CHAPTER 2
Mambila, cikin wannan kauyen mai nisa a kasar Nijar, duk da rana ta fadi, dare yayi, hakan bai hana farin wata haska kauyen ba. Kowane mutum a kauyen ya aje aikin da yake yi ya nufi gidanshi don an ce dare Mahutar bawa. Saidai ba haka yake ba a bangaren Jinah dake durkushe tsakiyar jeji da mutum kwance baya motsi, kamar babu rai a jikinsa. Tsoro da firgici ne kwance a fuskarta, haka ta cigaba da kokarin tasheshi, amma shiru kake ji kamar an shuka dusa. Cikin kuka take fadin
-Dan Allah ka tashi, bawan Allah nasan baka mutu ba.
Kuka Jinah ta cigaba da yi, wata kakkausar murya taji ana cewa
-Idan har kika cigaba da tabashi, to ba zai taba tashi ba!
A tsorace Jinah take ta dube dube dan ganin mai magana amma bata ga kowa ba, tunani tayi wata kila kunnuwanta ne ke zaginta. Cigaba tayi da jijiga Dauda, amma ba alamar zai motsa, tsoronta ne ya karu. Ganin hakan ba zai fisheta ba, ta tashi a guje ta nufi hanyar gida domin nemo agaji.
-Sarah! Sarah! Sarah!
Jinah take fada, da alama har ta fara fita hayyacinta. Kusan karo suka yi da Sarah.
A tsorace Sarah tace
-Me ya faru kike wannan uban gudun da yimin irin wannan kiran?
Jinah na haki tace tana kama hannun Sarah
-Sarah zo ki gani, yaki tashi! Zo ki gani dan Allah!
-Kwantar da hankalin ki, kar ki tashe da mutanen gidan, fada mani me ke faruwa?
-Fa..du..wa ya..yi, faduwa yayi kasa, na tasheshi, na tasheshi amma yaki tashi. Sarah ina gudun ya mutu, wayyo Allah na...
-Muje ki nuna min inda yake.
Jinah kaita tayi inda Dauda yake, har yanzu dai yana nan kwance kamar gawa. Karasawa Sarah tayi kusa dashi, tana shirin tabashi suka jiwo ana cewa
-Me kuke a nan?
Lasaini ne, dan uwan Sarah.
Karasowa yayi yana fadin
-Me ya faru?
Ganin mutum a kwance kusa da su. Bai jira jin amsar su ba, ya sunkuci Dauda a kafadarshi, ya nufi gida dashi. bai dire dashi ko'ina ba sai bisa gado, sannan yace a samo masa ruwa. Jinah a guje taje ta debo ruwan, ta kawo masa. Zuba masa ruwan yayi a fuska amma shuru bai farka ba.
-Ya mutu ko?
Jinah tace zuciyarta na bugawa.
-A'a yana numfashi.
Lasaini ya bata amsa.
-To me yasa bai farka ba, gashi kuma ko motsi baya yi.
-Ki kwantar da hankalinki Jinah Cewar Sarah.
Wani mari Lasaini ya gaura masa, sai suka ga ya motsa. Ajiyar zuciyoyi Sarah da Jinah suka yi. A hankali Dauda ya bude idonshi yana binsu da kallo, kafin ya tambaya a ina yake.
Basu bashi amsa ba, Lasaini ya tambayeshi
-Kai dan wane kauye ne?
Dafe kai Dauda yayi kafin yace
-Ni dan kauyen NA GAMA ne!
-Ko zaka iya tuna abinda ya faru da kai?
Daga idanu yayi ya kalli inda Jinah take, sannan yace
-Gamo nayi da aljana ta rikida zuwa mutum ko kuma mutum ce ban sani ba...
Sarah ce tayi dariya, kafin su hada ido da Lasaini ta gimtse dariyarta.
-Zaka kwana anan kafin safiya, tinda yanzu dare ya riga yayi.
Cewar Lasaini kafin ya mike tareda cewa su Sarah su ma su je su kwanta.
Sarah ce ta juyo tareda kiran dan uwan nata
-Lasaini!
A fusace ya juyo yace
-Ya aka yi ne!
Sunne kai Sarah tayi cikin i'ina tace
-ah daman... daman.. so nake.. ba komai ma sai da safe.
Tsaki yaja bai kara bi ta kanta ba, yayi gaba. Kwalla ne suka zubo mata, ta rasa sai yaushe tsakaninta da dan uwanta zai daidaita. Tana fata watara ya yafe mata, su koma kamar yanda suke da.
Kama hannunta Jinah tayi ba tare da tace mata wani abu ba, suka wuce daki.
Suna shiga dakin kowace ta nufi makwancinta, Sai dai bacci ya kasa daukansu.
Jinah ce ta sauko daga nata gadon tana fuskantar Sarah tace
-Sarah, kin san dalilin da yasa yayi kamar ya mutu? Alhali bai san abinda ya faru dashi ba, kawai fasa ihu ne fa yayi ya fadi. Daman ana irin wannan ciwon ko kuwa?
Sarah ta kalleta tace
-Ba wani ciwo a yanda yace ya ganki, yayi tunanin aljana ce ba dole ya tsorata ya suma ba. Ai yayi kokari ma da bai hade zuciya ba tsabar tsoro.
Dariya dukansu suka yi, kafin Jinah tace
-Tinda baki jin bacci, ki bani labarin ki, da abinda ke tsakanin ki da dan uwanki, naga baku cika magana ba, kuma na lura duk lokacin da zai yi maki magana fuskarsa a daure take. Dazun ma naga haka, kece babba ko shi ne?
Ajiyar zuciya Sarah tayi kafin tace
-Yayana ne, shekara daya ce a tsakanin mu.
Tabe baki Jinah tayi, tace
-Shekara daya ya baki, shi ne ya rainaki har haka?
-Haba, ai kuwa sai na fada masa.
Zaro ido Jinah tayi tace
-Lah rufa min asiri da wasa nake, ai mutumin kirki ne.
Ganin yanda Jinah take zaro ido ya baiwa Sarah dariya.
Shuru na dan lokaci ya biyo baya, kafin Jinah tace
-To meye musabbabin abinda ya hada ku?
Shuru Sarah tayi kafin ta fara ba Jinah labarin
-Hakan ya fara faruwa ne lokacin da na fara soyayya. Ni da dan uwana mun kasance tamkar jini da hanta, kullum muna tare bama rabuwa, duk inda za'a ga keyata to ki tabbata za'a ga tashi...
Murmushi Sarah tayi tare da kwalla na tuno alakarta da dan uwanta a baya. Ta cigaba
-Na fada soyayya...
Kara matsowa Jinah tayi, cikin zumudin jin labarin soyayyar Sarah.
-Na fada soyayya ne da babban makiyin yayana mai suna Kimba. Kimba kyakyawa ne ajin farko ga kuma kudi, bai cika zama a kauyen nan ba saboda mutum ne mai yawan tafiye-tafiye. Yayana ya tsani Kimba kamar rai da ajali, lokacin da ya gane muna soyayya, sai da ya share kusan sati bai min magana kuma haka shi ne ya fara zama silar wargajewar alakarmu. Yayi kokarin ganin ya datse alakata da Kimba, amma fir na kiya, na nuna masa nifa ina son Kimba. Yana yawan fada mani, Kimba ba mutumin kirki bane, yaudarata kawai zai yi. Amma ina ni soyayya ta rufe min ido. Kimba ya turo yan uwanshi neman aurena, iyayen mu suka bashi, kowa na dangi na murna da auren mu amma banda yayana. Ana gobe daurin auren mu, da yawan samarin kauyen suka yi wata tafiya zuwa wani kauye dan nesa da mu mai suna Kumana. Hankalina bai kwanta ba dan tafiyar har da Kimba da yayana a ciki. Ina tsoron kar yayana yaje yayi wa Kimba wani abu. Saidai cikin ikon Allah suka dawo kowa lafiya lau. Sai dai Yayana yazo min da wani labari wanda shi yayi sanadin datse alakar dake tsakanin mu. Ya bani labarin cewa lokacin da suka isa kauyen Kumana, Kimba yayi shaye shaye ya bugu, ya shiga cikin jeji lokacin da ya dawo sai yaji yana ba abokinshi labari wai ya samu wata yarinya a jeji ya kore kishirwarshi, wato yayi lalata da yarinyar. Bansan lokacin da na wanke yayana da mari ba, ba zan taba manta abinda yayi ta nanata min ba "Yanzu Sarah ni zaki mara akan wannan dan iskan? To ki sani daga yau babu ke babu ni, kuma ba zan kara shiga tsakanin ki da wannan dan iskan ba!" Wadannan kalaman har yanzu suna min yawo a cikin kwakwalwa, amma ko kala ban ce masa ba dan nima a lokacin haushin sa nake ji, dan kazafin da yayi wa Kimba.
Da safe aka daura auren mu, shiru ban ga alamar yayana ba har aka daukeni zuwa gidan Kimba, tun daga ranar ban kara ganin yayana ba. A farkon auren mu, na kasance cikin farin ciki, na irin soyayyar da Kimba yake nuna min, duk abinda nake so Kimba yana yimin. Bayan wasu watanni Kimba ya nemi da na bishi garin da yake kasuwanci, hakan na damu sosai dan bana son nayi nisa da yan uwana, bare ma yayana, ina son na rinka ganinshi kullum koda kuwa baya min magana. Ba yanda zan yi dole na bishi, saboda mijina ne dole nayi masa biyayya.
Tafiya mai nisa muka yi kafin mu kai kauyen tsakiyar dare lokacin kowa yayi bacci banda wata mata wadda da alama zata fini shekaru kadan. Bayan mun aje kayan mu, matar tazo tace min naje ga ruwa cen ban daki nayi wanka. Bayan na gama, na kwanta baccin gajiya.
Hawaye ne suka zubo daga idon Sarah, shuru tayi dan ba zata iya cigaba da ba Jinah labarin ba, domin tana jin kamar yanzu ne abun yake faruwa. Rokonta Jinah tayi ta yi akan dan Allah ta cigaba. Share hawayen da suka zubo mata tayi kafin ta cigaba.
-Da safe, motsin yara ne dake wasa da kuma matan gidan da ke daka ya tayar dani, dubawa nayi gefena amma ban ga Kimba ba. Fitowata daga dakin naci karo da matar jiya da dare, bayan mun gaisa nake tambayarta ko taga mijina Kimba. Budar bakinta sai tace min wai "Ya tafi wajen daya daga cikin matansa, ni sunana Mariya nice matarsa ta biyu ke kuma kece matarsa ta biyar." Jiri naji ya fara dibana, a take maganar yayana ta fado min. Sai dai ba zan yi saurin yarda da maganar wannan matar ba. Nuna mata nayi da ban fahimci me take nufi ba. Anan take bani labarin cewa ai Kimba yanada mata da yawa da 'ya'ya a wurare daban daban, wannan ma shine karon farko da ya hade matan sa biyu waje daya. Bayan ta gama bani labari komawa nayi daki nasha kukana, shine abu mafi muni da nake ganin ya faru a Rayuwata. Ban taba tunanin Kimba zai min haka ba, dan yasha fada min "Kece matata ta farko kuma kece ta karshe." Bai taba fada min cewa yanada wasu matan ba. Kuma wani bangaren na zuciyata kasa gasgata maganar matar yayi, dole Kimba ne zai fada min gaskiyar abinda ke faruwa, haka na bar abin a zuciyata na zauna jiran dawowar Kimba. Kwanaki da yawa sun shude, babu labarin Kimba, nan na fara gasgata maganar yayana tabbas Kimba mayaudari ne. Bai tashi dawowa ba sai bayan wata daya, da zuwanshi na haushi da masifa da kuka akan ni sai ya sakeni na koma gidan mu, babu tausayi ya lakada min dan banzan duka, naci kuka da neman taimako amma babu wanda yazo ya kwaceni, saka Mariya yayi ta tattara 'ya'yanta suka tafi, bansan ina ya turata ba. Kashedi yayi min akan idan har ina son zaman lafiya to dole inyi masa biyayya. Haka dan zaman da Kimba yayi na kwana biyu ya mayar dani tamkar jaka, dukan safe daban na rana daban. Gashi ya hanani zuwa ko ganin gida, idan ya tashi zuwa wajen sauran matanshi, haka zai barni ni kadai a gida gashi babu damar naje gida, dan mu a al'adar mu idan aka yi aure ko yaji ba'a yi bare saki, da kin ga aure ya mutu to ki tabbata daya ne ya mutu ya bar daya. Haka gidan Kimba ya zame mani tamkar gidan yari...
Kuka ne yaci karfin ta, lallashinta Jinah kawai take yi, dan sosai ita ma ta tausaya mata.
Share hawaye tayi ta cigaba
-Na dauki shekaru masu yawa gidan Kimba babu wani sauyi, lokacin da ya aureni inada shekaru 18, yanzu kuma shekaruna 32. Bayan wani lokaci naji labarin matarshi ta farko a Nigeria take, kuma yafi dadewa a cen dan wani lokacin yana kwashe har shekaru 2 wajenta. Kuma yanzu cen ne zai je, ganin hakan yasa na rokeshi da ya barni naje ganin gida daga karshe ya amince amma da sharadin kafin ya dawo yana son ya tarar dani na dawo. A haka na amince akan zan zo naga dangina uwa uba yayana dan yau kimanin shekaru 5 da rasuwar Abban mu, ita kuma umman mu shekaru 3 kenan. Har lokacin yayana baya min magana, ranar da nazo, na durkusa har kasa nayi ta rokonshi akan ya yafe mani, amma ko kallon banza bai min ba. Nasan har yanzu yana sona, dan duk wata kulawa yana bani ne ta hanyar matarshi, ban rasa komai ba anan, ko ba komai ina jin dadin ganina kusa da yayana dan shi kadai ne ya rage min a dangi, gashi ban taba haihuwa ba.
A wannan karon har Jinah kuka take yi, dan Sarah ta bata tausayi ba kadan ba. Bayan sun ci kukan su sun gaji, Jinah tayi mata alkawari da zata daidaita tsakanin ta da yayan ta. Hakan yayi wa Sarah dadi kuma tana fatan haka. Ganin dare yayi nisa yasa kowace ta nemi makwancinta. Asuba ta gari!
Safiya na wayewa, Sarah ta tafi kasuwa yin cefane, ita kuma Jinah wanka ta shiga, bayan ta fito ta zauna taci abin karinta. Tana idawa ta kwanta da niyyar komawa bacci, wata murya taji na rera wasu baituka masu dadi a kunnenta. Baituka ne kamar na mutumin da yayi kewar masoyiyarsa.
Yanda Jinah ta kashe kunne, zai tabbatar maka da lallai tana jin dadin baitukan, tashi tayi ta leka ta window da niyyar ganin mai wannan dadaddiyar murya, sai dai kafin ta karasa lekawa taji sallama a bakin kofa. Amsawa tayi tareda tambayar waye.
Dauda ne ya amsa da
-Nine Dauda!
Fitowa tayi ta tarar dashi bakin kofa.
-Nazo nayi maki sai an jima, dan tafiya zan yi.
Ba tare da Jinah ta kalleshi ba tace
-To sai an jima..
Kallonta yayi yace
-Sai kuma yaushe zamu sake haduwa?
Zaro ido Jinah tayi tace
-A'ah ba da ni ba?
Dauda yace
-Saboda me?
Tace
-So kake ka mutu a hannuna? kaje kawai nagode.
Dariya Dauda yayi, abin dariya yake bashi ganin yadda Jinah ta kakkahe ita dagaske take.
-Ai ki kwantar hankalinki ni da nake fatan mu kasance na har abada..
Ya fada yana kashe mata ido.
Irin kallon sama da kasa Jinah tayi masa kafin tace
-Ban fa gane ba!
-Zaki gane nan gaba kadan, kyakyawar aljanata.
Ya fada yana murmushi tare da juyawa zai tafi, Jinah kuwa kamewa tayi kamar an shukata, tana ta juya maganar tashi dan ita sam bata fahimta ba. Tunawa tayi da dadaddiyar muryar nan da taji, da saurinta taje ta leka windon dakin amma bata ga kowa ba.
Tunani take a zuciyarta, waye wannan mai muryar, me yasa take jin wani abu a lokacin da yake rera baitukan kuma me yasa har yanzu muryarshi ke mata yawo a kwakwalwa?
Da wannan tarin tambayoyin da batada amsar su, ta nufi jeji da muryarta mai dadi tana rera daya daga cikin wakokin Umar M. Shareef.
Wa zani ba kaina? in ba ke ba a cikin yan mata
Wa zani ba raina? kece dai nake kira yar gata
Kaunar da nake miki ban yiwa kaina, kin riga kinyi rata
Kowa yazo tanka mini kan kaunarki yanzu ma fafata
In zaku yimin take, bani son wata sai ke
Ga masara ga wake, ni dai nace sai ke...