bc

WA ZAI FUSKANCE NI??

book_age18+
0
FOLLOW
1K
READ
revenge
family
opposites attract
heir/heiress
drama
tragedy
sweet
serious
campus
small town
like
intro-logo
Blurb

soyayya ta rufe mata ido, Farin ciki kawai take hangowa, Bata tunanin abin da zai faru da ita a gaba.ta yadda dashi ta bashi amana , sai dai ta rasa shi a dai dai lokacin da take tsananin bukatar shi.sun Gaza fahimtar ta, sun Yanke mata hukunci cikin fushi.WA ZAI FUSKANCE NI??

chap-preview
Free preview
Chapter 1
‎⚠️ GARGADI ‎Wannan labari ƙirƙirarre ne, ba labarin wani mutum na zahiri ba. Duk wani abu da mai karatu zai ga ya yi kama da abin da ya shafi rayuwarsa ko ta wani da ya sani, to wannan tsantsar arashi ne kawai. Don Allah a yi haƙuri, a ɗauke shi a matsayin wani ɓangare na labarin. ‎ ‎⚠️ HAƘƘIN MARUBUCIYA ‎Ban yarda wata ko wani ya kwafi, ya juya, ya sake wallafa, ko ya sauya wannan littafi ta kowace hanya ba tare da amincewata ba. ‎A mutunta haƙƙin marubuciya da aikin da aka rubuta cikin lokaci, ƙoƙari da tunani. ‎© Umma Mustapha - An haramta kwafi ko sake wallafa wannan aiki ba tare da izini ba. ‎WA ZAI FUSKANCE NI?? ‎BOOK 1 ‎Umma Mustapha ‎@umsar Arewapen Wattpad: Umma Mustapha ‎PAGE 1 ‎Bismillāhir-Raḥmānir-Raḥīm. ‎A cikin Jami'ar Sule Lamido da ke Jihar Jigawa, wasu 'yan mata guda biyu, waɗanda shekarunsu ba su wuce ashirin da huɗu zuwa ashirin da biyar ba, suna zaune a cikin babban ɗakin karatu na jami'ar. ‎Dukansu sanye suke da dogayen rigunan abaya. Ɗaya ta saka baƙar abaya, ɗayar kuma purple. ‎A gabansu akwai littattafan karatu da takardu iri-iri, alamar cewa suna shirin jarabawar da ake gab da fara musu. ‎Cikin library ɗin kuwa ya yi wani irin shiru. Kowa da ka gani yana zaune ne, kansa sunkuye kan littafinsa. Ba ka jin komai sai ƙarar AC da kuma sawun security da suke yawo a hankali, suna sa ido kan ɗaliban da suka zo karatu. ‎Sai dai ɗaya daga cikin 'yan matan, wadda ake kira NIHLA, ba ta cikin halin karatu ko kaɗan. ‎Kanta a kan desk take, idanunta a lumshe, kamar wadda barci ya ɗauke ta. ‎Fatima, wadda take zaune kusa da ita, ta ɗan ɗaga kai. Ta hango Daya daga cikin security yana tahowa wajensu, nan take ta miƙa hannu ta zunguri Nihla, tana mata alamar ta tashi. ‎A hankali Nihla ta ɗago manyan idanunta waɗanda suka yi ja, ta zubawa Fatima su. ‎"Menene?" ‎Fatima ta yi ƙasa da murya, tare da nuna mata security da ya taho. ‎"Security." ‎Nihla ta bi inda take nunawa da ido. Sai ta ja tsaki. ‎Ba tare da ta ce komai ba, ta sake kifa kanta a kan desk. ‎Fatima ta girgiza kai, sannan ta koma kan littafinta. ‎A haka security ya iso ya tsaya a gabansu. Ya ɗan bubbuga desk ɗin da Nihla take kwance a kai. ‎Amma Nihla ko motsi ba ta yi ba. ‎Sai ya juya ya kalli Fatima, ya yi mata alamar tambaya da hannu. ‎"Me ke damunta?" ‎Fatima ta ɗan yi murmushi, sannan ta amsa cikin ƙasa da murya: ‎"Kanta ne yake mata ciwo." ‎Jami'in tsaron ya fahimci abin da take nufi. Ya ɗan girgiza kai sannan ya wuce, tare da Yi mata fatan samun lafiya. ‎Fatima ta sake kallon Nihla. ‎Kusan kwana uku kenan yanayinta ya sauya. ‎Nihla da ta sani a baya ba haka take ba. ‎Duk da kasancewarta mai son shiru da kuma ɗan miskilanci, ba ta wasa da karatunta. Idan lokacin karatu ya yi, ba ta son wani abu ya raba mata hankali. ‎Amma yanzu... ‎Kamar akwai wani abu da ya mamaye zuciyarta, ya kwace mata nutsuwa da farin cikin da aka san ta da shi. ‎Ta rame. Idanunta sun yi zuru-zuru, kamar wadda ta shafe watanni tana jinya. ‎Karatunta kuwa ta ajiye shi gefe, duk da cewa jarabawarsu ta kusa. ‎Wannan jarabawar tana daga cikin jarabawarsu ta ƙarshe, domin suna semester ƙarshe na Level 4. ‎Fatima tana tsoron kada Nihla ta samu matsala a wannan semester ɗin. ‎Abin da ya fi damunta kuwa shi ne, ba ta san abin da yake damun ƙawarta ba. ‎Ta tambayeta sau da dama, amma Nihla kullum amsarta guda ɗaya ce: ‎"Babu komai." ‎Amma Fatima ta san akwai wani abu. ‎Akwai wani abu mai girma da ƙawarta take ɓoye mata. ‎Ba ta san mene ne ba. ‎Fitima ta duba agogon hannunta taga karfe Daya da rabbi, Dan haka tacewa NIHLA ta tashi suje suyi sallah. ‎Suka fice daga library ɗin suka nufi toilet domin su kama ruwa su yi alwala. ‎Bayan sun fito, kai tsaye suka nufi masallacin mata da ke cikin jami'ar domin gabatar da sallar Azahar. ‎Bayan sun idar da sallah, Nihla ta samu wuri a gefe ta zauna, ta jingina da bango. ‎Wayarta tana hannunta. ‎Ta buɗe wani saƙo da ta aika, ta sake dubawa. ‎Har yanzu babu amsa. ‎Ta sake duba wayar kamar tana tsammanin wata sabuwar sanarwa za ta bayyana. ‎Babu komai, shiru. ‎A wannan lokacin wayar Fatima ta yi ƙara. ‎Kira ne yake shigowa. ‎Ta ɗauki wayar ta kara a kunnenta. ‎"Okay, ina zuwa." ‎Shi ne kawai abin da ta furta kafin ta kashe wayar. ‎Ta kalli Nihla. ‎"Bari na je na dawo. Zan karɓo material na karatu." ‎Ta ɗan dakata kafin ta ƙara da cewa: ‎"Ki jira ni." ‎Nihla ba ta ce komai ba. Kai kawai ta ɗaga mata. ‎Fatima ta fice daga masallacin. ‎Ita kuwa Nihla ta zame ta kwanta a wurin, ta lumshe idanunta. ‎A lokacin ne duk tunanin da take ƙoƙarin gujewa ya sake dawo mata. ‎Tunanin mutum ɗaya. ‎IRFAN. ‎A hankali ta buɗe idanunta, ta kalli wayar da ke hannunta. ‎Tambayar da har yanzu ta gaza samun amsarta ta sake dawowa mata: ‎"Ina IRFAN ya shiga?" ‎Kwana uku kenan. ‎Kwana uku ba ta san inda yake ba. ‎Ta kira wayarsa sau da dama, amma amsar da take samu guda ɗaya ce: ‎Wayar a kashe take. ‎Tun ranar da ya ɓace daga ganinta take ta buga wayarsa, amma ko sau ɗaya ba ta shiga . ‎Ta aika masa da saƙonni. ‎Babu reply. ‎Ta duba duk wani social media da ta san yana amfani da shi. ‎Babu shi. ‎Babu wata alama. ‎Kamar ƙasa ta haɗiye shi. ‎Irfan ba irin mutumin da zai yi haka ba ne. ‎Ba shi ne mutumin da zai ɓace na kwana uku ba tare da ya gaya mata komai ba. ‎Babu abin da yake rabasu sai lecture. ‎Wata rana idan ba shi da lecture, yana raka ta nata lecture. ‎Tun ranar da ta haɗu da shi, ba ta taɓa yin dogon lokaci ba tare da ta gan shi ba. ‎Amma yau... ‎Ba awa uku ba ake magana ba. ‎Kwana uku ne. ‎Kwana uku babu Irfan. ‎Babu muryarsa. ‎Babu saƙonsa. ‎Babu labarinsa. ‎Duk inda ta san za ta iya samun wani bayani a kansa, ta duba. ‎Amma babu shi. ‎Tunaninta da basirarta duk sun ƙare wajen neman mafita. ‎Ta rasa abin da za ta yi. ‎Ta kuma rasa wanda za ta tunkara da wannan matsalar. ‎Babban fatanta kawai shi ne ya kasance cikin ƙoshin lafiya, duk inda yake. ‎Ta lumshe idanunta, tana addu'a a cikin zuciyarta. ‎"Ya Allah, ka sa yana lafiya. Duk inda yake, ka tsare shi. Ka dawo min da shi cikin ƙoshin lafiya. Allah ka sa ba wani mummunan abu ne ya same shi ba." ‎Wannan addu'ar ita ce take ta maimaitawa tun ranar da abin ya faru. ‎Amma wata ƙaramar murya a cikin zuciyarta ta ƙi barin ta samu nutsuwa. ‎Idan yana lafiya, me ya sa ya ɓace haka? ‎Zuciyarta ta ƙara tsinkewa da tsoro. ‎Ta rasa wa za ta faɗawa damuwarta. ‎A haka Fatima ta dawo ta same ta. ‎Ta jima a tsaye tana kallonta, amma Nihla ba ta san cewa ta dawo ba. ‎"NIHLA..." ‎Shiru. ‎Fatima ta sake kiranta. ‎"NIHLA!" ‎A hankali ta buɗe idanunta, ta ɗago kai ta kalli Fatima. ‎Fatima ta zauna kusa da ita. ‎"Me ke damunki?" ‎Nihla ta sauke ajiyar zuciya. ‎"Babu komai, Fatima." ‎Fatima ta kalleta na ɗan lokaci. ‎Ta san ƙawarta tana ɓoye mata wani abu. ‎"Babu komai?" ta maimaita. ‎Nihla ta kau da kai. ‎Ba ta ba ta amsa ba. ‎Ita yanzu damuwarta guda ɗaya ce. ‎Wa za ta tunkara da matsalar? ‎Jabir. ‎Wata zuciyar ta ba ta amsa. ‎Amma nan take ta tuna cewa shi ma Jabir ɗin baya nan. ‎Ya tafi gida tun satin da ya gabata saboda bikin ƙanwarsa, kuma har yanzu bai dawo ba. ‎Dole ta nemi Jabir, domin tana son ta sanar da shi matsalar da take ciki. ‎Jabir shi ne kawai abokin Irfan kuma amininsa da ta sani sosai. ‎Zata iya kiran sa ta waya. ‎Ko kuma ta jira dawowarsa. ‎Yau Alhamis ne. Ta san dole cikin ƙarshen makon da za a shiga zai dawo. ‎Amma fa... ‎Idan Irfan bai dawo ba fa? ‎Yau an yi kwana uku. ‎Idan ta ƙara da kwanakin da za ta jira Jabir ya dawo, za a doshi kwana biyar ko shida kenan. ‎Anya bai kamata ta je Police Station ta kai rahoto ba? ‎Amma a matsayinta na me zata je? ‎Idan suka tambayeta: ‎"Menene alaƙarki da shi?" ‎Wace amsa za ta ba su? ‎Saurayi? ‎Ko kuma... ‎Mijinta? ‎Idan suka tambayi iyayensa ko 'yan uwansa, me za ta gaya musu? ‎Ba ta da wata mafita. ‎Dole ta jira dawowar Jabir. ‎"Ya Hayyu, Ya Qayyum..." ‎Nihla ta faɗa a ƙasan zuciyarta. ‎"Allah ka kawo min mafita." ‎Hannunta ya sauka kan ƙasan cikinta, ta shafa wurin a hankali. ‎Wani irin tsoro ya ƙara shiga zuciyarta. ‎Tana kwance tana tufka da warwara, ta gaza samun bakin zaren da za ta kama domin ta tinkari matsalar da take gabanta. ‎A nan ne ta ji muryar Fatima ta sauka a kunnenta. ‎"Ya kamata mu yi haramar fita, tunda mun gama abin da ya kawo mu cikin school ɗin. Ina ganin mu bi ta cafeteria, mu nemi wani abu mu saka a cikinmu." ‎Nihla ta yunkura ta miƙe daga kwanciyar da ta yi. ‎Ba tare da ta ce wa Fatima komai ba, ta ɗauki wayarta da jarkarta. ‎Suka fice daga cikin masallacin. ‎A hankali suke tafiya, musamman Nihla wadda ba ta jin daɗin jikinta. ‎Ga jiri. ‎Ga kasala. ‎Ga nauyin zuciya. ‎A haka suka lallaba suka isa cafeteria, kowa da abin da yake saƙawa a zuciyarsa. ‎Bayan sun isa cafeteria, Nihla ta nemi wuri ta zauna. ‎Ita kuwa Fatima ta zarce ta saka musu order. ‎Ba ta tsaya tambayar Nihla abin da za ta ci ba, domin ko ta tambayeta, ta san amsar da za ta ba ta. ‎Don haka kawai ta je ta saka musu oder abincin da ta san Nihla tana so. ‎Bayan Fatima ta saka musu order, ta dawo ta zauna kusa da ita. ‎Suna jiran abincin. ‎Fatima tana duba wani abu a wayarta. ‎Ita kuwa Nihla tana aikin da ta saba yi tun kwana uku da suka gabata. ‎Tunanin Irfan. ‎A haka mai kawo abinci ya zo ya same su. ‎Ya ajiye musu tuwon semo da miyar agushi, tare da bushashshen kifi da naman ganda. ‎Fatima ce ta yi musu order ɗin, saboda ta san yana daga cikin abincin da Nihla take so. ‎Ya ajiye musu abincin ya tafi. ‎Fatima ta ajiye wayarta, ta janyo robar da ke gabansu ta wanke hannunta. ‎Ita ma Nihla ta wanke nata hannun. ‎Suka yi Bismillah sannan suka fara cin abinci. ‎A wannan karon Nihla ta ci abincin da ɗan yawa. ‎Ta jima rabonta da abinci tun lokacin da ta shiga cikin wannan tashin hankalin. ‎Sai yau ta samu ta ci wani abu mai ɗan nauyi. ‎Bayan sun gama cin abincin, sai Nihla ta ji cikinta ya fara juyawa. ‎Alamar amai na son taso mata. ‎Da sauri ta zura hannunta cikin jakarta, ta ciro wata ƙaramar roba mai murfi. ‎A cikin robar akwai ruwan lemon tsami. ‎Ta buɗe ta kafa a bakinta, ta sha sosai. ‎Sanna ta sauke robar tana sauke numfashi a hankali. ‎Haka take fama da wannan matsalar 'yan kwanakin nan. ‎Sai da ta samu nutsuwa sannan ta rufe robar, ta mayar da ita cikin jakarta. ‎Ta ɗago kai ta kalli Fatima. ‎Fatima kuwa ta tsare ta da idanuwa, tana neman ƙarin bayani. ‎Nihla ta kau da fuskarta kamar ba ta san abin da Fatima take son sani ba. ‎Sai ta yi saurin tambayarta: ‎"Kin kira Malam Musa ne?" ‎Murmushi Fatima ta yi, ta kawar da kanta gefe. ‎"Eh, na kira shi tun dazu. Yana bakin gate, yana jirammu." ‎Malam Musa mai Napep, babban mutum ne mai hankali. ‎Aƙalla shekarunsa za su kai arba'in da biyar. ‎IRFAN ne ya samo wa Nihla Malam Musa domin aikensa kasuwa da sauran abubuwa. ‎Kowanne wata Irfan yake biyan Malam Musa kuɗin aikinsa. ‎Akwai girmamawa da mutuntawa sosai a tsakaninsu. ‎Wannan ya sa su Nihla suke ba shi girma sosai. ‎Malam Musa mutum ne mai kirki. ‎Tun bacewar Irfan, Malam Musa ya zama shi ne ke kai Nihla da ƙawarta Fatima makaranta, sannan ya ɗauko su. ‎Duk da cewa har yanzu babu wanda ya san abin da ya faru da Irfan. ‎Duk wanda ya tambayi Nihla game da shi, sai ta ce musu: ‎"Ya yi tafiya." ‎Hatta Fatima da ta tambayeta, wannan ce amsar da ta ba ta. ‎Haka ma lokacin da ta kira Malam Musa, ta gaya masa cewa Irfan ya yi tafiya, kuma ya ce zai ci gaba da kai su makaranta har sai ya dawo. ‎Suka miƙe suka yi haramar fita daga makaranta. ‎Da ƙafa suka taka har suka isa bakin gate ɗin jami'ar. ‎Makarantar ta sanya dokar hana masu Achaba da Napep shiga cikin makaranta. Sai dai su tsaya a bakin gate. ‎A bakin gate ɗin suka iske Malam Musa yana jiransu. ‎Yana faman goge Napep ɗinsa da duster. ‎Ba laifi, Malam Musa akwai tsafta sosai. ‎Sai da suka ɗan jira ya gama goge-gogen nasa, sannan suka shiga Napep ɗin suka tafi. ‎Malam Musa ya sauke su a ƙofar Hostel ɗin Asma'u Sa'id, da ke kan titin jami'ar. ‎Kafin ya juya ya tafi, ya tambaye su ko akwai wani aiki da zai musu. ‎Ya bayyana musu cewa akwai wani uzuri da ya taso masa. ‎Nihla ta girgiza kai. ‎"Ba komai, Malam Musa. Ka iya tafiya, ka je ka yi uzurinka." ‎Malam Musa ya amsa da godiya, sannan ya juya ya tafi. ‎Su kuma suka gangara suka nufi cikin hostel ɗin, ba tare da Nihla ta iya cire tunanin Irfan daga zuciyarta ba. ‎Da suka shiga cikin ɗakin, Nihla ta cire kayanta ta nufi banɗaki domin yin wanka saboda gajiyar da ta kwaso. ‎Ita kuwa Fatima ta fara gyara musu ɗakin, domin ba su samu damar gyarawa ba kafin su fita. ‎Bayan Nihla ta yi wanka, ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi wadda take jin daɗin sakawa. ‎Ta zauna a bakin gadon. ‎Bayan ɗan lokaci sai ta kalli Fatima. ‎"Fatima, ina son na koma gida yau. Na gaji da zaman hostel ɗin nan naku." ‎Fatima ta dakatar da abin da take yi, ta juyo ta kalli Nihla. ‎"Me ya sa kike son tafiya? Saboda me? Ba haka kika ce min sai Irfan ya dawo za ki koma gida?" ‎Fatima ta faɗa tana kallon Nihla. ‎Nihla ta sauke ajiyar zuciya. ‎"Fatima, a takure nake a hostel ɗin nan wallahi. Bana jin daɗinsa ko kaɗan. Surutun wannan roommate ɗin naki ma shi kaɗai ya ishi mutum. Sannan..." ‎Ta ɗan yi shiru kafin ta ƙara: ‎"Anan hayaniya ba ta barin mutum ya samu ko ɗan karatun dare ya yi." ‎Fatima ta yi shiru na ɗan lokaci tana kallon Nihla. ‎Sai ta girgiza kai. ‎"Ke dai ki faɗi gaskiya. Kawai kina kewar masoyinki ne, shi ya sa kike son ki koma." ‎Nihla ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta girgiza kai. ‎"Ba wai saboda Irfan zan koma gida ba. Na dai gaji ne da wannan hostel ɗin." ‎Fatima ta yi murmushi kaɗan. ‎"Hmm... Allah ya kyauta. Ni dai na san akwai wani abu da ba ki faɗa min ba." ‎Nihla ta kalleta da sauri. ‎"Fatima!" ‎"Na'am?" ‎"Don Allah kar ki fara." ‎Fatima ta yi dariya. ‎"To shikenan, ba zan fara ba." ‎Sai Fatima ta ƙara da cewa: ‎"Ki bari sai wajen ƙarfe shida na yamma sai ki tafi, kafin Nan rana ta yi sanyi." ‎Da wannan Fatima ta miƙe, ta ɗauki kayan wankanta, sannan ta nufi banɗaki. ‎Ita kuwa Nihla ta zauna shiru a bakin gadon. ‎Idanunta suka sauka kan wayarta. ‎Ta ɗauke ta a hankali. ‎Ta sake buɗe sakonnin da ta aika wa Irfan. ‎Har yanzu babu amsa. ‎Ta lumshe idanunta. ‎A cikin zuciyarta kuwa tambaya guda ɗaya ce kawai take ta maimaituwa: ‎Ina Irfan yake? ‎Kuma mafi girman tambayar da take tsoron amsarta ita ce- ‎ME YA SA YA ƁACE??????

editor-pick
Dreame-Editor's pick

bc

The Luna He Rejected (Extended version)

read
646.8K
bc

The Heiress's Choice

read
14.5K
bc

Dominating the Dominatrix

read
57.6K
bc

The Billionaire’s Accidental Baby

read
3.2K
bc

HIS FATHER'S LUNA

read
6.5K
bc

“Daddy, Will You Ever Love Me?”

read
16.7K
bc

Divorced At Eighteen

read
65.1K

Scan code to download app

download_iosApp Store
google icon
Google Play
Facebook