CHAFTER 6

2728 Words
Murmushi ya mata yace "Talatin da biyar da wata uku da kwana goma sha biyu." D'auke idonta tayi daga kanshi tace "Me ya kawoka?" Cike da isa da k'asaita yace "Lauyar da zata tsaya min nake nema." Kallonshi tayi fuskarta babu alamar wasa tace "Miye matsalar?" D'agowa yayi daga jinginar ya d'ora hannayenshi akan table d'in kamar yanda ita ma nata hannayen ke sama yace "Shari'a ce tsakanina da matata, mun rabu da ita, ina so na karb'i yarona amma ta hana, na nuna k'arfin ikona wajen karb'arshi, shine ta shigar da k'arata take so a karb'ar mata shi." Wani murmushin takaici tayi ganin yanda yake magana da gadara a ciki abinda bata san shi da su ba, girgiza kai tayi ta ci gaba da tambayarshi duk abinda ya kamata ta sani, daga k'arshe ne ta tambaye shi "Yaushe ne za'a saurari k'arar?" Saida ya sake jingina a kujerar yace "Gobe ne." Kallon mamaki ta masa ta aje alk'alamin hannunta tace "Kuma shine sai yau ka zo neman taimako? An fad'a maka lauyoyin basu da aikinyi ne?" D'aga kafad'a yayi alamar oho! Takardar data dinga d'aukar bayananshi ta d'auka ta mik'e tsaye ta zagaya inda yake zaune ta tsaya tace "Malam tashi fita anan ba zan iya ba, kaje ka nemi wani ko wata su tsaya maka." Jefa mishi takardar tayi tana dafe k'ugu da jiran ya tashi, wani shegen murmushi ya dinga saukewa har ya mik'e tsaye, gabanta ya tsaya hakan yasa ta ja baya tana had'e fuska sosai, sake matsawa yayi haka ita ma ta matsa shima ya matsa har ta kai ga bango, a hassale ta kalleshi tana nuna shi da yatsa tace "Tag.." Kasa fad'in sunan tayi dan haka tace "Bana son wannan shashancin, ka fice min a ofishi ba iskanci ne ya kawo ni ba." Zata wuce ta b'angaren damanshi yayi saurin d'ora hannunshi a bangon ya hanata wannan damar, ta d'aya b'angaren ta juya nan ma ya tareta da hannu, yanda kusancin nasu yayi yawa yasa ta duk'awa zata bi ta k'asanshi ta wuce, da sauri shima ya durk'usa ba kuma tare daya d'auke hannayenshi ba, dole ta soka kanta tsakiyar gwiwanta saboda rawar da jikinta ya d'auka zuciyarta na bugawa da sauri, duk yanda ta kai ga danna kanta tsakanin cinyoyinta hakan bai hanata jin k'amshin turaren dake matuk'ar sata jin abubuwa da dama ba. Ba zato ba tammani taji muryarshi a tausashe yace "Ina *ciki na* yake?" Da sauri ta d'ago ta kalleshi take hawaye suka zubo daga kurmin idonta, numfashinta da taji yana neman d'aukewa ne yasa ta kawar da kanta tace "Dan Allah bani wuri ina so nasha iska." Ba tare daya gyara mata ba yace "Sai kin ban amsa ta sannan." Da sauri ita ma tace "Idan ka matsa saina baka." Ajiyar zuciya taji ya sauke da har saida taji sautin iskan a fuskarta, mik'ewa yayi tsaye ya ja baya yana kallonta, da sauri ita ma ta mik'e tayi nesa dashi ta kalleshi tace "Fitar min a wurin nan ko nasa a fitar min da kai." Murmushi yayi tare da takawa ya koma ya zauna kan kujerar yana kallon yatsunshi yace "Amsata nake jira." Ba tare data matsa daga inda take ba ta kalli k'eyarshi tace "Babu wata alak'a data rage tsakani na da kai, abinda ya faru a baya ya riga daya wuce, dan Allah ka fita a nan." Juyowa yayi ya kalleta fuskarshi d'auke da murmushin nan yace "Amsar da zaki bani ita ce zata tabbatar min da akwai alak'ar ko kuma babu." Kawar da kanta tayi ba alamar wasa a muryarta tace "Na zubar, zubarwa nayi saboda banga anfaninshi ba." Da k'arfi ya mik'e daga kan kujerar ya yo kanta yana tsareta da idonshi, cikin wata birkitattar murya yace "Kin yi me? Akan me?" Juyawa tayi zata kalleshi sai taga kuma har ya k'araso kusanta kamar zai daketa, baya taja da sauri tana fad'in "Dan Allah ka fita nace." A tsawace cikin b'acin rai yace "Ba zan fitan ba *Fadu*, indi yini dahanuma gunin gi (Me kika d'auki kanki)?" Kaucewa tayi daga gabanshi ta nufi kujerarta tana fad'in "Harannuru (ban sani ba." Rik'e k'ugu yayi da duka hannayen biyu ya d'aga sama yana huci, ya d'an jima haka kafin ya sauke hannayen ya juyo ya kalleta, matsawa yayi kusa da kujerar daya tashi yace "Faduma na je sau da dama ina tambaya a kan ki, amma babu wanda yake kulani bare ya fad'a min wani abu dan gane da ke, Faduma na damu sosai akan halin dana jefaki, da k'yar na iya sanin cewa ba kya garin nan daga bakin yayanki Barka, ina ta tunanin ranar da zamu had'u zan ganki ne tare da abinda kika haifa, sai kawai yanzu kice min wai kin zubar, me yasa za kiyi haka Fadu?" Dafe kai tayi da hannu biyu cikin matsanancin kuka tace "Dan Allah *Tagur* bana son tuna komai akan bayana, bana so ka fita dan Allah, ni na manta da abinda ya faru, rayuwata nake yi yanzu sabuwa wacce nasha wahala sosai wajen ginata, kada ka sake ruguza min ita da wani tambihinka marar anfani." Shiru yayi na d'an lokaci sai kuma ya duk'a ya d'auki takardar daya jefa mishi, aje mata yayi kan teburin cikin muryar rarrashi yace "Dan Allah ki taimaka ki duba al'amarin nan nawa, sam banyi tunanin ganinki anan ba, a karon farko Faduma na rasaki, na biyu kuma na rasa abinda ya zauna cikinki, karo na uku dan Allah karki bari na rasa wani d'an nawa, karki duba abinda ya faru tsakaninmu Faduma, ki min wannan alfarmar a matsayin wacce aikinki ne dama." Saida ya sake tausasa murya yace "Dan Allah." Da sauri ya fita daga ofishin hakan yasa ta sake fashewa da wani kukan. Aminu da hankalinshi ya kasa kwantawa ganin ya jima a ciki, damuwarshi bata wuce ganin shima matashi ne, kuma ko dan ya dinga kallonta zai iya zama a ofishin, hakan uasa shi kasa zaune da tsaye, yana ganin fitarshi da minti biyu ya shigo da sallama, turus yayi ganin abinda ya jima bai gani ba, da sauri ya k'arasa yana fad'in "Subhanallahi, Faduma kuka? Me ya faru?" Jan kujerar yayi ya zauna yana kallon kanta dan ko d'agowa ba tayi ba, cikin tausasa murya ya sake cewa "Faduma, d'ago ki kalleni mana, kinfi kowa sanin damuwarki damuwata ce, duk abinda zai b'ata miki rai idan ina da iko zan tunkareshi na hana shi fuskantarki, dan Allah kiyi shiru ki daina kukan kinji, d'ago ki fad'a min me ya faru?" Saida ta samu ta saita nutsuwarta ta d'ago kai amma ta kasa had'a ido dashi, goge fuska tayi ta yi tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya sake cewa "Me aka miki Faduma? Wanda ya fita yanzu ya b'ata miki rai?" Girgiza kai tayi ta d'an kalleshi a kakkauce tace "Ba komai." Wani kallo ya mata yace "Ya zaki ci ba komai bayan ga komai ina gani a gabana, Faduma ko dai zaki fara b'oye min wani abu ne? Ni a ganina kamar babu abinda na cancanci ki b'oye min, duba da matsayina a wurinki da kuma gwagwarmayar da muka sha a baya." Kallonshi tayi da idonta har sun fara kumbara, saida ta sake jan majina ta kalleshi da k'yar ta iya furta masa "Shine, Abban Amjad." Ta k'arashe maganar da sake fashewa da wani kukan, waro ido yayi ya juya ya kalli k'ofar ya kuma kalleta baki bud'e yace "Abban Amjad? Kina nufin Tagur?" Jinjina mishi kai tayi ba tace komai ba sai kuka, ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yayi shiru shima, baisan me zai ce ba banda haushin mutumin da shi kanshi daya mishi iso zuwa wajenta. Suna zaman shirun nan wayar Aminu tayi sonn* (ring), ta jima tana sonne kafin ya d'auka yana sallama, jim yayi alamar yana sauraren abinda ake fad'a daga can b'angaren, cikin sanyin jiki yana kallon Faduma dake ta k'ok'arin share hawaye amma wasu na fitowa yace "Alhaji kayi hak'uri, a gaskiya ba zan iya maya dole ba idan ba zata karb'a ba, kuma kaga a k'urarren lokaci yayi magana, dan haka kawai ka fad'a masa yayi hak'uri." Da sauri Faduma ta kalleshi ta mishi alama da hannu cewa za tayi, d'an d'auke wayar yayi daga kunnenshi yana fad'in "Tu es s*** (Kin tabbatar)?" Da kai ta masa alamar eh, mayar da wayar yayi yace "Shikenan Alhaji, tace ba damuwa zata duba al'amarin." Takardar gabanta ta d'auka tana ji yana ci gaba da wayar, suna idawa ta kalleshi tace "Zaka taimaka min Aminu?" Cike da tausayinta yace "Zanyi Faduma, amma me yasa zaki shiga sabgar mutumin nan? Da kin barshi kawai ya nemi wani, kuma a d'an lokaci haka me zaki iya yi?" Mik'ewa tayi tana tattara kayanta ta sa a jaka tace "Karka damu ba zamu rasa abun yi ba insha Allah." Jinjina mata kai yayi yace "Yanzu me zan iya yi miki to?" Saida ta fara tafiya tace mishi "Muje." Mik'ewa yayi ya bi bayanta suka fita, saida ta rufe k'ofar ta kalleshi tace "Kaje ka same shi ku tattauna game da yaron, wane irin rik'o yayi mishi sanda ya karb'o shi, yanayin aikinshi, ma'ana mai tafiye tafiye ne? Idan mazauni ne wane lokaci yake fita kuma yake dawowa? Sannan ya dangantakarshi da yan uwanshi, yana da mahaifiya da yan uwa mata?" Numfashi ta sauke tace "Ni kuma zan je wajen matar nayi magana da ita, ya bani adresse d'inta." D'aga kai yayi ya nufi hanyar ofishinshi yana fad'in "Ba damuwa." Da sauri tace "Uhem Aminu." Juyowa yayi ya tsaya ta sake matsawa tace "Ya baka rahoton lafiyarshi dana yaron, idan kuma babu ya had'aka da likitanshi wanda ya yarda dashi." Jinjina kai yayi ya sake juyawa ya tafi haka ita ma mota ta shiga ta d'auki hanyar gidansu matarshi. _______________ Zaune suke su biyu sune sai wata data fito daga cuisine (madafa) rike da plateau (faranti) da indomie a ciki, ajewa tayi gabansu tana fad'in "Wai daga ina kuke haka uwar d'akina?" Saida Zaleeha ta sauko k'asa ta gyara zama tana cire mayafinta tace "Daga wajen wani lauya ne muke da aka had'amu dashi." Zaune tayi ita ma sai d'ayar data sauko k'asa ita ma tana fad'in "Lauya? Me zakuyi da lauya?" *Atta* ce ta kalleta tace "Lallai ma k'awata wallahi kin manta damu baki san me muke ciki ba, kina nufin duk abinda ake baki sani ba ma?" Duk da mamaki ta kallesu tace "Wallahi ban sani ba, me ya faru dan Allah?" Tab'e baki Atta tayi sai Zaleeha data fara cin indomien tace "Kenan baki da labarin wannan d'an yarinyar yaje har gida ya d'auke *Ridwan*?" Jinjina mata kai tayi tace "Na sani mana ta fad'a min." "To ai shiyasa ta shigar da k'ararshi kotu dan a karb'ar mata shi." Cewar Zaleeha, kallonta *Abeeda* tayi tace "Da gaske K'awata? Me yasa zakiyi haka? Madadin ki karb'eshi ta sulhu? Kuma naga tunda dai d'anshi ne muye ma sai kin b'atawa kanki lokaci, kiyi sabgar gabanki mana." Atta da Zaleeha ne suka kalli juna sai Zaleeha da tace "Ai ba zai yiwu ba, wannan yaron dole ya zauna wurin ko kuma wani mummunan abu ya faru marar dad'i, idan mukayi sakaci to ba wurin Tagur ba har ita kanta akwai wanda zaiyi bugun gaba da hakan ya karb'eshi kuma ya karb'u in fad'a miki." Da mamaki Abeeda tace "Kamar ya? Kina nufin dangin Tagur d'in?" Wani murmushi tayi mai ma'ana tana jefa lomar indomie tace "Hum! Shima da yasan alak'ar dake tsakaninshi da Ridwan da bai yarda ya karb'eshi ba." Da sauri Atta ta rik'o hannunta tana mata wani kallo, da ido sukayi zaurencensu haka yasa Zaleeha zanca magana da fad'in "Ai in fad'a miki wata shegiyar lauya na so had'aki da ita mai shegen wayo da tone tone kamar kaza, to haushi ta bani wallahi saboda dalilinta yanzu haka nake zauna, da yanzu fa ina shirin amarcewa da Alhaji na." Abeeda ce tayi dariya tace "Gaskiya kam ta cuce mu." Jinjina kai tayi tana fad'in "Haba ki barni da ita, ai wallahi saita raina kanta dan saita zubar da hawaye." Atta ce ta kalleta tace "Ke kuwa uwar d'akina me zaki mata? Ki rabu da ita kawai ki shiga wata harkar, idan da rabo sai kiga Allah ya kawo wanda yafi Alhaji." Girgiza kai tayi tace "Um um Atta! Barni wallahi saina gurza mata nima, in kin fad'i haka saboda Alhaji uwata kuma fa? Ba dan Allah ya taimaka ba an shiga an fita aka fito da ita, da yanzu kina jin ina Mama take? Tana d'aure fa a dalilinta, ai wallahi sai na ci uwarta ta gane bata da wayo, shiyasa na tambayi komai a kan ta nasan wacece ita, dan nasan ta inda zan b'ullo mata." Jinjina kai Abeeda tayi tace "Lallai zata shiga uku matar nan." "Ba kad'an ba ai." Cewar Atta ita ma tana saka hannu a abincin, haka suka ci gaba da cin abincin suna hirarsu. ________________ Bata samu Atta a gidan ba sai mahaifiyarta da mahaifinta, tun shigarta gidan ta fahimci matar gidan ita ke sarrafa gidan, alamu sun nuna mijin baya iya wani hubb'asawa a cikin al'amuran gidan, haka ta dinga fad'awa Faduma abubuwa marasa dad'i akan Tagur ka rantse bata da mak'iyi a duniya sama da shi, ko kuma bai tab'a mata wani abun alkhairi ba, kuma duk hakan saboda ya saki 'yarta ne kawai, ita dai har saida taji maganganun matar sun hau mata kai sannan ta mata sallama ta tafi. A b'angaren Aminu ma ya samu wasu bayanai daga gare shi, wajen rahoton lafiyarsa ne yace gaskiya baya da, akwai kuma takardun dale d'akin Atta a lokacin da yayi had'ari ita ta rik'esu, kuma a gaskiya yanzu baya son wani abu da zai sake shiga tsakaninshi da ita, ganin babu wata tsayayyar magana yasa Aminu kiran Faduma dan ya sanar da ita yaji yanda zasuyi, a lokacin ta fito daga gidansu Atta ta d'auk. Bayan ya fad'a mata ne tace "Aminu muna buk'atar rahoton lafiyarshi, saboda ta hakane zamu samu wanda yafi cikakkar lafiyar da zai iya kula dashi, hatta mutanen da yaron zai zauna dasu in so samu ne zamu so musan lafiyarsu da hallayensu, yin sakaci da wannan abubuwan zasu iya janyo lalacewar tarbiyar yaron da wasa da lafiyarshi, hakan ba abinda zamu so bane." Ajiyar zuciya Aminu ya sauke yace "Ya zamuyi yanzu kenan? Dan da fari yace ko zai had'amu da wani likita abokinshi." Da sauri tace "Ba matsala ya had'amu in dai yasan zamu samu abinda muke so." "Ok bari muyi magana." Ya fad'a yana shirin kashe wayar tace "Saurara." Dakatawa yayi yace "Uhum!" A hankali tace "Yana kusanka?" "Eh." Ya fad'a yana satar kallon Tagur da yake danna waya, d'orawa tayi da "Ka sani a speaker zanyi magana dashi." Saida ya saka yace "Zaki iya magana." Aje wayar yayi akan table d'in dake gabanshi yana kallon Tagur, cikin sanyin murya sosai tace "Ina da sharad'i a aikina, in ka amince zan iya ci gaba da aikin, in kuma baka amince mu dakata daga nan." Kallon juna sukayi Tagur da Aminu sai kuma ya kalli wayar, nuna kanshi yayi alamar wai dashi take? D'aga masa kai yayi cike da jin haushinshi dan shi tunda yasan waye shi yake jin kamar ya rufe shi da duka. Kamar yasan me yake tunani kuwa sai ya saki wani murmushin rainin hankali ya d'ora hannayenshi akantable d'in yana kallon wayar yace "Wane sharad'i kenan Fadu?" Cikin fad'a kamar zata cinye shi tace "Karka sake kirana da wannan sunan." Murmushi yayi mai sauti tare da fad'in "To naji na daina, miye sharad'in?" A hankali tace "Sharad'i shine duk wanda zan tsaya ma ina yin aiki tuk'uru wajen gano gaskiya, ina kuma bayyana gaskiyar ko da kuwa laifin zai shafi wanda nake karewa ne, zan tsaya maka amma idan har na lura yafi dacewa uwar ta rik'e d'anta to shakka babu zan koma tsagenta ne na gabatar da abubuwan da zasu nuna cancantarta wajen rik'eshi, ka yarawa?" Cikin murmushi kamar yana gabanta ya kalli Aminu yace "Na amince, amma wai yaushe kika zama lauya ne." "Wannan kuma matsalarka ce." Ta fad'a tana kashe kiran, girgiza kai yayi yana dariya ya ma manta da Aminu na gabanshi ya mik'e tsaye yana fad'in "Faduma bala'i, Faduma rigima, har yanzu tana nan yanda take bata canza ba, hummmummmmhmmm." Wani kallo Aminu ya masa yana harareshi ya mik'e tsaye shima a shagub'e yana fad'in "...
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD