CHAFTER 7

3542 Words
"Faduma sarauniyar taushi ce, bala'i da masifarta tana yinshi ne ga wanda bai mata kirki ba." Tsam ya tsaya yana kallon Aminu kallon tuhuma, kallon me kake nufi da abinda ka fad'a? Me kake nufi da taushi? Kai tsaye ya daddala masa harara tare da juyawa ya koma ya zauna, tab'e baki Aminu yayi alamar ko oho, juyowa yayi ya kalleshi yace "Na d'auka can zamu tafi?" Da wata muryar dak'ilewa yace mishi "Na fasa." Ajiyar zuciya Aminu ya sauke ya juyo da kyau yana fuskantarsa, d'ora hannu yayi akan kujerar daya tashi yana kallonshi yace "Ina zan samu likitan? Duk aikin da Faduma ta bani ina cikashi, yau ba zai zama na farko kuma a kan ka ba." Banza yayi da shi yana rubutu da alk'alami a takarda, saida ya gama ya tura mishi takardar gabanshi ba tare daya kalleshi ba, yana ganin haka shima ya d'auka ya duba, ganin adrese da sunan Dr. ne yasa shi juyawa yana sake tab'e baki ya fice. Da wani mugun kallo ya bishi, lokaci d'aya yaji ya tsani yaron da baisan komai a kan sa ba bayan sunansa da aikinsa, yana ji kuma kamar baida mak'iyi sama dashi, fatanshi kawai Allah yasa babu komai tsakaninshi da Faduma, dan har yau har gobe yana *son* Faduma, rashin sanin inda take yasa ya dunfari rayuwarshi ta gaba, amma fa bai manta data baya ba, Faduma ba ta shiga rayuwarshi bane dan ta fita, shiyasa ma yanzu ta dawo gare shi, zai kuma tsaya tsayin daka da jajircewa wajen ganin ya same ta, yasan zaisha wahala sosai da fuskantar matsaloli bila adadin, daga wajenta ita kanta, wajen iyayenta da suke kallonshi mutumin banza marar amana da alk'awari, da kuma nashi iyayen ma zai fuskanci wani k'alubalen duk da ba mai girma bane, amma hakan ba zaisa ya ji tsoro ba ko ya sare, dan babu wannan tsarin a tsarinshi ko kad'an, yanda duka b'angarorin ke tutiya da jin cewa su jinin tubawa ne, haka shima wannan jinin ne ke yawo cikin jikinshi, dan haka sai inda k'arfinsa ya k'are. Ta fito daga wajen malam *Lawali* wanda take tambayarshi abinda ya shige mata duhu, musamman in tana so tasan hukuncin da shari'ar musulunci ta tanada, kiran Aminu ne ya shigo wayarta ta d'auka tana fad'in "Aminu ya ake ciki?" Daga b'angarenshi ya amsa mata da "Faduma d'an rainin hankali ne mutumin nan, yanzu haka fa wajen Dr. d'in ne zan tafi ni kad'ai." Wani murmushi ta feso mai ban haushi tace "Na sani Aminu, manta dashi kawai, yanzu ina ne asibitin saina sameka acan?" Kai tsaye ya amsa mata da "Clinik Alheri." Jinjina kai tayi tace "Ok gani nan zuwa." Datse kiran yayi ita kuma ta shiga wata kwanar da zata bata damar hawa kan titin daidai, duk da ta titin yar kasuwa ta bi ta manta da lokacin tashin Amjad yayi, sam bata mantawa duk yanda aiki ke shan kanta, amma yau na farko ta manta dashi a makaranta ta wuce inda zasu had'u da Dr. d'in ________________ Ko da ta dawo gida mamanta ke fad'a mata yanda sukayi da lauyar sharewa kawai tayi tana fad'in "Ni naji dad'i ma wallahi da bata same ni ba." Cike da gargad'i uwar tace "Wallahi Atta ki tabbatar kun samu tsayayyen da zai tsaya muku, kinga ba zanyi asarar kud'i na dana ranta miki kika d'auki lauya ba, sannan ba zan yarda wannan shegen mijin naki ya rik'e yaron nan ba, dan in haka ta faru mun shiga uku mun lalace babu hanyar samun kud'i daga gareshi." Tsaki taja mai sautin gaske tana nufa d'aki tana fad'in "Wa yace miki ma zai zauna hannunshi ne? Ko baya ma Allah sai Ridwan ya dawo hannu na, ai ina da hanyoyin da zan dawo dashi cikin sauk'i ba tare da an ji kanmu ba, kawai dan insa kotu ta tirsasa mishi barinshi wurina ne, sannan a wajabta mishi d'aukar nauyinshi ta yanda duk wata zai dinga dire min masu gidan rana nayi haka." Saida ta ga shigewarta d'aki tayi murmushi k'asa k'asa tace "Ni ma kuma sai kin dinga biyana ko na dinga rik'e miki shi in zaki tafi yawon iskancin naki, dan yanzu duniya gwamnati ta hana aikin banza, ba zan duba 'yata ce ke ko shi jikana bane wallahi, ah to ba sauk'i a al'amarin." _______________ Sun ji dad'in yanda suka samu ganin Dr. d'in duk da yana daf da tashi daga aiki dan 12:00 ta wuce, ya karb'esu da mutumtawa ganin masu ilimi ne da kuma masaniyar da suka bashi, hakan yasa har ya sake kiran Tagur suka sake magana, saida ya gama wayar ya kallesu da kyau ya duba wani babban littafi ya aje shi gabanshi, dubawa ya shiga yi tsawon mintuna kafin ya tsaya akan wani shafi ya cire gilashin idonshi ya kallesu yana turo musu littafin yace "Wannan dai kusan shine na farko kuma na k'arshe a reccord d'inmu, ba wani mai yawan jinya bane, yana yi sai dai bai son zuwa asibiti, kusan ma idan zazzab'i ya bashi wahala yakan kirani naje gida na dubasa." Numfasawa yayi ya ci gaba da cewa "Babu wata rashin lafiya a tare dashi da akan iya d'auka, kama daga ciwuka masu sauk'in jinya har zuwa ga manya ma, kusan ni ne likitan dake duba har mahaifiyarshi da yan uwanshi mata biyu, da kuma ita kanta matarshi, to amma..." Duk ido suka zuba mishi suna kallonshi da saurarenshi, d'orawa yayi da fad'in "Yaron yana da athma, kuma ta mahaifiyarsa wacce take fama da ita shekara da shekaru, babbar matsalar kuma ita ce shi yaron tashi athmar chronique ce." Kusan a tare ita da Aminu suka sauke ajiyar zuciya, kallonta Aminu yayi yace "Dole ta rik'e yaronta kawai, tunda asim (athma) ciwon da ake d'auka ne, ko uban bai d'auka ba wasu yara dake tare dashi zasu iya kamuwa." Jinjina kai tayi alamar eh, kallon likitan tayi tace "Mun gode daka bamu lokacinka, zamu tafi." Duk mik'ewa sukayi Aminu har ya bud'e k'ofar Dr. d'in yace "Baki ji ba." Juyowa sukayi saiya kalli Faduma yace "Zamu iya yin magana daga ni sai ke?" Kallon juna sukayi da Aminu sai kuma ya kalleshi yace "Me yasa sai daga kai sai ita?" Kallon Aminu yayi fuskarshi a d'aure yace "Saboda zamuyi sirri ne." Kallon Aminu tayi dake shirin magana tace "Shikenan ka jirani.a waje." Dawowa tayi ta zauna sai Aminu daya dinga kallonsu yana hararen Dr. d'in, k'wafa yayi ya fita daga ofishin yana banko k'ofar da k'arfi, kallonshi tayi ganin yana kallon k'ofar da Aminu ya rufo tace "Uhum ina ji." Kallonta yayi ya d'ago daga kujerar yana d'an lilawa da ita ya had'e hannayenshi, cikin nutsuwa yace "Haka kawai naji hankali na yafi kwantawa da na fad'a miki sirrin nan, bansan ko zai miki anfani ba? Amma dai abune daya jima yana damuwa, kuma kullum na tuna da abun na kan jefawa kaina tambayoyi cewa *ya akayi haka ta faru*? *Dama ana iya samu ne*? Daga k'arshe kuma saina jinjina k'udirar ubangiji akan bawan nasa." Wani kallo mai kama da harara ta masa tace "Ban fahimci inda zancanka ya dosa ba har yanzu? Ko zaka iya fad'a min me kake nufi?" Ajiyar zuciya ya sauke ya sake kallonta ya cire gilashinshi yana sake matso da kujerarshi yace "Kin gane ko? Shekara biyar da suka wuce Tagur yayi wani mummunan had'ari, ranga ranga aka d'aukeshi aka kaishi babbar asibiti (H******), yayi jinya sosai a block na tsayin wata hud'u, daga baya kuma ya warke lafiya lau aka sallamesu suka koma gida, a ranar da aka sallamesu likitan dake dubashi ya buk'aci yayi magana dani a matsayina na amininsa kuma likita, da kuma d'aya daga cikin shak'ik'anshi, a lokacin daga matarshi sai mamanshi da kuma yayarshi wacce suke uba d'aya *Gomboy*, lokacin da Gomboy tace zata je babu wanda ya hanata, har zamu shiga ofishin sai kuma Atta ita ma tace zata je tunda abinda ya shafi mijinta ne, bamu barta ta shigo ba har likitan ma bai goyi bayan haka ba, a wannan rana ya fad'a mana abinda ya d'aga mana hankali sosai, daga ni sai ita muka san da wannan abu." Gitgiza kai yayi yana d'auke kallonshi daga fuskar Faduma yace "Kuka tayi sosai tana rok'ona alfarmar karna fad'a masa saboda ba zai iya d'auka ba, na kuma gamsu da abinda ta fad'a min naja baki nayi shiru, abun mamaki sai kawai na ga matar Tagur ta zo asibitin nan awon ciki bayan wata shida da faruwar wannan lamari." Wani murmushi yayi yace "Kamar tasan abinda naje tambayarta kenan sanda naje gidan, sai tayi saurin tarata da cewa wai naga ikon Allah ko? To gaskiya na yarda dan ikon Allah yafi k'arfin wasa, na fad'a miki ne dan bansan ko zai miki anfani ba." K'ura masa ido Faduma tayi, kama daga idonshi zuwa labb'anshi duk kallon yanayinsu take, kallon hannayenshi tayi da sula ya had'esu, basa rawa kuma baya yawan motsasu, d'an numfashi ta furzar tana sauke hannunta daga kan hab'arta data tangale, ita ma kamar yanda ya ma hannayenshi tayi tace "Me likitan ya fad'a muku? Ba zai iya haihuwa ba?" Da sauri ya d'aga mata kai alamar eh, jinjina kai tayi ita ma tana cije leb'e, kallonshi tayi tace "Akwai bayanin haka a rubuce? Ko kuma kana da wani abunda zai tabbatar min da haka?" Girgiza kai yayi yace "Gaskiya bana da, amma in kina so zan iya had'aki da likitan." Kyab'e baki tayi tace "Rubuta min, zanje na same shi." K'aramar takarda ya d'auka ya rubuta mata ya mik'a mata, mik'ewa tayi tana karb'a ta kalleshi tace "Amma kana ganin Gomboy ta fad'a mishi kuwa?" Girgiza kai yayi yace "Ban sani ba gaskiya, dan ban tab'a mishi maganar ba, amma dai sanda na ga Atta da ciki da sanda ta haihu ma na dinga zolayarshi, amma sam baiyi alamun ya gane me nake nufi ba." Jinjina kai tayi ta juya zata fita tace "Nagode." Da kallo ya bita har ta fita, wani k'aramin murmushi ya saki, har ranshi ta birgeshi yanda yaga ta dage tana son samun tabbacin lafiyarsu daga bakunan likitoci ba shaci fad'i ba. Yana ganin fitowarta ya k'ureta da ido kamar mai jiran karin bayani, da tuhuma ya tambayeta "Me ya fad'a miki? Faduma ya zaki yarda ku keb'e daga ke sai shi wai zakuyi magana?" Murmushi ta sakar masa cikin rarrashi da zolaya tace "Allah dai ya huci ran oga Aminu, kayi hak'uri kaji ba san sake ba, nasan nayi kuskure." Saida ya sake had'e fuska yana hararen ofishin da suka fito yace "To me ya fad'a miki?" Kallon mamaki ta masa tace "Sirri mukayi fa." "Sirrin nake so naji Faduma." Ya fad'a da k'arfi, a tsorace ta kalleshi jin yanda ya d'aga mata murya yana matsowa daf da ita, d'an ja baya tayi tana juyawa bayanta sai kuma ta kalleshi tace "Dan Allah ka manta da mutumin nan, me yasa ranka ke b'acewa? Kawai fa mun tattauna ne kan abinda muka tattauna tun a gabanka." Girgiza kai yayi yana ja baya yace "Ba gaskiya bane Faduma, amma ki sani koma me ya fad'a miki wallahi bai kai ko rabin abinda ni nake ji a zuciyata a game dake ba." K'aramin murmushi tayi kawai tace "Kaje a motarka, nima zanje na ga wani Dr. ne a babbar asibiti." Da kallo ya bita kawai yana jin shifa ya fara gajiya da wannan abun, kawai zai fito ya fad'i abinda ke zuciyarshi kowa ma ya huta, amma ba zai iya jurar ganin ana kawo mata hari ba. Tana zuwa Eguillage ta samu labarin yau likitan baya aikin safe sai k'arfe 15:00 na yamma zai shigo, da k'yar ta samu mutumin ya mata alfarmar rubuta mata takardar da idan ta dawo anjima zata samu ganin likitan kai tsaye ba tare data jira ba, godiya ta masa ta juya zata koma mota, *Amjad*, shine sunan daya zo mata a rai bazata, da k'arfi ta dafe k'irji ta bud'e baki taja numfashi, da sauri ta shiga lalubar wayarta a jaka, tana dubawa da k'arfi ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, 12:58, ina aikin me na manta da yarona?" Da gudu ta nufi mota sam bata kula da yanda ake kallonta ba, tana zuwa ta bud'e da sauri ta shiga taja da k'arfi kamar motar ta k'wace mata, karo na farko a rayuwarta da zata iya cewa tayi gudun ganganci akan hanya ba sai yau. _______________ Ganin 12:40 tayi yasa mai adaidaitar kiranta ya sanar da ita wallahi yana hanyar d'aukosu adaidaitar ta lalace, cikin jin haushi ta balbaleshi da masifa har ta kashe wayar, kiran Hasheer tayi yana d'auka babu sallama ko wani abu tace "Yara nace kaje ka d'aukosu, mai adaidaitar yace ta lalace baije ya d'auko su ba." Wani bak'in ciki ne ya taso mishi a wuya, magana cikin rashin wayo da taunawa da bayar da umarni, k'ittt ya kashe wayar kawai dan da yana gabanta saiya nuna mata bai ji dad'i ba, dan yana tare da abokinshi duk da bai ji ba, amma ai zai iya fahimtar wanda ya kira baiyi sallama ba bare a gaisa, kallon abokin nashi yayi yace "Ina zuwa dan Allah zan d'auko yara a makaranta ne." Cikin fara'a ya amsa da "Ba damuwa, saika dawo." Fita yayi ya d'auki hanyar makarantar, yana zuwa kam ya samu yaran su uku tsaye daga ciki dan mai gadi bai barsu fita ba. Yana shiga daga ciki suka ruga suka rumgume shi suna fad'in "Abba yau da kanka ka zo d'aukarmu?" "Um." Ya amsa musu dashi yana kallon Amjad daga can baya duk ya takure da alama ma hawaye yake sharewa, kallon Sharfudeen yayi yace "Waye waccen?" Da sauri yace "Abba shine wanda Mamanshi ta kai mu gida jiya, shima yau mamanshi bata zo ba tun d'azu yake jiranta." Kama hannunsu yayi yana nufa wajenshi yace "Ayya, ko lafiya?" Suna k'arasawa ya tsaya gabanshi ya dafa kanshi yana fad'in "Sannu ko, mamanka ce bata zo ba?" Ja baya yayi yana fad'in "Ina wuni." Da fara'a ya amsa da "Lafiya lau, muje saina kaika gida kaga rana tayi sosai, ta yiwu wani aikin ne ya rik'e mamanka." Girgiza kai yayi yace "Babu aikin da ke sa Ayya ta manta dani, nafi tunanin ba lafiya ba." Ya k'arashe maganar da sako da wasu hawayen, matsawa yayi kusanshi yana fad'in "Ah haba kar kayi wannan tunanin, insha Allahu babu komai ka yarda da abinda na fad'a maka, muje saina kaika gidan." Girgiza kai yayi yace "Um um ka tafi kawai, Ayya ta hana ni tafiya da duk wanda ban sani ba." Murmushi yayi yana jinjina tarbiyar da yaron ya samu daga iyayenshi yace "Amma ai ni ka sanni tunda ni ne Abbansu Sharfudeen." Girgiza kai yayi yace "Zan jira Ayya na san bata manta dani ba." Ajiyar zuciya ya sauke yana fito da wayarshi ya mik'a mishi yace "To ga wayata saika kira Abbanka, amma ba zan tafi ba har sai na tabbatar kaima ka bar wurin nan." Da sauri ya kalleshi sai kuma yayi k'asa da idonshi cikin share wasu hawayen dake ta mishi malalowa yace "Aba na ya rasu tun kafin a haife, ni ban sanshi ba ma ko da a hoto ne." Yanda yayi maganar cikin sigar tausayi sosai yasa Hasheer jin tausayin yaron sosai kamar zai mishi kuka, dafa kanshi yayi yace "Sannu kaji, Allah ya jik'anshi da rahama." Cikin qhare hawaye sosai yace "Ameen." Sake mik'a mishi wayar yayi yace "To kira Ayyar ka." Jinjina kai yayi ya karb'a yana fad'in "Nagode Obdo (kawu)." Murmushi yayi yace "Sai naji harshenka wani wuri, ba bahaushe bane kai?" D'aga kai yayi yace "Eh, duka iyayena tubawa ne shiyasa nima na zama batube, amma a garin nan aka haifeni kuma anan na tashi." Cike da k'aunar yaron lokaci d'aya ya jinjna kai alamar gamsuwa, yana shirin danna ok Faduma ta kutso cikin makarantar ko rufe mota ba tayi ba ta fita, duk da lafayarta ta sauka daga kanta amma bata damu data gyara ba idonta na kan Amjad, yana ganinta shima ya mik'a mishi wayar da gudu ya k'arasa gareta, rumgume juna sukayi cike da murna, sumbatar wuyanshi tayi tace "Kayi hak'uri kaji yau aiki ne yasha kaina, amma insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba." Shima saida ya sumbaci goshinta ta saukeshi k'asa sannan yace "Na sani Ayya haka kawai ba zaki barni nan ba, amma a yau na tabbatar da cewa Ayyata ce komai nawa." Dariya tayi ta lak'ace mishi hanci tana fad'in " Wannan *Oddonur* (d'ana ne) ne." Rumgumeta yayi shima yana dariya yace "Wannan Ayyata ce." Sai lokacin ta sake kai kallonta wajen su Izzadeen, kamoshi tayi yana mak'ale a jikinta ta shiga gyara lafayarta ta d'ora sama kai suka k'araso. Tunda ya sauke idonshi akan fuskarta gabanshi ya shiga luguden fad'uwa, komai na jikinshi harbawa ya shiga yi musamman gudun jininshi daya ninku, wani abu yaji yana tafiya a hankali yana ratsa duka sassan jikinshi, abune daya jima bai jishi ba ko akan Saudat, wani haske ne yaji ya mamaye zuciyarshi tare da saukar mishi da wata sanyayyar nutsuwa, yanda ta nuna matuk'ar kulawarta akan yaron ya birgeshi, kyakyawar fuskar ta gigita lissafinshi, sanda take sakin sayayyan murmushi kuma ya tafi da duk wata damuwarshi da b'acin ranshi, sanda ta lak'ace hancin Amjad ta fad'ad'a dariyarta sai yaji kamar zai suma, sai kuma ya gasgata abinda yaranshi suka fad'a cewa mai murmushi duk sanda zatayi magana, ya yarda kam a yanzu duba da tunda ta fito a mota hak'oranta basu b'uya daga kallonshi ba. Yanzu haka kuma da take takowa kamar hawainiya cikin tsananin nutsuwa da kamala da kuma aji da k'asaita, vibration d'in da wayarshi tayi dake hannunshi ne yasa shi saurin dawowa hayyacinshi, ba dan haka ba data tsargu da kallon da yake mata, tana isowa shi kuma ya duba mai kiran, d'auka yayi ya d'an matsa gefe dasu ya amsa, lokacin ita kuma ta bawa duka yaran hannu sun gaisa duk yana hangensu, yanzun ma karkace yayi yana tsinkayen fararen hak'oranta, yanda kumatunta ke ta faman lob'awa ne kawai yaji dariya ta sub'uce mishi, maganar da akayi a waya ya fargar dashi yana fad'in "Zan sake kiranka dan Allah." Kashe wayar yayi ya tako a hankali ya matso kusansu, yana zuwa saida ya sauke b'oyayyar ajiyar zuciya saboda wani irin k'amshin turare daya daki hancinshi, k'amshi ne mai dad'in gaske wanda lokaci d'aya ba zaka gane wane irin turare bane, k'amshinshi kamar na wuta amma kuma yana da sanyayyan k'amshin da yake nuna humra ce ko kuma an had'a biyu ne, cikin daddad'an sauti ya tsinkayi sautin tattausan murya cikin sark'ewar harshe mai surkin hausada tubanci tana fad'in "Sai dai ku ku fad'a min ranar da zaku fara zuwa, idan kuka zo na gani saina kai muku shi har gida shima." Ganin ya k'araso ta kalleshi cike da kunya ba tare da sun had'a ido ba tace "Ina wuni." Ba tare daya d'auke idonshi daga kanta ba yace "Lafiya lau." Nan ma bata kalli idonshi ba sai k'irjinshi tace "Nagode da taimakon daka min, naji dad'i da baku tafi kun barshi anan ba shi kad'ai, nagode." Kallon yaran tayi ta d'aga musu hannu tana fad'in "Bye bye, sai anjimanku." Ta juya zasu wuce ita da Amjad taji yace "Nima nagode." Tsayawa tayi ta juyo, karon farko da suka had'a ido, take taji gabanta ya fad'i sai kawai tayi saurin kawar da nata idon tace "Akan me fa?" Wani murmushi ya saki yana ci gaba da kallon fuskarta yace "Jiya sun fad'a min ke kika kaisu gida, nagode sosai." Murmushi ta masa wanda ya tafi da gaba d'aya imaninshi ya saki baki wajen kallonta, a hankali ta furta "Ba komai, ai 'ya'yana ne suma." Kallon yaran yayi yace "Muje." Dukansu suka ranka yaran na gaba su kuma suna baya, jin idonshi a kan ta ne yasa ta tsayawa baya tana tafiya cike da kunya, shi kam kanshi k'asa yake amma yanda take sauke k'afa fa yanda take d'aukewa duk a kan idonshi, lallen dake k'afafunta bak'i da ja dogayen akaifunta data rufesu da jan lalle, yanda lafayar ta d'auru sosai tare bud'ewa duk in ta wurga k'afarta cikin nutsuwa, sai yaji kamar ya tsaya haka yana ci gaba da kallonta. Suna kaiwa kowa motarshi ya nufa, saida ta bud'e zata shiga ya sake fad'in "Sai anjima." Saboda tukara da tayi da kallon da yake mata yasa ta kalleshi kawai ta jinjina kai, bud'a motar kowa yayi ua shiga suka d'aga, duk da tasan gidansu na gaban nasu kuma hanyar d'aya ce, amma yanda duk sanda kallonta ya kai kan motar sai taga idonshi a kanta yasa taji haushi ta canza hanya, saida ya daina ganinta ya dawo cikin nutsuwarshi ya tuna shi fa babban mutum ne, akwai buk'atar ya kama kanshi kar zalamarshi ta fito fili lokaci d'aya. Murmushi kawai ya sake saki shi kad'ai ya zura hannu ya d'auki wayar zai kira wanda yace d'azu, yana bud'e s******* d'in lamba ta fito a wayar reras, d'an kallon mamaki yayi alamar bai gane ba, lokaci d'aya kuma ya zaro ido ya bud'e baki, wani murmushi ya saki har hak'oranshi na bayyana, cikin kallon gabanshi da kuma wayar yayi enregistrer (seve) lambar da sunan *Murmushi na*. Wani murmushi ya kuma saki sanda ya kalli sunan, tab'e baki kawai yayi ya aje wayar gefe.
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD