Sharfudeen ne yace "Eh, idan kika bamu tuwo muka ci sai mu koma wajenmu." "Idan na k'i fa?" Ta fad'a tana kallonshi, Hasheer dai dariya yake yi sai Salima da tayi saurin cewa "Ka ba Umma hak'uri in dai kana son cin tuwo yaro." Wuri suka samu suka zauna cikin ladabi yace "Umma an wuni lafiya?" Da murmushi ta amsa da "Lafiya lau Hasheer, har an dawo?" "Umma na dawo, ya gida?" Amsawa tayi da "Gida lafiya lau." Kallon Salima tayi tace "Je ki d'auko mishi abinci, ko kun ci abinci ne?" Ta k'arashe da kallonshi, girgiza mata kai yayi alamar a'a, tashi Salima tayi take ta d'auko ta kawo musu, zuba musu tayi shi da yaran suka saka hannu, suna cikin cin abinci Mujaheed ya shigo babu sallama da sigari a hannunshi, Salima ya kalli cike da gadara yace "D'auko min abinci na." Mik'ewa tayi tana hararenshi ta wutsiyar ido ta shige, cikin dakakkiyar muryar da babu alamar wasa Hasheer ya kalleshi yace "Karka sake shigowa gidan nan da sigari, iyakar shanka da ita daga k'ofar gida abinda yayi wajen gidan, amma banda cikin gida saboda akwai yara da yanzu ne ake tarbiyarsu, sannan ya zama na k'arshe da zaka sake shigo mana cikin gida babu sallama." Yana gama fad'a ya sunkuyar da kanshi ya ci gaba da cin abincin, cikin sababi da bala'i da d'aga murya yace "Kai! Kai ubana ne da zaka zauna ka tank'washe k'afafu kana kafa min sharud'a, to ba za ayi ko d'ayan ba kayi abinda zakayi, kaga bana shiga harkar kowa a gidan nan ya kamata nima a fita harkata." Kallon Umma yayi cikin raini yana nunata da hannu yace "Kinga ki wa d'anki magana, wallahi saina kakkaryashi babu abinda ya dame ni, akan me zai zauna yana fad'a min haka sai kace ya haife ni, ko dan anga uwata bata gidan ne?" Cikin sanyi ta kalleshi tace "Kayi hak'uri Mujaheed ba zai sake ba." Kallon Hasherr tayi tace "Hasheer babu ruwanka da lamarinshi, nan gidansu ne yana da damar da zai shigo duk yanda yaga dama, tunda baya shiga b'angarenka to kayi zamanka can." D'ago kai yayi ya kalleta da mamaki yace "Amma Umma ba dan ni na fad'i haka, saboda yara ne wanda suka fi sauran d'aukan abu mai kyau da marar kyau." Ba alamar wasa tace "To suma su zauna wajensu mana, kaga basu zo ba bare su gani." Wani murmushin takaici yayi dan yasan tana fad'in hakane saboda maslaha kawai, amma kuma wanda take yi dominshi ba zai gani ba, ai kuwa sautin tsaki suka ji yana fad'in "Aikin banza, wannan duk salon munafurci ne, ni fa ba yau na fara rayuwa dake ba, sai dai ki ma wani wannan makircinki kuma ba dai ni ba." Wani kallo ya masa yace "Mujaheed! Mujaheed! Na rok'eka duk sanda zaka ci zarafin mahaifiyata ka dinga yi bayan idona, kai kasan albarkacinta kullum kake ci, ka daina wani abun mana tunda ba mahaukaci bane kai." A tsawace Umma tace "Hasheer, kayi abinda ya kawoka mana ka koma wajenka." Saida ya had'e abinda ya tokera masa wuya ya cire hannunshi ya mik'e ya fita, suma yaran mik'ewa sukayi suka bi bayanshi, Salima na zuwa ta mik'a mishi ya karb'a yana bud'e kwanon, gaban Umma yaje ya nuna mata yana fad'in "Dubi wannan yar iskar abincin data zuba min, yanzu ko waccen Sharfudeen d'in mai k'aton kai ba sai ya cinye shi ba." Karb'ar kwanon tayi ta mik'e tana fad'in "Bari na zubo maka da kaina." Da kanta ta sake zubo mishi wanfa tasan dole ya ci ya barshi, kawo mishi tayi yana karb'a ya juya ya fice yana magana k'asa k'asa, girgiza kai tayi tace "Zanyi hak'uri kamar yanda ubanka har ya rasu yana fad'a min, uwarka ma haka yayi hak'uri da ita bare kuma ni." Ko da suka shiga kallo d'aya ta masa tasan ranshi a b'ace yake, amma tana kallo suka shiga d'akinshi, bata damu ta ji me ya faru ba bare tasan hanyar da zata bi wajen ganin dariya ko murmushinshi, ita kam matsalarta ma abinci da bata girka ba kuma taga bai shigo da komai ba, dole da taji yunwa ta mik'e taje ta d'ora indomie, tana idawa ta fito da plate shi kuma ya fito d'auke da Izzadeen har sunyi bacci, kallon juna sukayi lokaci d'aya kowa ya d'auke kanshi, d'akinsu ya kwantar dasu ya koma ya kwanta shima. ________________ Kamar kullum ta aje shi a makaranta ta wuce ofishinsu, ta samu Aminu ya rigata isa har tana tsokanarshi dan baya da mata ne yayi sammako haka, dariya ya mata yace "Wacce nake so ce bata so na." Dariya tayi cike da son kawar da zancen tace "Haka dai ka ce." "Hakane mana." Ya fad'a yana kallonta shima, saida ta wuce nata ofishin kamar yanda take kullum ta cire lafayarta ta d'ora rigar aikinta ta zauna. Misalin 09:30 rana tayi sosai Aminu ya shigo da sallama, kai tsaye ya shiga ya tsaya gaban teburin ya d'ora hannayenshi hakan yasa shi d'an rank'wafawa yace "Kina da bak'o fa." Kallonshi tayi tace "Bak'o kuma? Waye?" Ba tare daya d'auke ido daga kanta ba yace "Um ban sanshi ba gaskiya, ya zo d'aukar lauya ne." Wani kallo ta masa mai kama da harare tace "Shine kuma zaka ce bak'o na? Kawai kaji dashi mana, ina da abubuwa dayawa kuma kaga jibi zanyi tafiya." Karkace kai yayi cikin rarrashi yace "Dan Allah mana ki saurare shi, ni ya fara samu ya fad'a min komai, sai nace mishi zan had'ashi da oganniyata, dan matsalar babba ce." Harara ta sake banka masa tace "Aminu bana so fa, yana ina yanzu?" Da ido ya nuna mata yace "Yana waje." Gyara zamanta tayi tace "Shikenan shigo dashi." Murmushi yayi yace "Yawwa ko ke fa." Girgiza kai tayi har zata maida dubanta ga ordi. ya sake tsayawa yace "Ehem! In tambayeki mana?" Da ido ta masa nuni da ina jinki, cike da zolaya yace "Meye sunan masoyiya da harshen tubanci?" Dariya tayi har kumatunta suka lob'a tana girgiza kai, kallonta yayi cike da birgewa yana murmushi yace "Ina jinki mana." Ba tare data kalleshi ba tace "Yau yan mata zasu shiga uku kenan, to sunan masoyiya da tubanci *dara nra*." Wani tattausan murmushi ya saki da sosai take birgeshi duk abinda tayi, musamman tana harshen tubanci saita k'ara kyau, fita yayi ita ma ta ci gaba da murmusawa, ba jimawa taji an k'wank'wasa k'ofar, cikin taushin murya k'asa k'asa yanda ba zakayi tunanin ko na kusa da ita yaji ba tace "Shigo." Bud'ewa akayi amma bata d'aga kanta ba tana ta danna ordi., taji an rufe k'ofar kuma anyi taku biyu zuwa uku, amma kuma sai taji an tsaya ba'a ci gaba da tahowa ba, hakan yasa ta d'aga kai da niyyar cewa a k'araso mana. Sanda sukayi ido biyu wani mummunan fad'uwa ne gabanta yayi, k'arfin harbawar da zuciyarta tayi yasa ta saurin dafe k'irjinta ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Bata iya rufe bakin ba dan gaba d'aya jikinta ne taji ya kwashi rawa, ba dan a zaune take ba shakka babu fad'uwa zatayi, tuni idonta suka canza lauyi suka yi sirkin ja tare da taruwar ruwa taf idonta, tana ta k'ok'arin janye idonta ta rufe bakinta, tana so tayi dauriya ta b'oye halin data shiga ciki, amma abun ya gagara ta tsareshi da idonta, zufar data gangaro daga goshinta ta sauka d'as saman gashin idonta ne ya tilasta mata rufe idon hakan kuma yasa hawayen zirarowa suka bi tattausan kumatunta, a lokacin kuma tayi nasarar rufe bakinta ta sauke wani irin numfashi mai k'arfin gaske da sauti, hannunta dake rawa ta d'auke daga k'irjinta tasa ta goge hawayen. Gyara zamanta tayi tare da daidaita nutsuwarta ta d'aga kanta, bata yarda ta sake kallon fuskarshi ba ta bud'a baki zatayi magana, kif taji ta nemi muryarta da harshenta ta rasa, da ta bud'a bakin sai taji kamar bata iya magana ba ko kuma bata san da wane yare zata yi magana ba. Da sauri ta tashi har kujerar ta tintsire ta fad'i da sauri har tana hard'ewa ta shige yar k'aramar ban d'akin dake cikin ofishin ta rufe k'ofar, jingina tayi a k'ofar ta fashe da kuka marar sauti, danne muryarta tayi ta d'aga kai sama tana kuka sosai har tayi zaune k'asa ta manta a ban d'aki take, rintse ido tayi sosai tana fad'in "Me yasa na ganshi? Me ya dawo dashi rayuwata kuma? Me ya dawo nema a guri na? Me ya kawoshi garin da nake?" Ci gaba tayi da kukan kamar ranta zai fita wanda ta jima ba tayi ba na hawaye sai na zuciya kawai, kamar an tsikareta kuma saita mik'e tana share hawayen, gaban madubin ta k'arasa ta wanke fuskarta ta d'aga kai ta kalli kanta, girgiza kai tayi tace "Me yasa zakiyi kuka? Me yasa zaki kasa fuskantarshi? Kin manta dashi fa, rayuwarki kawai kike yi, ya lalata miki ita a shekarun baya, karki bari ya sake lalata miki ita a yanzu ma, karki bari ya sake ruguza miki buri mana." Jinjina kai tayi alamar gamsuwa da shawarar da zuciyarta ta bata, goge fuskarta tayi ta gyara kanta sosai sannan ta fito. Tunda ya shigo ya sauke ido a kanta yaji idonshi na mishi gizon ita ce ko ba ita bace? Dan tabbatarwa ya rufe k'ofar ya taka d'aya biyu har uku, yana tabbatarwa ita ce ya tsaya cak, a lokacin kam dan kwananshi basu k'are bare, amma a yanda zuciyarshi ta buga kanshi ya sara daya rasa ranshi, kakkarwar da yaji hannayenshi na yi da k'afafunshi ne yasa shi jimk'e hannayen da k'arfin tsiya, ya so sunkuyar da nashi kan ko dan kunya, amma sai hakan ya zama jan aiki, haka kawai shima ya kafeta da nashi idanun yana kallo, dantse hak'oranshi yayi sosai har saida jijiyoyin hannunshi da goshi duk suka fito, sai k'ullutun mak'ogwaronshi dake ta kai kawo alamar yana ta had'a yawu da k'arfi. Tashin da tayi da sauri ne ya ceceshi wajen sanin lallai yana motsi, dan tana shigewa ta rufo k'ofar shi kuma ya rufe ido, a hankali ya sake bud'esu akan k'ofar, harbawar da kanshi ke yi da rawar da har yanzu k'afafunshi keyi yasa dole ya k'arasa da k'yar ya zauna kan d'aya daga cikin kujeru biyun dake fuskantar wacce ta tashi, duk'e kai yayi ya d'ora akan hannunshi daya d'ora kan teburin, d'aya hannun kuma ya dafe saitin zuciyarshi da yake jin kamar zata fasa ta fito waje. Yana hakane yaji bud'e k'ofar alamar zata fito, da sauri ya d'aga kanshi yana kallon k'ofar, sam bata yarda sun sake had'a ido ba kanta na kan kujerar, sunkuyawa tayi ta d'auke kujerar ta zaunar da ita, saida ta gyara rigarta ta zauna kan kujerar tana janye ordi. d'in ta janyo wani babban littafi, alk'alami ta d'auka ta rik'e ba tare data kalli fuskarshi ba tace "Sannu ko." Wani zazzafan iska ya furzar da k'arfi yana d'auke idonshi daga kanta, wata ajiyar zuciya ya sauke sannan ya sake kallonta yana mai tattaro duka nutsuwarshi da k'arfinshi, da k'yar kamar mai koyon magana ya furta "Sa...nnu." Kallon wuyan rigarshi tayi jin yanda ya amsa da wuya, d'auke idonta tayi daga nan tace "Sunanka?" Kallon mamaki ya mata jin wai Faduma ce zata tambayi sunan shi a duniyar nan? Lallai ma ya fad'a yana jinjina kai, jingina yayi kan kujerar ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kallonta da isa yace "Sunana *Tagur Sugui*." Ba tare data kalleshi ba dai tace "Shekaranka nawa malam Tagur?" Wani murmushin mamakin rainin hankalinta yayi dan yasan da gangan take haka ba abinda ya kamata ta fara tambayarshi kenan ba, amma saiya dake yace "Ina jin yanzu ne zan cika talatin." Karo na biyu da suka sake kallon juna ido cikin ido, kallon bansan iskanci ta masa, gyara zamanta ta sake yi ba tare data daina kallonshi ba tace "Gaskiya zaka fad'a min." Shima amsa mata yayi da "Ba komai to ina jiranki, fatan nasara." Kai tsaye ta amsa mishi da "Kai ma ina maka fatan samun nasara, sai anjima." Tana fad'a ta datse kiran, k'aramin ofishinsu ta fara wucewa ita da Aminu wanda sukayi had'in gwiwa, tana fita a mota ta d'auki ordi. d'inta da jakarta ta rataya ta nufi ciki, makulli tasa ta bud'e k'ofar kafin ta shiga ciki, ba wani walallen ofishi bane amma dai a tsaftace yake sai k'amshin turaren jikin Faduma daya zamar mata jiki har ya mannewa ofishin shima kamar yanda yake a motarta d'akinta da duk wani abu da tayi anfani dashi. Rataya jakar hannunta tayi akan wani d'an k'arfe tare da cire lafayarta ita ma ta ratayata akai, hakan ya bayyanar da rigarta iya gwiwa mai tsaga biyu da wandonta da kuma d'an kwalin dake d'aure a kanta sosai, wani coffre ta jawo dake gaban table d'in ta d'auki rigarta ta lauyoyi bak'a da hularta, warwareta tayi daga ninken sai k'amshin turare take kamar na wuta ta saka, cire kallabin tayi ta d'ora hular ta tsaya akan daidai k'ullin gashinta da tayi, duk tsawonshi haka ta laulayeshi ta had'eshi da ribom d'inta, tana kallon madubi ita kanta saida tayi murmushi dan tasan kayan na mata kyau ba kad'an ba. Jawo kujerar tayi tasa wani hanck. ta goge sannan ta zauna, bud'a ordi. d'in tayi tare da d'aukar wasu takardu ta shiga dubawa a tsanake tana tattara komai tana kuma nazartar wasu abubuwa, inda tana yi tana kallon agogon dake saman k'ofar shigowa dan kar lokaci ya wuce mata bata ankara ba. Tana haka har k'arfe 09:30 tayi, had'a kayan tayi duka wasu tasa a jaka wasu kuma a sa a jakar ordi. d'in sannan ta rik'e a hannu ta fito, saida ta kulle sannan ta nufi mota, saida ta juya ta kalli gungun wasu maza da suke gaishe ta ita ma ta gaishesu cikin girmamawa sannan ta shige ta bar wurin. ________________ Duk yanda ya so yayi banza da lamarinta abun ya gagareshi, da k'yar ya samu ya kai daren nan har ya wayi gari yau safiya, tsabar ciwon cikin daya kwana dashi ko sallah asuba bai samu yayi ba, yanzu ma jin kamar zai mutu tsabar wahala ne yasa shi tasowa yana layi da duk'u duk'u ya kawo kanshi d'akinta, baccinta take ta shara babu alamar tayi sallah, bai jira komai ba wajen haye gadon yaja zanin rufar ya shiga ciki, kamar a mafarki taji an birkita ta tare da janye rigarta sama aka bud'e k'afafunta. Duk yanda ta so janye kanta daga gareshi kasawa tayi, kokawa ta dinga yi dan ta k'waci kanta, ba yanda ta iya dole ta zuba mishi ido tana kallo har ya gama abinda yake ya mik'e, bala'i da masifa ta sha shi a safiyar tana ta fad'a wai ya zai mata fyade? Hak'urin ne ba zai iya ba na yau da tace? Hakan yasa ko yara bata shirya suka tafi makaranta ba sai shi ya shiryasu har mai d'aukarsu ya zo, sanda ya rakasu suka fita zai shiga d'akinshi tayi k'wafa tana fad'in "Kawai ku maza kun d'auki mata anfaninmu kenan a gurinku, kenan ba zaka iya zaman aure dani ba idan baka kusanta ta? Hmmm!" Juyowa yayi ya tako ya zo har gabanta ya tsaya, kallon idonta yayi yace "Saudat, ina kiyaye miki gayyato b'acin rai na, ki kiyaye gayyata ta raina ya b'ace a kan ki, ke baki san zafin zuciyata bane sai sanyinta, baki san hushi na ba sai hak'uri na, kar zaman aurena dake ya zama silar da zaki raina ni, wallahi ranki zai mugun b'ace a kan haka." Jinjina kai yayi shima ya shige d'akinshi, shiryawa yayi ya fito cikin farar shadda, duk da a falon ya ganta amma haka ya aje mata kud'i akan cantre teble d'in dake wurin ya fice.
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD