CHAPTER 9

2698 Words
“Haihuwa maganin mutuwa, ba don ke ba da iri ya ƙare!" Wannan shi ne kirarin da ake wa haihuwa. Kuma sukan ƙara da cewa, “Kyan gida da magaji!” kirarin haihuwa kirari ne na ƙaruwa. Ma’anar haihuwa ita ce, yayin da miji da mata suka sami ƙaruwa ta samun ɗa ko ‘ya. Ma somin haihuwa kuwa shi ne, lokacin da mace ta samu juna biyu, wato ta sami ciki, bayan an tabbatar da igiyar aure tsakaninta da mijinta. Ƙarshen haihuwa shi ne yayin da jariri ya fito daga cikin uwarsa ta hanyar al’ada. Da zarar mace ta samu ciki (juna-biyu) sai iyayenta ko masu lura da ita su duƙufa wajen neman taimako don ta sauƙa lafiya. Akan kuma kafa mata dokokin da zata kiyaye, kamar kada ta riƙa cin abinci, ko abin sha mai zaƙi, kamar zuma da sukari ko rake ko mazanƙwaila ko alawa, saboda sauƙin nauyin fitowa abin haihuwa wanda yake faruwa da ciwon zaƙi. To, kuma akan umurce ta da ta riƙa shan magani a kai a kai, kamar sabara da bauri. Da kuma wasu tadodi na mai ciki kamar rashin fita da dare ba tare da wani makami ba, kamar wuƙa ko lauje ko ɗan makoɗi ko mashinjiri ko dagi, saboda shu’umi da aljani. Anan in an ga alamar cewa haihuwa ta kusa, sai a shiga neman maganin sauƙin guiwa, kamar shan rubutu da jiƙe-jiƙe. Sai a aika a ƙirawo wata mace, wato ungozoma, don ta kula da mai haihuwa. Kuma in ta sauƙa lafiya a kula da abin da aka Haifa. Sannan ta yanke cibiya, ta binne uwa, wato mahaifa. Kuma ba za a ba da sanarwar haihuwa ba, sai in an ga faɗuwarta, kana ungozoma ta kan ce “ Alhamdulillahi, barka da arziki!” da sauran maganganu ko addu’o’i da a kan yi bayan mahaifar ta faɗi. Daga nan farin ciki ne zai mamaye uwar a lokacin da taji kukan farko na jaririnta, abu na farko da zata so tayi shine ta dauki jaririn a hannunta, ta rungumeshi kwarai a kirjinta. Sai dai ita Jinah da ta haihu ba tare wani ya sani ba ko taimakon wata ungozoma ba, sam bata ji son daukar jariran ba a hannunta, eh tagwayen da ta kawo duniya mace da namiji. Ita abinda tafi bukata a lokacin shine ta runtse ido idan ta bude taga babu yaran ace mafarki take. Na farko dai bata san yaushe, ta yaya kuma da wanene ta samu cikin ba. Sannan ga wannan mutuwar da ta konkwasawa sirikanta kofa, kuma gashi bata samu wani taimako ba lokacin da zata haihu, sannan cibiyar jariran a yanke take, to ta yaya haka zaka ta faru? Abubawan al'ajabin da suka zo suka cunkushe mata kwalwa kenan. Cikin tsoro, tasa zani ta lullube jariran, sannan ta kwanta ta juya masu baya tareda rufe ido. Ji tayi kamar mutum a kusa da ita, zuciyarta ce ta buga. Bude ido tayi, taga Sarah durkushe gabanta. Hawaye dukansu biyu suke, dan Sarah ta karanci tsantsar tashin hankali a fuskar Jinah. -Labari yaje mana kan abinda ya samu sirikanki, abun babu dadi Jinah. Ya shi Daudan ya farka? Girgiza mata kai kawai Jinah tayi. -Kar ki damu, insha Allahu zai samu lafiya. Mikewa Sarah tayi ta zauna bakin gadon, tana shafa kan Jinah, irin ta kwantar mata da hankali. -Allah mai iko, jariran waye? kamar yan... Sarah ta fada lokacin da ta lura da yan tagwayen jarirai a bayan Jinah. -Nawa ne! Jinah ta fada a takaice cikin muryar damuwa. -Sabuwar haihuwa. Me kike... a'a wannan ba zai taba yiyuwa ba. Kasa yarda Sarah tayi. -Da gaske nake Sarah! Cikin Jinah, Sarah ta kalla taga wayam, sannan ta kalli jariran, hannu ta dora a bakinta da ya kasa rufuwa tsabar mamaki, ta kasa magana. Haka ta tsaya na tsawon wani lokaci kafin tace -Tun yaushe? -Dazu.. -Ikon Allah! Ta..ta yaya ba ki.. Me yasa jariran basu yin kuka? Gaskiya yayi wuri ace kin haihu Jinah! -Na sani Sarah, na fiki shiga razanin ganin wannan al'amari, akwai ma abubuwa da dama da suka faru da na kasa fahimta, kuma nake bukatar wani yayi min bayani. -Da taimakon wa kika haihu? -Babu wanda ya taimaka min. -Ikon Allah, Jinah! Mikewa tayi, ta yaye zanin da Jinah ta lullube jariran, nan ta lura babu kaya jikinsu. Fita tayi daga dakin ta samo bokiti cike da ruwa da kuma wani bahon wanka. Daya bayan daya tayi masu wanka, Sannan ta shafesu da mai kafin ta lullubesu da zani. -Karbi ki basu mama! Sarah ta fada, tana mikawa Jinah jariran. Hannunta na rawa ta fara karbar macen. Lokacin da jaririyar ta bude bakinta, ta tura mata kan maman, da sauri Jinah ta runtse ido, sannan taja wani dogon numfashi, wani yanayi ne mai dadi ya lullubeta, bude idonta tayi, lokaci na farko da ta jita a matsayin uwa. Murmushi tayi tana shafa kumatun jaririyar. Bayan dan wani lokaci, shima namijin tayi masa kamar yanda ta yiwa macen. -Sai kuma me zan yi? Ta tambayi Sarah cikin kasalalliyar murya. -Ban sani ba Jinah, amma tabbas idan mutanen nan suka fahimci kin haihu ba kyaleki zasu yi ba. -Na sani, zasu gane cikin ba na Dauda bane. -Toh tun wuri ya kamata mu bar gidan nan. -A'a Sarah, ni zan tsaya sai nasan halin da Dauda yake ciki. Ke kije da yaran ni na biyoku a baya. -Ba zan iya daukansu duka biyun ba. Sake Jinah tayi alamar tana tunani, kafin ta mike tana niyyar fita daga dakin. -Ina zaki je? Sarah ta tambayeta. -Ina zuwa. Fita tayi sannan ta dawo da Samira 'yar yayar Dauda. Yarinya ce da ba zata wuce shekaru 13 ba, amma Jinah ta yarda da ita sosai. Fadawa yarinyar tayi cewa wannan jariran ita ta haifesu kuma bata san kowa ya sani kuma tana son ta taimakawa Sarah taje da jariran. Yarinyar bata tsaya jin wani cikakken bayani ba, ta fita ta samo amalanke, da yake lokacin babu kowa a tsakiyar, saka kowane jariri suka yi kondon jarirai, kowacce ta dauki daya a suka kama hanyar kauyen Mambila. Jinah kwantawa tayi da niyyar rage gajiyar dake jikinta, amma bacci ya kasa daukanta, wata murya taji amma wannan karon, ji tayi ance : Kiyi hakuri Jinah. Mikewa tayi ta nufi gidan mai magani dan ganin halin da Dauda yake ciki, har yanzu bai farka ba, sai da ta dauki dan lokaci kafin ta dawo gida, wanka ta shiga tayi. Tana idawa, ba'a jima ba wata yarinya ta leko tace mata tazo inji Rashida daya daga cikin kishiyoyin sirikarta. Amsa kiran tayi, ta nufi dakin Rashidar, da shigarta ta tarar da gungun mata wadanda duk yawancinsu yan uwa Dauda ne sai kuma ita Rashida. -Me kike yi a daki, ko kina tunanin abincin karin shi zai sarrafa kanshi? Cike da mamaki Jinah ta dago tana kallonta, ba wai abinda ta fada bane ya bata mamaki, a'a yanayin yanda tayi mata maganar ne. Dan wannan shine karon farko da Rashida tayi mata irin wannan maganar cikin yanayin mugunta. Wata tsohuwa dake zaune kusa da Rashida, ta taso ta zagaya Jinah sau uku kafin ta yarfa mata wasu ruwa cikin kwarya da tsintsiyar kaba. Komawa tsohuwar tayi ta zauna tareda fadawa Rashida wani abu a kunne. Zabura Rashida tayi cikin karaji tace -Daman na sani! Ba cikakkiyar mutum bace, gashi yanzu Gwamma ta tabbatar. -Itace, komai ya faru ne sanadinta, muna zaune lafiya kafin zuwanta, babu wata masifa irin wannan da ta taba konkwasa mana kofa. Wata 'yar uwar Dauda ce ke fadar haka tana nunen Jinah da yatsa. -Kwarai kuwa, ya za'a yi ace Isa ya mutu a dakinta kuma Dauda gashi cen rai a hannun Allah. Wata daga cikin yan uwan Daudan ta kara da hakan. -Wai ya aka yi kuka zama kamar makafi, baku ga yanda take kama da aljanu ba. Mayya mai cin kurwar maza. cewar wata makociyarsu. -Ina yawan ganinta a mafarki, duk lokacin da naso fada sai wani abu ya tokare min makoshi. Cewar wata yar uwan Dauda. -Rannan a tsakiyar dare na ganta tana magana da karnuka... Girgiza kai Jinah take ko ta farka, dan ita a tunaninta mummunan mafarki take, dan ganin abinda ya faru jiya yana sake maimatuwa yanzu, kamar ana tariyar kaset. Rufe ido tayi sannan ta bude, tsoro ya kara shigarta ganin idanun wadannan matan kanta suna kallonta cike da tsana. Bata ankara ba, taji sun rufeta da duka da yakushi. Ihu Jinah take tana kuka amma babu wata mai imani da ta sassauta mata. Jinah tana kuka tana maimata : dan Allah ku fada min me nayi maku, me yasa kuke dukana? Ita al'amarin daure mata kai yake ganin yanda take zaune da sirikanta lafiya kuma suna kaunarta amma lokaci daya sun juya mata baya gashi yanzu kokarin kasheta suke. Tunani take "Anya wannan zahiri ne kuwa ba mummunan mafarki ne nake ba?" Haka matan nan suka cigaba da jibgarta babu tausayawa, kamar daga sama taji ana cewa -Baku jin kunya ne, duk abubuwan da suka faru a gidan nan. Maza ku rabu da ita! -Innalillahi! Me kuka aikata haka? Jinah bata san ko waye ya kawo mata dauki ba, amma taji an daina dukanta. Mahaifiyar Dauda ce da yayarsa. -Gwamma ta fada mana ko wacece ita, wannan yarinyar ita ce sanadiyar duk wani tashin hankali a gidan nan, Mayya ce ita! Cewar Rashida tana nishin gajiyar dukan Jinah. Wani mugun kallo Jinah taga sirikarta ta watsa mata, wanda yasa duk gwiwowinta suka sace. Yanzu kenan tana goyon bayan wadannan matan, to me yasa? Kuma wacece wannan tsohuwar da suka yarda da abinda ta fada? -Ku kyaleta, sirikata ce ni nasan me zan yi mata. Nusaiba (wato 'yarta, yayar Dauda) taimaka min na kaita dakinta. -Mama! Cewar Jinah tana kuka, lokacin da suke su uku a dakinta. -Kada ki kara kirana da wannan sunan. Ki tattara kayanki yanzu ki bar gidan nan, kafin sauran yan kauyen su san abinda ke faruwa, kuma na hanasu dukanki ne kawai albarkacin soyayyar da dana yake maki. Mahaifiyar Dauda ta fada kafin ta juya ta fita. -Yanzu Nusaiba kin yarda da abinda suke fada a kaina? Jinah ke tambayar Nusaiba yayar Dauda. -Ban sani ba Jinah, amma Gwamma bata taba karya ba ga abinda ya shafi wannan, dan tasan mayu sosai. Shuru Jinah tayi, ta cigaba da sheshekar kukanta, dan batada abin cewa. -Bari na taimaka maki, ki hada kayanki. Cewar Nusaiba. -Amma fa wannan ba shine na farko ba da na hadu da wannan tsohuwar, me yasa bata taba cewa ni mayya ce? -Nima ban san dalili ba Jinah. Zuwa karfe goma na safe, Jinah ce zaune tare da kayanta bisa amalanke zuwa kauyen Mambila. Tayi matukar galabaita, ko'ina na jikinta ciwo yake, cikin awannin da basu fi 24 ba, abubuwa da dama sun faru wadanda tsabar rashin sanin ma'anarsu tana nema ta zauce, abinda tafi kasa ganewa yanda farat daya dangin mijinta suka sauya mata. Tunaninta komawa yayi kan mijinta da yake cen kwance rai a hannun Allah, ji tayi sam babu dadi, Addu'a tayi Allah ya tashi kafadunsa, duk da tasan sai ya kara shiga wani halin idan ya farka yaji labarin mahaifinsa ya rasu. Bayan tafiyar kamar mintuna ashirin, suka karaso gidan su Sarah. -Sannu Jinah, labari ya riskemu, yanzu haka shirye shiryen tafiya muke, Allah ya jikansu yasa aljanna ce makomarsu. Gaskiya abin juyayi ne sosai ya samu dangin mijinki. Safiya matar Lasaini ke fadar haka kamar wacce aka jona a radio, kalamanta sai suka kara sa Jinah fashewa da kuka, kuma a lokacin idan aka tambayeta kukan me take, ita kanta bata san amsar me zata bayar ba. -Kiyi hakuri ki daina kuka Jinah, dama duk mai rai mamaci ne. Murmushi kuma safiya tayi lokaci guda. Dazun Sarah ta haihu, ta haifi kyawawan tagwaye. Wasu na tafiya, wasu na zuwa. Ikon Allah kenan. "Kenan Sarah wata karyar ta kuma yi a kaina?" Jinah ta fada cikin zuciyarta. -Ah Masha Allah! Abinda Jinah ta iya fada kenan, tareda kirkiran wani murmushin dole. -Eh, kuma babu wanda yasan tanada ciki. Ita kadai ta haihu ba tare da wani ya sani ba, gaskiya uwar rikonki jaruma ce. Lasaini na jirana zamu je jana'iza, ki wuce Sarah na ciki, yanzu muma mun dawo. Daman maganar ta fara isar Jinah, suna yin sallama tayi saurin karasawa dakin Sarah. Sarah ganin Jinah ta tabbatar ba lafiya ba dan duk fuskar Jinah ta kumbure. -Me ya faru Jinah? -Dukana suka yi Sarah, sannan suka yi min sharrin maita kafin su koreni daga gidan. -Allah sai ya saka maki, bani labarin abinda ya faru. Jinah labarin duk abinda ya faru taba Sarah daga lokacin da ta barota, sai dai kamar ita Sarah ma bata fahimci komai ba. Taimaka mata tayi ta kwanta, zuwa dare ta dauko man zaitun ta tattausa mata jikin, ba abinda Jinah keyi bayan kukan wahala. -Allah sai ya saka maki Jinah, kuma insha Allah aniyarsu sai ta bisu. Sarah ke fada tana kwalla, dan abin yayi matukar bata mata rai. Da taimakon tausar da Sarah tayi mata, Jinah ta samu yin bacci sai dai kafin nan sai da taji muryar nan ta rada mata : "Nagode da zama uwar 'ya'yana". Da yamma, Jinah da Sarah suna zaune a daki suna fira, suka ji ana bubbuga kofa, Yayan Sarah ne Lasaini, shigowa yayi yace Jinah ta basu wuri zai yi magana da Sarah. Fita Jinah tayi zuwa tsakar gida, inda taga mutanen gidan kowa sai yi mata irin kallon da dangin mijinta suka rinka yi mata. Tsoro ya kamata, ba tare da tace uffan ba ta jawo banci ta zauna bakin kofar dakin. Cikin dakin kuwa, rigima ce ta kaure tsakanin Sarah da yayanta Lasaini. -Ni babu ruwana da abinda wadannan mutanen suka fada maka, kawai sharri suke mata. -Ke da kanki kin sani, yanayinta yayi kama da na aljanu, dole a ce mayya ce. -Na fada maka mutum ce kamar mu. Lasaini, ka tuna da Tanti Amina, cousin din Mamarmu? -Eh na tunata! -Ba mutane sharrin maita suka lakaba mata ba. Amma ni da kai da Mama mun san ba mayya bace. Korarta aka yi daga kauye kamar karya. Kuma kai kasan daga baya abinda ya faru... Jikin Lasaini yayi sanyi yace -Eh kashe kanta tayi. -To kuma shine kake son haka ta sake faruwa ga Jinata? Wannan ba mai yiyuwa bane, ba wanda zan bari ya taba min Jinah, mutane mugaye ne Lasaini. -Kinada gaskiya, kiyi hakuri. Nan Lasaini ya lallashi kanwarsa tareda tambayar lafiyar yan tagwayen da yake tunanin 'ya'yanta ne. Bayan sati daya, aka yi bikin yan tagwaye, aka sa ma macen suna AYA shi kuma namijin AYYU KANTE. Jinah ce ta zabi sunayen sai dai ita kanta bata san dalili ba. Kawai abinda ta sani KANTE sunan mahaifin Kimba ne mijin Sarah. Wani abin mamaki ga tagwayen girma suke yi da sauri, har wani lokaci cikin raha Sarah sai tace: "Lallai wannan diyanki, suma akwai abubuwan al'ajabi a tare dasu kamar ke." Jinah tana cikin farin cikin kasancewarta uwar wadannan yan tagwaye, wani lokacin idan ta kallesu sai taga kamar tasan fuskokin a baya. Sosai suke tuna mata wani, wanda ta kasa gane waye. Matsala daya da har yanzu take fuskanta har yanzu a kauyen wasu kallon mayya suke mata, tana shan tsagwama sosai. Ganin haka Sarah ta shirya barin kauyen ita da Jinah da kuma tagwayen ba tare da taso rabuwa dan uwanta ba da kuma dan yaro Bukari, dan ba zata iya jure ganin halin da Jinah take shiga ba a kauyen. A wata safiyar Lahadi, suka dauki hanya zuwa gidan Sarah wato gidan mijinta Kimba. Basu kai gidan ba sai tsakiyar dare, amma da zuwansu sai suka tarar da alamun mutane a gidan. Ba zai wuce Kimba ne mijinta ba, amma kuma ba shi daya bane. Zuciyar Sarah ce ta buga, tunawa da tayi yace mata kar ta yarda ya rigata dawowa. ------------------------------------------------------ Assalamu alaikum, fatan kun sha ruwa lafiya readers? I'm sorry much, na jinkirin yin update na wannan labari. Sai kuna yi kuna hakuri dan rubutu akwai wahala bare ga sabon shiga. Kuma nasan a wannan chapter akwai wurare da dama, da sai mutum yayi da kyar ya fahimta. But everybody be cool! Sai mun hadu a wata chapter insha Allah ? @El_Ashtar
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD