CHAPTER 1

2915 Words
Cigaban labari Sanyanyar iska ce mai dadi ke kadawa, Bishiyu ne ke rangaji daga dama zuwa hagu. Tsintsaye sai shawagi suke a sama, ga kukan dabobbi iri iri sai tashi yake a wannan jeji. Wannan yanayin ne ya kara dada wa baccin da Jinah ke yi dadi. Baccinta take cikin kwanciyar hankali bisa babbar bishiyar kuka. Haka ta cigaba da bacci har lokacin da surutun da ake yi mata a kunne ya tasheta. - Jinah! Jinah! Wani karamin yaro ne ke maimaita hakan da alama so yake ya tasheta. -humm... cikin muryar bacci Jinah ke amsawa -Ki tashi Tanti Sarah na kiran ki (Tanti na nufin kanwar uwa ko ta uba, ko matar uba a Nijar wanda haka ya samo asali daga yaren French kamar dai yanda wasu ke cewa Aunty da yaren English). Ba tare da Jinah ta amsa mashi ba ta sauko daga kan bishiyar, tare da janyo babban zanin da ta shinfida bisa reshen bishiyar, sannan ta rufe duka jikinta dashi har da fuskarta. -Tanti Jinah me yasa kike bacci kan bishiya? Baki tsoron wani abu ya sameki a wannan daren? Mama tana yawan ce mana akwai hadari zuwa cikin jeji da dare. Tsoron mutane kike yasa baki magana gaban su? Me yasa kike boye fuskarki...? Tambayoyin da yaron ke ta aiko mata ne ba kakkautawa. Da sauri ta dakatar dashi : -Dan Allah ka yi mana shiru, kai bakin ka ko gajiya baya yi irin wanann Tambayoyi haka! -To kiyi hakuri na dena... Bata tankashi ba, suka dauki hanyar zuwa gida, Gida ne wanda aka yi da bulo da siminti, hakan ke nuna mai gidan yanada dan abin hannu, dan sauran gidajen duk na kara ne a kauyen, Gidan Lasaini shi ne taken da ake yiwa gidan. Jinah ba wanda ta sani a gidan da kauyen bayan matar da ta kawota, sai kuma wannan yaron mai suna Bukari wanda shima tasu tazo daya ne sakamakon wayonshi da kuma shegen surutu dake gareshi. Lokacin da suka karaso gidan, shigewa daki Jinah tayi ta fada akan gado, kamar kullum yau ma shiru take ba magana. Tanti Sarah ce ta shigo dakin tare da yiwa Bukari da ya fita da gudu godiya. -Sannu Jinah, zaki ci wani abu? ko na kai maki ruwan wanka ne? Duk wadannan Tambayoyi da Tanti Sarah ta yiwa Jinah, Jinah girgiza mata kai kawai tayi. -Jinah! Wai sai yaushe zaki fara yimin magana, yaushe zaki fada min abinda ke damunki? Tun lokacin da na fara ganin a cikin jeji, kika ce min na taimaka maki baki iya tuna komai da dalilin da ya kawo ki cikin jejin, kawai abinda kike iya tunawa sunanki ne, tun daga ranar baki kara bude baki kin yi min magana ba, bakya magana da kowa idan ba Bukari ba. Ki je jeji kiyi kwanciyarki idan kika dawo sai ki shige daki ki ki fitowa. Yau tsawon wata daya kenan da na kawoki gidan dan uwana, amma babu wanda ya taba ganin fuskarki idan ba ni da Bukari ba. Na yiwa kowa karya akan ke diyar kawata ce ta bani rikonki.. Ki yimin magana Jinah! Ki fada min damuwarki? Kar ki sa nayi nadamar taimakonki da nayi. Ni ina daukan ki ne tamkar kanwata, kuma hakan na mani ciwo ganin halin da kike ciki. Cikin Sanyanyar murya Sarah ke fadawa Jinah haka. Jinah ta fahimci Sarah tana son tayi mata magana ne. Kuma tasan wannan matar ta cancanci ta sanar da ita duk wata damuwarta. Tasowa Jinah tayi daga inda take tareda durkusawa a gaban Sarah, kafin tace -Kiyi hakuri Sarah, ba wai nayi hakan bane, don in bata maki rai ko rashin yarda ba, abin yana min ciwo ne na rashin tuna rayuwata ta baya, ina jin kewar wasu mutanen da na kasa gane su waye, ina jin nan ba a muhallina nake ba, ina jin kamar wannan shi ne karon farko da nake rayuwa a cikin mutane kamar ku, Na kasa fahimta, na kasa fahimta Sarah. Ina son na san ta yaya hakan ta kasance, wata kil 'yan uwana basa sona ne suka jefar dani, kin fa sameni ne da kayana a cikin jaka da kuma makuden kudade a ciki, wata kil kuma guduwa ce nayi, ba zan... Kuka ne yaci karfinta, tabbas da alama tana jin abun sosai a ranta, sai dai ba yanda zata yi. -Na fahimce ki Jinah, wannan yanayi ne mai rikitarwa, shi yasa ni da ke muka kasa fahimtar komai. Amma ki ragewa kanki damuwa kar ki haifarwa da kanki wani ciwo. Ke yarinya ce, kuma akwai rayuwa mai tsawo a gabanki.Ya kamata ki fita kiyi abokai, ki sake sabuwar rayuwa kafin ki tuna komai, domin ta yiwu zai dau lokaci kafin ki tuna rayuwarki ta baya. Fadawa Jinah tayi jikin Sarah tare da fashewa da wani sabon kukan. -Ki bar kukan haka yanzu, tashi kiyi wanka sannan ki zo ki ci abincin ki. -Nayi wanka tin dazu... Jinah tayi mata karya tare da sunkuyar da kai -Oh na tuna ashe baki yin wanka sai tsakiyan dare kowa yayi bacci, me yasa kike tsoron mutane su ganki? -Kafin na hadu dake, duk wanda na gani na nufeshi da niyyar ya taimaka min sai ya gudu. Shi yasa nace wata kila akwai wani abu ne a fuskata da yake ba mutane tsoro, ko kuma kawai munina ne ke tsorata mutane. Ku kadai ne ke da Bukari baku ranci na kare ba ranar da kuka fara ganina. Abin da Jinah ta fada ne yasa dariya ta kwacewa Sarah. -Allah Sarah da gaske nake, mutumin da na fara gani, rokona yayi tayi akan dan Allah kar in cutar dashi in kyaleshi, ai kuwa ina bashi hanya ya fece kamar mashi. Dariya Sarah take tace -Ni kaina na so guduwa lokacin da na fara ganinki. Cikin mamaki Jinah ta kalleta tace -Me yasa? Hannu Sarah ta dora akan fuskar Jinah tana shafawa tace -Jinah, kina da wani masifaffen kyau ne, fuskarki har wani sheki take, ki duba ko ina a jikinki daidai ga gashin ki har ya wuce mazaunan ki. Gaskiya kyanki ba irin na mutane bane, sai dai ko na aljanu. Idan mutum ya fara ganinki dole yayi tunanin ke ba mutum ba ce, dan ko ni ban taba ganin mutum mai irin wannan kyau ba. Cikin jin dadi Jinah tace -Allah da gaske kike? -Da gaske nake Jinah, ki bari duk randa kika je bakin kogi ki duba fuskanki a ruwa zaki gani. -Kenan babu wani dalili da zan boye kaina? -A'a, zo bari in gabatar da ke ga mutanen gidan nan ba tare da kin boye fuskarki ba, daman sun sha tambayata wai don me yasa kike boye fuskarki. Kama hannun Jinah tayi suka fita zuwa tsakar gida, inda kowa sai aikin gaban sa yake. Ganin Jinah yasa kowa ya tsaya da abinda yake, suka zura mata na mujiya. Ganin haka Sarah ta katse shirun da cewa -Sunanta Jinah, itace yar kawata da ta bani riko. Wurin shiru yayi, mutanen gidan na bin Jinah da kallon tsoro. Sarah ta kara katse shirun da fahimtar dasu cewa Jinah mutum ce kamar su, kuma tana boye fuskarta ne dan ganin yanda mutane ke yawan kallonta da jin tsoronta. Ajiyar zuciyoyi ne ke tashi a wajen, wasu da yawa tsoron su ya rage, amma wasu har yanzu suna ganin wannan kyau na Jinah yayi yawa. Wasu kuwa tasowa suka yi suna ta taba jikin Jinah, wasu kuma na shafa dogon gashinta suna al'ajabin wannan abu. Ganin Jinah duk ta tsargu yasa Sarah ta janyeta. Rungume Sarah Jinah tayi tana hawayen farin ciki, domin Sarah tanada kirki, gashi dai basu hada komai da Jinah ba amma ta dauketa tamkar wata yar uwarta. Tin daga ranar komai ya koma daidai tsakanin Jinah da Sarah, suka koma tamkar wasu shakikan kawaye, duk da Sarah zata fi Jinah da kusan fiye da shekaru 10, domin Jinah tana shirin shiga shekara ta 17 ne ita kuma Sarah tanada shekaru 33. Kauye kowa ya dauka ana ta yadawa cewa ai gidan Lasaini akwai wata kyakyawar yarinya mai kama da aljanu. Mutane na ta tururuwar zuwa ganin Jinah, hakan ya dauki lokaci sosai, har ta kai idan Jinah ta fito a hanya mutane na kallonta har suna nunanta suna cewa ita ce mai kama da aljanu, har ya kai Jinah na tsarguwa da abinda suke mata. Shi yasa koda yaushe tafi son taje cen cikin jeji tayi ta wasa da dabbobi, kuma tafi jin dadin kwanciya kan reshen bishiya da kwanciya kan gado. Sai dai yanzu bata boye fuskarta kuma tana magana da mutane. 'Yan matan kauyen da dama kishi da ita suke, ganin samarin su nata rawar kafa gunta wasu har zuwa tambayar aurenta suke. Ita kuma Jinah ko a jikinta don wannan bai ma gabanta. Sarah ta fahimci hakan har wata rana take tambayar Jinah -Me yasa baki kula samarin dake zuwa wajenki? -Kawai haka nan, naji bana da ra'ayin soyayyar ne. Jinah tace a takaice. -Jinah ya kamata ace kina kulasu, dan idan da ta nice ba zan bari ki ma fara ba, domin aure shine babban kuskuren da na taba yi a Rayuwata. Amma sanin aure shine darajar kowacce mace, yasa nake son ki fidda gwani a cikin masu neman aurenki. Cike da mamaki Jinah ta kalleta tace -Amma me yasa? Ina mijinki yake? Sai yanzu wannan tunanin yazo min dan tinda nazo gidan nan ban taba ganin mijinki ba... Sarah ta katseta da cewa -Ke nifa kar ki sauya mana magana, ya maganar da muke yi amma ke kina so ki canja zancen ki kamo wani babi. Bansan daga inda kike ba amma mu nan a kauyen Mambila muna aurar da yarinya ne da wuri... Ita ma Jinah katseta tayi da cewa -Kece dai kike son canja maganar! Ita ma ta kara musawa -A'a ke dai kika canja maganar! Musu ne ya barke a tsakanin su kafin daga bisani Sarah tace -To shikenan wata rana zan fada maki. Jinah tace -Me zai hana ki fada yanzu? Sarah tace -Ke dai nace ba yanzu ba... Mikewa Jinah tayi tana kakkabe zaninta tace -To shikenan, ni dai na tafi cikin jeji. Tabe baki Sarah tayi tace -Aikin kenan! Cikin shagwaba Jinah tace -Ina jin dadin zaman ne a cen, kuma ko ba komai ina kallon yanda dabbobi ke kai kawo... Kara tabe baki Sarah tayi tace -Ina guje maki kar ki je wani aljani ya ganki, ya makale maki, kin ga sai ki dawo gida ki zauna. Fita Jinah tayi daga gidan tana dariyar maganar Sarah. Tana isa cikin jejin, kamar kullum bishiyar da take hawa tayi kwanciyarta ta dale, cikin zurfin tunani ta fada, tunani take ko zata iya tuna wani abu na rayuwarta ta baya, kamar kullum dai tana jin kewar wasu mutane da ta kasa gane su waye, tafi jin kewar wani wanda tana tunanin nata ne na kusa da ita sosai, da ta fara irin wanann sai zuciyarta ta rinka bugawa da sauri da sauri. Tana cikin wannan tunanin ne taji wata murya tana cewa -Ni fa ba zan koma gida yanzu ba, kawai kuyi tafiyar ku! Lekawan da Jinah zata yi sai ta ga wasu samari su uku ne a kasan bishiyar da take kwance. Daya daga cikin samarin ne yace -Ka dakata da taurin kan nan naka Dauda, dare fa ne ke shirin yi, kuma kaga nan jeji ne bamu san me yake dauke dashi ba na cutarwa. Dayan saurayin kuma yace -Musa fa na da gaskiya Dauda, bamu san meke akwai na hadari ba anan... Dayan saurayin mai suna Dauda wanda yake ta yiwa yan uwan nashi taurin kan ba zai koma gida yanzu ba, ya katseshi da cewa -Ku rabu da ni kuyi tafiyar ku! ku wane irin masu naci tsiya ne? na fada maku ni ba yanzu zan koma gida ba, ta yaya zamu fito farauta ko fara bamu kama ba, sannan mu koma gida haka hannu rabbana? Kuna tunanin wani abu zai same ni ne? Ai bansan cewa abokaina matsorata ne ba. -To mu kaga tafiyar mu zaka iya tsayawa, ruwanka ne wannan. Muje Mahadi idan ya gaji ya iskemu gida. Tafiya suka yi suka barshi anan, shi kuwa ko a jikinsa. Duk abinda ke faruwa Jinah na saman bishiya tana kallon su. Wata dabara ce ta fado mata, tace bari na koyama wannan dan rainin wayon hankali. Shi kuwa Dauda zaunawa yayi karkashin bishiya ya dauko Kwari da bakanshi yana gyarawa. Koda ya ida tashi yayi wai da niyyar kama wata kurciya da ya gani. Cikin Sanda Jinah ta bishi a baya ba tare da ya sani ba, boye fuskarta tayi da gashinta sannan ta dira gaban Dauda, Dauda kamewa yayi guri daya ya kasa motsi, ita kuma Jinah ta kara nufoshi... Ganin haka Dauda ya fara kyarmar tsoro yana cewa -Dan Al..lah ki..yi hakuri ki kya..leni kar ki cutar dani... Mamata zata damu sosai idan na mutu, nine dan autanta. Kiyi min rai! Dariya ta so kwacewa Jinah, kamar ba shi bane yake ta cika baki dazun. Dauda kokarin guduwa yayi ai kuwa sai ga maciji kuma gabanshi, kasa motsi yayi ya fasa ihu -Wayyo Allah! yau lokacina ne yayi!! wayyo!! Taku daya Jinah tayi gaban macijin, ta durkusa tana kallon macijin cikin ido, koda macijin ya hada ido da ita sululu ya juya ya koma daga inda ya fito. Duk wannan dramar da ake yi Dauda yana tsaye a kame yana kallon ikon Allah, dan yau ya tabbata tashi ta kare. Jinah kasa rike dariyarta tayi, ai kuwa tayi ta dariya har ta gaji dan kanta ta dena, amma har yanzu Dauda ko motsi shi kawai gani yake tashi ta kare. Jinah ta matso kusa dashi tana mai dauke gashin da ke kan fuskarta tace -Ni ba aljana bace, mutum ce kamar ka. Har yanzu shiru Dauda yayi yana kallon ikon Allah. Jinah ta kara cewa -Kamar ba kai bane kake ta kurari dazu ba, wai duk ina jarumtar taka? Kallo dai kawai Dauda ke bin Jinah dashi. Abin ya fara ba Jinah haushi tace -Tsaya da yimin wannan kallon, na fada maka nima mutum ce! Ajiyar zuciya Dauda ya sauke tare da cewa -Na kasa yarda ne... Jinah tace mashi cikin zolaya -To kayi hakuri da tsoratar da kai da nayi, kawai ina son na gwada jarumtar ka ce, ganin yanda kake ta cika ma abokanka baki dazun. Juyawa tayi da niyyar tafiya. Dauda ya dan dawo cikin hayyacinsa, tsoronshi ya ragu. Cikin zuciyarsa yace "Kuma da ita Aljana ce ba yanda za'a yi ta ceceni a hannun wannan macijin, kuma ba yanda za'a yi ta kyaleni tayi tafiyarta." Tsayawa yayi yana kallon Jinah da tayi nisa, yana kallon irin halittar da Allah yayi mata kamar wata aljana. Kuma da ya tuna yanda tayi ta kori macijin nan sai ya kasa yarda cewa ita mutum ce. Dauda bai san lokacin da ya fara bin Jinah a baya ba, lokacin da Jinah ta fahimci ana binta a baya, tsayawa tayi ta juyo ta kalleshi tace -To kuma yanzu me kake so? Ka dakata da bina. -Nima..nima bansan me yasa nake binki ba, kawai dai ina son nayi maki godiya akan cetona da kika yi, kuma ina son nasan sunanki... A tsawace Jinah tace -Wannan kuma ba zai yiwu ba, maganar godiya kuma ni nayi haka ne dan nishadi, shikenan zaka iya tafiya. Juyawa tayi da sauri da niyyar tafiya, tuntube tayi ta fadi kasa, da gudu Dauda ya nufeta da niyyar taimaka mata -Sannu ba kiji ciwo ba? Kwalla a idonta tace -Wayyo Allah zafi! Anan Dauda yaga ya kara tabbatar ma kanshi lallai wannan mutum ce kuma akwai kurciya a tattare da ita. Lokacin da yazo da niyyar tabata, da sauri Jinah taja baya dan bata so ya tabata. Kuma me yasa zata yi haka alhali taimakonta zai yi? itama kanta bata san dalili ba. Dauda ya dan ji ba dadi yace -Kawai ina son ganin inda kika ji ciwo ne. Da sauri Jinah tace -A'a kar ka tabani! Dauda bai tsaya saurarenta ba ya kama kafar tata, dole ta kyaleshi, kaya ce yaga ta taka a kafarta ta hagu. Jin laushin kafarta da Dauda yaji yace -Masha Allah, gaskiya kinada fata mai laushi da dadin tabawa... oh yi hakuri. Kafarta kawai Dauda ya taba yana wannan sambatun ina ga... Wata bishiya Jinah ta nuna mashi tace ya debo kunnuwanta, dan ta canja maganar, dan ta fara lura dan saurayin ya fara fita hayyacinshi. Dauda yace -s**t, barni nayi aikina, ba abinda zaki nuna min dan nima haihuwar kauye ne. Cikin shagwaba Jinah tace -To kayi a hankali. Murmushi Dauda yayi yace -Kinga shi yasa raina mutane baida kyau, ki duba yanda kika nemi kasheni da tsoro kema gashi yanzu Allah ya saka min. Kallonsa Jinah tayi tace -Kana nufin dan na tsorata ka ne yasa naji ciwo? Dauda ya kara yin murmushi yace -Ni dai ban ce ba.. Turo baki Jinah tayi a shagwabe tace -Haka kake nufi ba gashi da bakinka kake fadi ba.. Fashewa da dariya Dauda yayi, kafin daga bisani wajen yayi shiru. Ciro ganyen bishiyar Dauda yayi sannan ya nika ganyen da taimakon wasu duwatsu biyu sannan ya saka dadai inda Jinah ta taka kayar. Keta zaninta tayi kadan ta bashi ya daure mata ciwon. Kamata Dauda yayi da niyyar taimaka mata ta mike, wani zafi ne yaji ya sauka a jikinsa kamar an kunna masa wuta. Ihu Dauda ya fasa kafin ya fadi sumamme ko matacce. --------------------------- To Fans ku biyo mu domin jin abin da zai faru da Dauda sanadin taba Jinah da yayi. ---------------------------
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD