PROLOGUE
Motsi take ji, takun sawun kafafu na kara tinkaro inda take, a jikinta tana jin ko meye ke nufota zai cutar da ita ne. Amma ta yaya zata iya guduwa, ta yaya zata iya guduwa domin ta buya? Alhali ba zata iya ba, domin sai da kafafuwa ake gudu, ita kuwa bata da su. Abinda kawai take iya yi shine tayi rarrafe. Ai kuwa bata yi wata wata ba ta fara rarrafawa iya karfinta, duk da haka ba zata iya kubuta daga wannan mutumin da tuni ya nufo gurinta yana tangadi. Namiji kakkausa mai girma, jiki ne ya fara yi mata rawan tsoro koda ta hada ido dashi. Kallonta yayi tare da yin wani shu'umin murmushi, ita kuwa ganin hakan ma ya kara mata tsoro, kara kusanto ta yayi tare da durkusawa daidai kafafunta. Murya na mata rawa ta tambayeshi "Me kake so dani?" Ba tare da bata amsa ba ya kara kokarin riketa ita kuwa da sauri ta kara ja baya daga zaune bisa mazaunanta. Kara yunkurawa yayi ya rikota tareda fincike mataccen zanin dake jikinta. Tayi ta kokarin ta kwaci kanta, amma hakan ya faskara domin akwai banbancin karfi tsakanin su. Wani masifaffen wari ne ke fita daga jikinshi, warin giya ne, alamar yasha ya bugu ne. Cikin muryar kuka da ban tausayi take rokon wannan mutumi "Dan Allah kayi hakuri ka kyaleni! baka ganin yanda nake? Mumuna kuma gurguwa? Kayi hakuri ka kyaleni kar kara min wata najasar!"
"Ke kike ganin wannan a jikin ki, dan abinda nazo nema wajenki bayada wata nasaba da kazantarki ko gurguntarki." Kalmomin da kawai suka fito daga bakinshi, ya cigaba da abinda ya kawoshi. Bai rabu da ita ba har sai da yaga ya samu biyan bukatarshi, yayi mata fyade.
Sunanta Hauwa, ita kadai ke rayuwa cikin bukkarta nesa da wani kauye mai suna Kumana dake a wata kusurwa a kasar Nijar, kauye ne da kowane gida yake rayuwa cikin farin ciki amma banda ita, kauye ne da kowane makoci yake zaune lafiya da makocinsa amma banda ita. Sanadin munin da take da shi ga kuma kasancewarta musaka na rashin kafafuwa duka biyu yasa mutanen garin suka koreta a cewar su Mayya ce. Ta kasance ita daya ke da irin wannan halittar a kauyen, ita kanta ba zata iya tuna ina mahaifanta suke ba, kawai ta tsinci kanta korarriya kamar kare daga wannan kauye tun tana yar karamarta.
Bayan ya gama abinda yake so, ya fito ya barta a sume yayi tafiyarshi ba tare da ya waiwaya ba balle ya duba ko tana raye. Bayan wasu awanni Hauwa ta farka, matsanancin ciwon da zugin da tsakanin cinyoyinta ke mata yasa ta fashe da kuka mai tausayi, gashi babu wani da zai kawo mata dauki, ba dangin kusa balle na nesa.
BAYAN WATA TARA (9)
Wannan rana ta banbanta da sauran ranakun, Hauwa tana jin wani abu, tana jin wani abu da itama ba zata ce ga asalin abinda take ji ba. Ta tashi ne tana jinta cikin wani farin ciki, komai lafiya lau. Katon cikin dake jikinta ta shafa, jin alamar yanda dan cikin nata ke motsawa yasa ta saki murmushi. Sanadin wannan fyaden da wannan mutumi yayi mata watanni 9 da suka wuce yasa ta samu ciki,duk da ba wai kamar kowane da bane, shi ga sanadin yanda ta sameshi amma tana cikin farin ciki, ko ba komai yanzu tasan ba ita daya bace tanada mai debe mata kewa, wanda take samu tayi fira dashi duk da tasan ko dan cikin nata na jinta ba zai iya amsa mata ba. Tana jin dan cikin nata har cikin ranta, domin shine haske yanzu a gareta.
Fitowa tayi da rarrafe ta nufi cikin dajin domin samo abinda zata saka ma cikinta. Bayan taje ta samu 'ya'yan itatuwa da suka fado kasa taci ta koshi, komawa tayi gindin bishiyar wani mangoro dan ta dan huta kafin ta juya zuwa gida. Bacci ne mai nauyi ya dauketa har dare yayi, sheshekar kuka ne ya tayar da ita. Inda take jin sautin kukan ta nufa tana yi tana buya. Wata matashiyar mata ta gani sanye da zallan fararen tufafi ta gani a durkushe a kasa. Kasa dauke idanunta tayi daga kan wannan mata, don wannan shine karin farko da taga irin wannan halitta. Ta raya a zuciyarta "dan mutum ba zai iya samun irin wannan kyau ba haka, gaskiya wanann Matar tanada masifar kyau." Kasada ta dauka na karasawa kusa da matar tare da tambayarta "Baiwar Allah lafiya kike kuka?"
Cikin sheshekar kuka ta bata amsa "Yarona... yarona mutuwa zai yi idan ban bashi Yattaba ba, ganyen shuka da shine zai iya warwakar dashi!"
Cikin tausawa Hauwa tace "Ayyah, ai kuwa akwaishi a cikin killatacciyar fadamar kauyen nan." Matar tace "Ai ba yanda zan yi na shiga fadamar domin ni Aljana ce." Gaban Hauwa ne yayi wani mumunan faduwa, tsoro ya mamayeta, cikin ziciyarta take cewa : Na shiga uku ni Hauwa, yau kuma na taro abinda yafi karfina, aljanu wadannan dai masu karfin sihiri da shan kwalwar mutum, yau gani ga daya daga ciki. Me zan yi yanzu? Idan nace zan gudu, rarrafe nake kafin nayi wani yunkuri zata kamani. Ganin yanda jikin Hauwa ke mazari aljanar ta fahimci ta tsorata ne "Kar ki damu ba zan cutar dake ba, zaki iya tafiyarki ki kyaleni na cigaba da kukan mutuwar dake tunkaro yarona (Dana)." Hauwa juyawa tayi, tayi tafiyarta sedai ba gidanta ta nufa ba, wannan fadamar mai tsaro ta kauyen ta nufa, guri da dan Adam ne kawai zai iya shiga gurin, Idan har aljani yayi kuskuren shiga wurin to fa ba zai fito da rai ba, dan fadama ce da mutanen garin suka gada daga kakanin su mai cike da tsaro na tsafi.
Hauwa tana son ta taimaki wannan aljana, dan ita daya ce ta taba yi mata magana ba tare da ta nuna mata kyama ba. Cikin sanda da kulawa Hauwa tayi nasarar debo ganyen. Cikin kuka mai hade da farin ciki aljanar take ma Hauwa godiya, ta amshi ganyen da dan gudunta dan taba danta.
Lokaci na farko da Hauwa ta fara jin wani mummunan ciwon ciki ya turnuketa, da alama lokacin ne yayi, Haihuwa. Har awanni masu yawa suka shude Hauwa na cikin wannan hali, har lokacin da aljanar ta tardota.
"Na zo ne in maki godiya, ta dalilinki dana ya samu lafiya, ki fada min duk abinda zan yi maki ni kuma zan yi ma..." Tsayawa tayi da maganarta sakamakon ankara da tayi da halin Hauwa take ciki.
"Wayyo.. ci..kina, da alama ya..ro..na ne ke zuwa...!
Aljanar ta fahimci haihuwa ce zata yi, anan ta fara kokarin taimaka mata, bayan wani lokaci kadan ta haife 'yarta mace.
Aljanar ta rike 'yar tana murmushi tare da sanar da Hauwa abinda ta haifa. Murmushi da hawayen farin ciki ne suka kwacema Hauwa. Wuka aljanar tasa ta yanke cibiyar yarinyar sannan ta nadeta da zani.
"Ina rokonki da ki kular min da 'ya ki rike min ita,ki kawatata da kyau kamar naki, bana son ta wulakanta kamar yanda na wulakanta, ina son ki saka mata suna JINAH, ma'ana aljana da yaren mu..."
Sai yanzu aljanar ta fahimci kalar kalamin da Hauwa take, alama ce ta mutumin da karshensa yazo, domin bata karasa fadin abinda take son cewa ba rai yayi halinsa.
Aljanar daukar yar jinjirar mai suna Jinah tayi zuwa gidanta, kafin daga bisani taje ta bizne gawar Hauwa.
"Daga ina kike da dan Adam? Kinsan hadarin da ke tattare da kawota nan da kika yi?" Cewar mijin aljanar bayan ganin Jinah da yayi. "Yar matar nan ce da ta ceci dan mu, bayan ta haifeta ne ta mutu kuma ta bani amanar 'yarta ne kuma na dauka." "Amma kin sani sarai cewa,sauran dangin mu (Aljanu) ba zasu karbi dan Adam ba a cikin mu, kuma zamu fuskanci babban hukunci idan suka gano hakan." Sanin mijinta nada gaskiya yasa bata kara cewa komai ba, dan tasan ta riga da ta dauki alkawari kuma dolenta ta cikashi. Tuna alkawarin zata mayar mata da 'ya kyakyawa yazo mata, sedai tuni Jinah mai kyau ce dan tsabar kyau itama kamar aljanu take.
Jinah girma take yi a hankali a cikin wadannan halittu (aljanu), sedai ta ganin tsana a gun sauran aljanu, duk da su marikanta suna kaunarta sosai, suna jinta tamkar 'yar cikin su, kuma suna kareta daga dukkan wani sharrin aljani da yake son cutar da ita, tana samun kulawa haka daga wajen dan uwanta (dan marikanta wanda mahaifiyarta ta ceta) mai suna Fally, Fally yana matukar son Jinah dan a kullum sai yayi fada da yan uwanshi aljanu idan suka ce zasu taba Jinah. Son da yake nuna ma Jinah yayi tsananin da har iyayensa sun sanar dashi illar yin hakan, dan babu aure tsakanin dan Adam da aljani, kuma hukunci mai tsanani ga duk wanda yayi kokarin taka wannan doka a duniyar aljanu, amma ina shi Fally bai san wannan ba dan tuni har yaga Jinah ta zama matarshi, kuma itama haka sosai take sonshi.
Wata rana Fally ya dauki Jinah zuwa wani kebataccen guri wanda wannan guri ya kasance anan aljanu wanda suka kasance masoya, suke alkawarin zama tare na har abada a tsakanin su. A lokacin Fally na da shekaru 18 ita kuma Jinah na da 16.
"Jinah kin shirya zama dani, zama dani har abada?" cewar Fally rike da hannuwan Jinah suna masu kallon Juna.
"Sosai ma, ina kaunarka kuma zan kasance koda yaushe a tare da kai." Ta bashi amsa cikin farin ciki
Wata yar karamar wuka Fally ya dauko tareda yanka babban yatsanshi, itama haka Jinah tayi, sannnan suka hada yankakkakun yatsun nasu gu daya inda jinin nasu ya garwaya. Bayan sunyi hakan sannan Fally ya dauko wata kwarya mai dauke da wasu koren ruwa, ya fara sha sannan ya ba Jinah itama tasha.
Jinah cire zanin dake daure kugunta tayi, sannan ta kara cire wanda yake daure a kirjinta. Kwantawa tayi akan wani jan kyalle dake shinfide a gurin babu komai a jikinta. Shima Fally dama wani gajeren wando kadai a jikinshi ya fiddashi, sannan ya zuba wasu ruwa a jikin Jinah, bayan wani dan lokaci sai ga wani maciji ya bayanna a hannunshi, sakin wannan maciji yayi yanata bin jikin Jinah, uta kuwa ko a jikinta, dan ta san wannan yana daga cikin siddabarun alkawarin nasu, kuma daman ta iya sarrafa dabbobi kamar sauran aljanu, kuma kasancewar kyawun dake gareta irin na aljanu yasa tana iya yin wasu abubuwa sosai wanda cikakken dan mutum ba zai iya ba.
Macijin ya bace bayan wasu yan lokuta. Bayan wannan, cikin farin ciki Fally suka raya wannan rana kamar kowanne ango da amarya. Hakan zai nuna sun dau alkawarin zama na har abada a tare.
Waje kuwa, sama tayi mugun baki, wanda hakan na nuna ba alkhairi a yau, eh babu alkhairi don saduwar mutum da aljani baya haifar da abu mai kyau. Lokacin da suka zo tafiya gida, Jinah da Fally sun lura da canjawar yanayi na garin, su kuwa ko a jikin su dan yau ta kasance masu ranar farin cikin da ba zasu taba mantawa da ita.
Fally daukan Jinah yayi suka nufi gida, tin daga nesa suke jiyo kukan Mahaifiyar Fally wato uwar rikon Jinah. Fally aje Jinah yayi suka nufi dakin mahaifiyar tasu. Mahaifiyar karasowa tayi wajen Fally kafin ta sakar masa wani masifaffen mari. Dafe kunci Fally yayi kafin ya dago ya kalli mahaifiyarsa cike da mamaki.
"Mama me ya faru? me nayi kika mareni?" Fally ya tambayi mahaifiyar tashi cike da mamaki. "Me ya faru mama?" Ita ma Jinah ta kara jefo ma uwar cikin mamaki.
"Baku ga yanda sama tayi bane? Ko baku ji kukan dabbobi bane? Ku a ganin ku lafiya a wannan lokacin mahaifin ku baya gida?" Kallon Juna Jinah da Fally suka yi dan su har yanzu basu fahimci komai ba.
"Ke Jinah tun tuni na fada maki, mahaifiyarki ta mutu, kuma mutum ce, kuma kema mutum ce, mu kuwa jinsin aljanu ne. Kuma akwai banbanci tsakanin duniyat mu da taku, wanda dole watara zaki nemi ki zama uwa, ki yi aure ki haihu, kuma hakan zai faru ne kawai idan kin auri mutum dan uwanki. Sai da na fada maki kar ki kuskura wata alaka ta hadaki da aljani!"
Yanda mahaifiyar take magana zaka fahimci ranta yayi matukar baci.
"Ni..Ni.." cike da i'ina Jinah ta fara kokarin ta kare kanta amma sai ta sunkuyar da saboda kunya.
"Mama kinsan muna son junan mu kuma..."
"Kai kuma ka rufa min baki, ai komai ma laifin ka ne! idan ba sakarci ba me ya kaika yin alkawari da ita? To ku sani abinda kuka yi babu wanda bai samu labari ba, dan yanzu haka mahiafin ku yaje amsa kira. Dama dangi sun jima suna son su ga bayan Jinah, yanzu kuwa ta sanadin abinda kuka yi kun basu hujjah kwararra da zasu batar da Jinah. Gashi bansan me zasu yi maku ba..."
Tsoro ne fal ya cika fuskokin matasan, dan Jinah har ta fara zubar da kwalla. Fally ne ya riko hannunta dan tabbatar mata da ba abinda zai samun su.
A take mahaifiyarsu ta fara hada kayan Jinah, dan bata son wani abu ya samu Jinah saboda ba zata yafe ma kanta ba, na rashin cika alkawarin da ta daukar ma mahaifiyar Jinah. Kuka Jinah ta fara, rabuwa da wadanda take tunanin sun zamar mata yan uwa abu ne mai ciwo garesu, mafi ciwo ma shine a rabata da abin kaunarta Fally.
Wanda tun tasowarta shine abokin rayuwarta kuma dan uwanta. Gashi yanzu har sun yi alkawarin zama na har abada a tare.
Shi kuwa Fally ya fada duniyar tunani, dan hankalinshi ya guje, ya kasa gane abinda ya kamata yayi. Kukan da yaci karfin Jinah ne ya dawo dashi hankalinsa, rungumeta yayi sosai sannan ya rada mata a kunne
"Ina sonki Jinah, ina makk son da ba zan iya rabuwa da ke ba, son da ba zan iya samun madadinki ba. Zasu rabamu amma na maki alkawarin zan samo mana hanyar da zamu zauna har abada. Mun riga mun yi alkawarin zama na har abada. Kada ki taba mantawa da hakan Jinah, Ke tawa ce, kuma tawa ni kadai!"
"Eh ni taka ce Fally, taka ta har abada."
"Ki min alkawarin ba zaki taba mantawa da ni ba."
"Nayi maka alkawari ba zan manta da kai ba, koda kuwa na so haka..."
Mahaifiyar su ce ta rabasu, da sauri ta finciki Jinah tayi sama da ita. Fally yayi kokarin ya bisu amma mahaifinsa da ke shigowa yayi sauri rikoshi.
"Ya kamata ka barta ta tafi Fally, idan ba haka ba zasu kasheta. Yanzu kaje ka dakatar da alkawarin da kuka kafin awanni 24 abun ba zai yi kyau ba."
Shiru Fally yayi bai ba mahaifin nashi amsa ba. Mahaifin ya dafashi yace "Kana jina Fally kayi sauri kaje yanzu!"
Juyawa yayi ya tafi, mahaifin nashi na tunanin ya tafi ya dakatar da alkawarin nasu ne. Sai dai shi a zuciyarshi ya kudura Jinah tashi ce har abada ba zai taba rabuwa da ita ba, alkawarin da yayi mata kenan kuma yasan itama ba zata taba mantawa dashi ba. Kuma dole ya nemota duk inda mahaifiyarsa ta kaita. To me zai sa yaje ya dakatar da alkawarin nasu?
Inaaa! wani masifaffen ihu ya saki wanda yayi sanadin tarwatsewar manyan itacen dake kusa dashi.
A bangaren su Jinah kuwa, wani nauyayyen bacci ne aljanar ta saka Jinah, Nisa sosai tayi da Jinah kafin ta kawota bakin wani kauye. Wani siddabaru ta yiwa Jinah wanda zata manta da duk wata rayuwarta ta baya, wadda tayi da aljanu, ta cirewa Jinah duk wani karfi dake gareta na iya sarrafa wasu abubuwa kamar yanda aljanu suke yi, har karfin dake ga Jinah na ganin aljanu shima ta cire mata, wanda indai ba shi aljani yaso Jinah ta ganshi ba.
Jinah ya dawo kamar kowanne mutum, kuma ko ba komai zata koma tayi rayuwa a cikin yan uwanta bil'adama. Jinah ta manta da Fally, ta manta da alkawarin da suka yi, ta manta da ita matar aljani ce.