CHAPTER 1
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Ya Allah, Ubangijin tsintuwa da ɓacewa,
Ka sanya wannan littafi ya zama haske a cikin duhu, ya zama sako na hakuri ga wanda haushin rayuwa ya dabai, ya zama ta'aziyya ga talaka, da tunatarwa ga mai dukiya.
Ya Allah, duk kalmar da ke cikinsa da taɓa zuciya, Ka sanya ta zama dalilin sauyin rayuwa mai kyau. Duk kuskuren da ke cikinsa, Ka yafe min, domin kai ne Masani, ni kuma mai neman gaskiya ne.
Ya mai juya kaddara, Ka juya kaddarorinmu zuwa ga mafi alkhairi.
Allahumma amin.
*TSINTACIYA*
by
Ameena m Abdullahi
Ga shimfida mai jan hankali da zaka iya sakawa a farkon littafinka *TSINTACIYA*:
---
*TSINTACIYA*
Akwai abubuwan da bamu nema ba, amma kaddara ta kawo mana su.
Akwai kuma abubuwan da muka nema da gaske, amma har abada bamu same su ba.
Wani ya tsinta dukiya a inda wani ya tsinta kaskanci.
Wani ya tsinta farin ciki a cikin talauci, wani kuma ya tsinta bakin ciki a tsakiyar mulki da kwanciyar hankali.
Wannan littafi ba labarin tsintuwa kawai bane. Labarin rayuwa ne.
Labarin yadda hakuri yake mayar da tsakuwa lu'u-lu'u.
Labarin yadda kaddara ke wasa da mutum, ta daga talaka ta sauke mai mulki.
Labarin yadda sauyin rayuwa ke zuwa a daƙiƙa guda - daƙiƙar da zaka tsinta abu daya da zai sauya duk rayuwarka.
*TSINTACIYA* zai koya maka cewa:
Dukiya ba ta nuna darajar mutum.
Talauci ba laifi bane.
Kuma tausayi... tausayi shi ne dukiyar da ba ta taba faduwa.
Idan ka taba jin an manta da kai,
Idan ka taba jin duniya ta yi maka nauyi,
Idan ka taba tsinta wani abu da ya girgiza zuciyarka...
To wannan littafi naka ne.
Bude shafin farko. Shiga duniyar TSINTACIYA
Bismillah rahamanu Rahim wassallalahu Allah nabiyu
.............. hadarine agarin yayi bakyinkyirin cikin kankanin lokaci ruwa ze iya sauka ga iska me
sanhi da saukar da nutsuwa da take kadawa a hankali jejine gurin ba sosai ba se dogayan
bushiyu da sukaiwa jejin kawanya, agefe guda Kuma wasu kyawawan fararan fulanin dajine
ke tafiya cikin nutsuwa Amma kana ganninsu zakasan sauri suke. Bazasufi shekara 15
aduniya ba suna sanhe da kalkin saki ajikinsu Riga da zani da tukunyar kasa a hannunsu da
alamu ruwane aciki, Daya daga cikinsu ce cikin harshen fulatanci ta ce
"MUHSINAH muhi sauri fa Kinga hadarinnan Kara kaimi yake, in ruwa ya ruskeme bazamu
komai gida da huri ba gashi ke inna dellu zata iya dukanki ni da dauki" dogon nufashi wadda
aka kira taja cikin muryarta me sanhi da Dadi ta na cewa "Indo wlh saurin nake ga gajiya dake
damunta, nafiki San mukima gida da huri,
"Wai sauri kike a Ina kike saurin MUHSINAH? Mehisa kike haka ne kina Gani de mutannan rugarnnan kowa hi yake dake akan izza da sarauta gashi ke ba yar kowa ba ki rabu da abinda
kike kiji da matsala Daya mana, tafada cikin damuwa. "hmm Indo har dake? Kinsan bahin
kaina bane inaso na gyara tafiyata irin ta kowa Amma na kasa kodan hinda ake Dani ai zanso
nagyara Amma Indo nakasa, tafada hawahe masu zafi da Kuma na tsiyayo mata.
"Kinga MUHSINAH Allah ya huci zuciyarki ni Bada wata manufa na fada ba nafadi abinda
yan rugarnnan ke fadane kawai, Amma kihi hakuri kuka banajin bane kinji'?" Tafada tana
share mata hawahe, murmushi MUHSINAH tah i wadda a kullum ke Kara mata kyau ta ce
"Babu koma Indo kawai yanzu muhi sauri mukima ruga Kinga an fara yayyafi, Kuma in
yatabani affana ze game kokuma cihona yatashi, Kai Indo ta daga mata takama hannunta
suka shuga wata yar bukka tana cewa,
"Gwanda mu fake Annan don in muka huce Babu wajan tsayawa Kuma daga Gani
ruwannan da gaske yake, tsayawa sukai suna kalon yadda ruwan yafara karfin ga sanhin
damunta da kamshin kasa da yake tashi mesanyaya zuciya da saukar da nutsuwa,
"Kinga kwa na manta ya kwa dazu kuka Karke da inna dellu, anga kudin kuwa?" Ara Zane
MUHSINAH ta dago tana kalon Indo kafin cikin rudu ta ce.
"Na shuga uku Indo na manta da kudin inna dellu, billahilazi bani na daukar mata kudi ba, ki
yarda Dani Indo, ta fada hawahe na bin kuncin ta "Kinga MUHSINAH kina bani haushi wlh ai
nasan bake kika dauki kudinba baze huce dije ce ta dauki kudin ba za Azo ana kece, tafada
hankalinta kwance, Rai bace MUHSINAH ta dago tana kalonta kafin cikin dacin murya ta ce
"Indo bana so meyasa kike son batan Rai Indo? So nawa zan gaya Miki dije itadin yar uwa
tace har so nawa zan gaya Miki bani son kina jifan yar uwata da munannan kalamai, mehisa
baza taci darajata a wajanki ba a matsahinta na yayata. me yasa baza taci darajar affa ba
Indo zamu Bata dake akan yar uwarta bazan laminci batanci a gurinki ba?" Tahi GABA fuuuu
cikin bacin Rai,
Baki sake Indo ta bita da kalo mamakinta ya daskarrar da ita cikin kunci da bacin Rai ta daga
murya ta ce,
"Na gode MUHSINAH ki nunamin Banda Wani matsahin a gurinki ni na daukeki yar uwa ba
kawa ba ke kin dauke ni kawa komai nahi, nahi shine sabida ke sabida banajin Dadi in anacin
zarafinki kome nafada akan dije na fadane sabida bacin ran abinda inna dellu take Miki, shiru
tahi tana Jan dogon nuffashi kafin ta Kuma cewa. Insha Allah daga tana irin ta yau bazan
Kara da bakina a matsalarki da ta gidanku ba ko makamancin haka lefinane da nake nuna da
muwata akanki, na gode da kika fahimtar Dani"
Cakkk MUHSINAH ta tsaya daga tafiyar da take jiki a sanyahe ta juyo tana kalon Indo wadda
taho ranta a bace, Dede tazo zata huce ta gefanta tasa hannunta ta riketa, dauke hannun ido
tahi zatai gaba ta Kuma ruke ta cikin sanhin murya tana cewa "kihi hakuri Indo rainane ya
Baci bana son inji kina aibata yar uwata sabida nasan baza ta aikata hakan ba, da made yaya
babale kikace se in yadda Amma Dan Allah kihi hakuri Kuma kidena ai Bata ya dije a gabansa
kinji'?" Nuffashi Indo taja tana murmushi ta ce,
"Shikennan muje Kinga har Rana ta fara futowa muhi sauri, Kai ta daga mata suna hin gaba
tafiya sukai me Dan Sahi kafin suka shugo Dan karamin rugar Fulani me dauke da gidane
kala kala basu da Wani yawa acikin rugar Yara da masu kiyo se hucewa suke da alamu daga
kihi suka daho tafiya sukai me Dan tsahi kafin suka tsaya a kofar wata babban gida Wanda
akai rufin kofar gidan da karare se kofa shuga wadda take dauke da langa langa, tsayawa
sukai dije ta ce,
"Ki shuge gida Kinga garin da lema ga sanhi kodan cihonki, Allah ya doraki kan inna dellu ta
ce zatahi muki Wani abun ko duka, ki shuga. Murmushi MUHSINAH tahi tace
"To se anjima Indo ki cewa innarmu zan shugo da magariba na gaida ta inde Allah ya Dora
ni kan affa ya barni" to shikennan tahi gaba tana daga murya
"Ki shuga gida baruwanki da zama a wajan lema ki kula kinsan de yadda kike Shan wahala
ko?" Murmushi tahi tana bin Indo da kalo tana son Indo kamar me ta damu da damuwarta
kalon yar uwa take mata gashi in akai ruwa ta runka sa mata doka kamar mamanta
murmushi ta juya ta na tura kofar langa langar gidan............