bc

Tsintaciya

book_age18+
0
FOLLOW
1K
READ
revenge
family
HE
second chance
kickass heroine
single mother
drama
tragedy
serious
city
small town
like
intro-logo
Blurb

tsintaciya labarine na soyayya, radadi juriya kalubale da wata budurwa fulani mai suna muhsinah ta fuskanta wanda a karshe komai ya sauya mata sauyawa ta ban al ajabi da birgewa wanda ya kunshi masarauta guda biyu da wani gidan dake da kalu bale da kuma kalubalan marikiya da kuma na cuta kai yana kunshe da abubuwan al ajabi wanda se ka karanta zaka fuskanci abinda nake nufi kubiyoni danji ya ze kasance shin kuma ku tan bahi kanku wai me ze faru aciki masarautar nan guda biyu me hadinsu shin me ya hada yarinya tsintaciya da masarautu biyu wannan amsar fa kallo baze baku ita ba bibbiyata da zakuhi ne ze baku amsar tan bayohinnan

chap-preview
Free preview
CHAPTER 1
Bismillahir Rahmanir Rahim. Ya Allah, Ubangijin tsintuwa da ɓacewa, Ka sanya wannan littafi ya zama haske a cikin duhu, ya zama sako na hakuri ga wanda haushin rayuwa ya dabai, ya zama ta'aziyya ga talaka, da tunatarwa ga mai dukiya. Ya Allah, duk kalmar da ke cikinsa da taɓa zuciya, Ka sanya ta zama dalilin sauyin rayuwa mai kyau. Duk kuskuren da ke cikinsa, Ka yafe min, domin kai ne Masani, ni kuma mai neman gaskiya ne. Ya mai juya kaddara, Ka juya kaddarorinmu zuwa ga mafi alkhairi. Allahumma amin. *TSINTACIYA* by Ameena m Abdullahi Ga shimfida mai jan hankali da zaka iya sakawa a farkon littafinka *TSINTACIYA*: --- *TSINTACIYA* Akwai abubuwan da bamu nema ba, amma kaddara ta kawo mana su. Akwai kuma abubuwan da muka nema da gaske, amma har abada bamu same su ba. Wani ya tsinta dukiya a inda wani ya tsinta kaskanci. Wani ya tsinta farin ciki a cikin talauci, wani kuma ya tsinta bakin ciki a tsakiyar mulki da kwanciyar hankali. Wannan littafi ba labarin tsintuwa kawai bane. Labarin rayuwa ne. Labarin yadda hakuri yake mayar da tsakuwa lu'u-lu'u. Labarin yadda kaddara ke wasa da mutum, ta daga talaka ta sauke mai mulki. Labarin yadda sauyin rayuwa ke zuwa a daƙiƙa guda - daƙiƙar da zaka tsinta abu daya da zai sauya duk rayuwarka. *TSINTACIYA* zai koya maka cewa: Dukiya ba ta nuna darajar mutum. Talauci ba laifi bane. Kuma tausayi... tausayi shi ne dukiyar da ba ta taba faduwa. Idan ka taba jin an manta da kai, Idan ka taba jin duniya ta yi maka nauyi, Idan ka taba tsinta wani abu da ya girgiza zuciyarka... To wannan littafi naka ne. Bude shafin farko. Shiga duniyar TSINTACIYA Bismillah rahamanu Rahim wassallalahu Allah nabiyu .............. hadarine agarin yayi bakyinkyirin cikin kankanin lokaci ruwa ze iya sauka ga iska me sanhi da saukar da nutsuwa da take kadawa a hankali jejine gurin ba sosai ba se dogayan bushiyu da sukaiwa jejin kawanya, agefe guda Kuma wasu kyawawan fararan fulanin dajine ke tafiya cikin nutsuwa Amma kana ganninsu zakasan sauri suke. Bazasufi shekara 15 aduniya ba suna sanhe da kalkin saki ajikinsu Riga da zani da tukunyar kasa a hannunsu da alamu ruwane aciki, Daya daga cikinsu ce cikin harshen fulatanci ta ce "MUHSINAH muhi sauri fa Kinga hadarinnan Kara kaimi yake, in ruwa ya ruskeme bazamu komai gida da huri ba gashi ke inna dellu zata iya dukanki ni da dauki" dogon nufashi wadda aka kira taja cikin muryarta me sanhi da Dadi ta na cewa "Indo wlh saurin nake ga gajiya dake damunta, nafiki San mukima gida da huri, "Wai sauri kike a Ina kike saurin MUHSINAH? Mehisa kike haka ne kina Gani de mutannan rugarnnan kowa hi yake dake akan izza da sarauta gashi ke ba yar kowa ba ki rabu da abinda kike kiji da matsala Daya mana, tafada cikin damuwa. "hmm Indo har dake? Kinsan bahin kaina bane inaso na gyara tafiyata irin ta kowa Amma na kasa kodan hinda ake Dani ai zanso nagyara Amma Indo nakasa, tafada hawahe masu zafi da Kuma na tsiyayo mata. "Kinga MUHSINAH Allah ya huci zuciyarki ni Bada wata manufa na fada ba nafadi abinda yan rugarnnan ke fadane kawai, Amma kihi hakuri kuka banajin bane kinji'?" Tafada tana share mata hawahe, murmushi MUHSINAH tah i wadda a kullum ke Kara mata kyau ta ce "Babu koma Indo kawai yanzu muhi sauri mukima ruga Kinga an fara yayyafi, Kuma in yatabani affana ze game kokuma cihona yatashi, Kai Indo ta daga mata takama hannunta suka shuga wata yar bukka tana cewa, "Gwanda mu fake Annan don in muka huce Babu wajan tsayawa Kuma daga Gani ruwannan da gaske yake, tsayawa sukai suna kalon yadda ruwan yafara karfin ga sanhin damunta da kamshin kasa da yake tashi mesanyaya zuciya da saukar da nutsuwa, "Kinga kwa na manta ya kwa dazu kuka Karke da inna dellu, anga kudin kuwa?" Ara Zane MUHSINAH ta dago tana kalon Indo kafin cikin rudu ta ce. "Na shuga uku Indo na manta da kudin inna dellu, billahilazi bani na daukar mata kudi ba, ki yarda Dani Indo, ta fada hawahe na bin kuncin ta "Kinga MUHSINAH kina bani haushi wlh ai nasan bake kika dauki kudinba baze huce dije ce ta dauki kudin ba za Azo ana kece, tafada hankalinta kwance, Rai bace MUHSINAH ta dago tana kalonta kafin cikin dacin murya ta ce "Indo bana so meyasa kike son batan Rai Indo? So nawa zan gaya Miki dije itadin yar uwa tace har so nawa zan gaya Miki bani son kina jifan yar uwata da munannan kalamai, mehisa baza taci darajata a wajanki ba a matsahinta na yayata. me yasa baza taci darajar affa ba Indo zamu Bata dake akan yar uwarta bazan laminci batanci a gurinki ba?" Tahi GABA fuuuu cikin bacin Rai, Baki sake Indo ta bita da kalo mamakinta ya daskarrar da ita cikin kunci da bacin Rai ta daga murya ta ce, "Na gode MUHSINAH ki nunamin Banda Wani matsahin a gurinki ni na daukeki yar uwa ba kawa ba ke kin dauke ni kawa komai nahi, nahi shine sabida ke sabida banajin Dadi in anacin zarafinki kome nafada akan dije na fadane sabida bacin ran abinda inna dellu take Miki, shiru tahi tana Jan dogon nuffashi kafin ta Kuma cewa. Insha Allah daga tana irin ta yau bazan Kara da bakina a matsalarki da ta gidanku ba ko makamancin haka lefinane da nake nuna da muwata akanki, na gode da kika fahimtar Dani" Cakkk MUHSINAH ta tsaya daga tafiyar da take jiki a sanyahe ta juyo tana kalon Indo wadda taho ranta a bace, Dede tazo zata huce ta gefanta tasa hannunta ta riketa, dauke hannun ido tahi zatai gaba ta Kuma ruke ta cikin sanhin murya tana cewa "kihi hakuri Indo rainane ya Baci bana son inji kina aibata yar uwata sabida nasan baza ta aikata hakan ba, da made yaya babale kikace se in yadda Amma Dan Allah kihi hakuri Kuma kidena ai Bata ya dije a gabansa kinji'?" Nuffashi Indo taja tana murmushi ta ce, "Shikennan muje Kinga har Rana ta fara futowa muhi sauri, Kai ta daga mata suna hin gaba tafiya sukai me Dan Sahi kafin suka shugo Dan karamin rugar Fulani me dauke da gidane kala kala basu da Wani yawa acikin rugar Yara da masu kiyo se hucewa suke da alamu daga kihi suka daho tafiya sukai me Dan tsahi kafin suka tsaya a kofar wata babban gida Wanda akai rufin kofar gidan da karare se kofa shuga wadda take dauke da langa langa, tsayawa sukai dije ta ce, "Ki shuge gida Kinga garin da lema ga sanhi kodan cihonki, Allah ya doraki kan inna dellu ta ce zatahi muki Wani abun ko duka, ki shuga. Murmushi MUHSINAH tahi tace "To se anjima Indo ki cewa innarmu zan shugo da magariba na gaida ta inde Allah ya Dora ni kan affa ya barni" to shikennan tahi gaba tana daga murya "Ki shuga gida baruwanki da zama a wajan lema ki kula kinsan de yadda kike Shan wahala ko?" Murmushi tahi tana bin Indo da kalo tana son Indo kamar me ta damu da damuwarta kalon yar uwa take mata gashi in akai ruwa ta runka sa mata doka kamar mamanta murmushi ta juya ta na tura kofar langa langar gidan............

editor-pick
Dreame-Editor's pick

bc

Dominating the Dominatrix

read
57.6K
bc

The Billionaire’s Accidental Baby

read
3.2K
bc

The Luna He Rejected (Extended version)

read
646.9K
bc

The Heiress's Choice

read
15.0K
bc

HIS FATHER'S LUNA

read
6.5K
bc

“Daddy, Will You Ever Love Me?”

read
16.8K
bc

Divorced At Eighteen

read
65.1K

Scan code to download app

download_iosApp Store
google icon
Google Play
Facebook