CHAPTER 3

2309 Words
Kamar yanda yake a duniyar mutane haka yake a duniyar aljanu, idan har aljani ya taka daya daga cikin dokokin al'adarsu, ana yanke masa hukunci daidai da laifinsa. Abinda ya faru ga Fally kenan, ya rasa duk wani karfi nashi da iko irin na kowanne aljani. Idan kuwa haka ta kasance ga aljani, kwanaki kadan suke rage masa a maimakon dubannin shekarun da zai yi. Aljanun da sarki ya turo sun yi nasarar cafke Fally ne, lokacin da yake kokarin bin Mahaifiyarshi da Jinah. Sanadin abinda ya aikata aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari. -Me kayi aka kawo ka wannan wajen? Cewar wani aljani da suke daki daya da Fally a gidan yarin. Ba tare da Fally ya bashi amsa ba ya cigaba da cewa -An yanke mana hukuncin daurin rai da rai ne, kuma ko ba dade ko ba jima dole zamu mutu a bayan wannan kantar, dan haka kayi amfani da sauran lokacin da ya rage ma da wannan zaman tunanin da kake... tam duk da ka ki kayi magana, kuma nasan kana ji na, bari na baka labarina da dalilin zuwana wannan waje. Na kasance daya daga cikin aljanu masu tafiye tafiye daga wannan kasa zuwa wata kasa bisa umarnin sarki. Inada mata, na kan dade ban koma gida ba, hakan yasa matata take amfani da wannan damar tana kawo kwarata gida. Nasha kamata amma bansan wane mataki zan dauka ba, har dai wata rana da na kamasu zuciya ta debeni na cire masu kai ita da kwartan nata sannan na kona gawarsu. Wannan yasa aka yanke min hukuncin daurin rai da rai. Ko a cikin aljanu ko cikin mutane, cin amana mummunan abu ne, yana iya kasancewa ga mace ko ga namiji, wannan ya zama kamar ruwan dare. Cin amanar wanda muke so yanada ciwo. Ba zaka taba sanin zafin cin amana ba sai lokacin da wanda ka yarda dashi yaci amanarka. Sai dai daukar hukunci kamar yanda wannan aljanin yayi ba abinda zai rage maka na daga radadin zuciya. Har yanzu Fally bai da alamar yin magana, dan ba lalle bane ma yaji abinda aljanin yake fada. Hankalinsa yana cen a tunanin abar kaunarsa, yana cikin kewarta sosai kuma da fama ciwon rashinta a kusa dashi. Wani aljani daya daga cikin masu gadin gidan yarin ne, yazo ya sanar dashi, mahaifiyarshi ta kawo masa ziyara. Bayan yazo daidai inda mai kawo ziyara ke haduwa da fursuna, mahaifiyarsa ya gani, take ya ji zuciyarsa ta rage zafi. Ita ma ta ji dadin ganin danta duk da akwai shamaki tsakaninta dashi. -Yaya kake dana? Tace tana mai tausaya masa -Lafiya lau nake, ke fa yaya kike? -Lafiya nake, sai dai nayi kewarka sosai. -Nima haka, yaya baba? -Lafiya lau yake, shi ma zuwa an jima zai zo ganinka. Ta fada, yanayinta na nuna alamar damuwa. Fally ya fahimci bata zo da labari mai dadi ba. - Ba zasu sake ni ba koh mama? -A'a dana... -Haba! Mama kinsan fah kwanakina kidayayyi ne anan. -Na sani Fally, na sani, hakan shi ke kara tayar min da hankali, kusan zaucewa nake ganin na samu hanyar fitar da kai! -Na sani Mama, kawai ina jin tsoron ranar da zan... -Ranar da zaka mutu? Ka yarda da ni, mutuwa ba yanzu zaka yita ba, zan fitar da kai daga wannan guri koda kuwa zan rasa raina. Haka ta cigaba da kwantar masa da hankali tare da yi masa alkawarin zata fitar dashi koda kuwa hakan zai zama ajalinta. Uwa kenan, ta kan so ta wahala akan danta ya wahala, Uwa zata iya sadaukar da komai dan ganin murmushin danta. Ga uwa farin cikin danta shine gaba da komai. Bayan tafiyar mahaifiyarsa, damuwarsa ta rage, farin ciki fal a zuciyarsa, tabbas yasan mahaifiyarsa zata fitar dashi, abinda yafi sanyashi farin ciki shine idan ya fita zai ga sanyin idaniyarshi Jinah, wadda ta dalilin ta ya rasa duk wata kima tashi ta aljanu, wadda ba zai taba daina sonta ba har abada.. -Kana ganin Jinah ba zata manta da kai ba kuwa? Wani bangare na zuciyarsa ne ke fadar haka. -A'a ba yanda za'ayi ta manta da ni... Nan fa rikici ya barke tsakanin bangarorin zuciyarshi. -Kana da tabbaci ne? Tayi fa nisa da kai yanzu! -Nisa ba abinda zai iya a soyayyar mu. -Ka tuna, tana da masifaffen kyau, kuma ba wani namiji da zai ganta bai kyasa ba. Murmushi yayi. -Baka yarda ba kenan? -A'a abokina, ni da Jinah mun riga mun yi aure, tare da alkawarin zama na har abada. Duk namijin da yayi kuskuren kusantarta, to fah jikinsa zai zama tamkar kifin da aka fiddo awa daya daga cikin ruwa. Mutuwa zata tabbata ga mutumin da yayi kuskuren yin hakan. Eh, Jinah tawa ce ni kadai har abada! A bangaren su Jinah Sarah ce ta shinfida tabarma, Jinah ta zauna. Dauko matajin kai da Man kwakwa Sarah tayi sannan ta zauna a bayan Jinah. -Bari muga yanda za'a yima wannan gashin naki, ki rage yawo dashi haka buzuzu. Sarah ta fada tana yamutsa gashin Jinah da mataji. Sarah sai da ta fara da nasanin farawa Jinah kitso, dan gashinta ba dai yawa ba, ga kuma santsi. Lura tayi da wani tabon haihuwa a bayan wuyan Jinah, tsayawa tayi, dan ta tuna mijinta yanada irinshi komai da komai shima kuma daidai da inda na Jinah yake. Abin daureta mata kai yayi, amma sai ta barshi a zuciyarta kafin ta maida hankalin ga yi mata kitson. Duk lokacin da ta kamo gashin da niyyar kitsawa sai Jinah tayi ta murkususu tana fadin "da zafi." tana turo baki. Sarah bata tanka mata ba, da abin Jinah ya isheta sai tayi mata rankwashi a tsakar ka ita kuma Jinah ta fasa kara. Haka suka cigaba da yi abin gwanin ban sha'awa. -To an kare! Sarah ta fada, mikewa jinah tayi tana ajiyar zuciya tace -Haba kin ji yanda mazaunaina suka yi kamar zasu kama da wuta. -Je ki duba madubi, zaki ga yanda na gyara maki shi, sai kin min godiya.. Dariya suka yi kafin Jinah taje ta duba a madubi, gashin yayi kamar an zatse kwarya, shi ba babba ba shi ba karami ba. Koda Jinah ta gani kasa motsawa tayi dan yayi bala'in kyau. Manyan zane ne Sarah tayi mata a tsakiyar kai tare da game jelar gashin ta dunkule waje daya ya sauka a gadon bayanta, kasancewar Jinah fara, haka fatar gashinta fara ce yasa zanen kitson ya fito da kyau. -Sarah kinyi gaskiya, yayi kyau sosai wallahi, nagode. -To idan kika tashi kwanceshi, zan sake maki wanda yafi wannan. -A'a gaskiya ba zan iya kara irin wannan zaman ba, ai sai duwawuna su fashe.. Dube dube Sarah take tana neman abinda zata jefi Jinah dashi, fahimtar abinda zata yi yasa Jinah tayi waje da gudu. -Shakiyiya! Sarah ta fada tana dariya. Bayan wasu yan mintuna suna zaune cikin daki, suka ji Bukari yana ta kwada sallama. Sarah ce ta amsa sannan tace masa ya shigo. -Wai kai Bukari, ba nasha fada maka idan kayi sallama biyu ta isa, sai ka jira a amsa ba? Cewar Jinah. -Babu banbanci idan biyu nayi ma tayi, idan kuma shida nayi ma tayi ko Tanti Sarah? Bukari ya fada cikin muryarshi ta yarinta. -Da gaskiyarka Bukari.. Sarah ta fada tana dariya, ita dai tana son Bukari, tana jinsa kamar danta. Bata samu sa'ar samun haihuwa ba gashi kuma ita mai son 'ya'ya ce. Sai dai ta dalilin Jinah da Bukari tana jinta tamkar Uwa kuma hakan yana mata dadi. -Jinah! kitsonki yayi kyau! Bukari ya fada yana kallon kitson Jinah. -Hmm nagode, Sarah ce tayi min. -Tanti Sarah kin iya kitso, fada mani kudinshi koda dubu dubu ne yanzu na biya.. Cewar Bukari, shi a dole dagaske yake, kallon juna matan suka yi. Barkoncin Bukari yasa yake da saurin shiga rai. Yaron yanada hankali da wayo, yana da cikin yaran kauyen masu zuwa school. Kwada masa kira yaji ana yi, ya amsa. -La'ilah, na manta! Tanti Sarah, Jinah mama tace na kirawoku kuci abinci. Sannan ya juya ya fita da gudu. -Duk wannan surutun da yake yi, ashe aikoshi aka yi kinji sai yanzu ya tuna. Cewar Jinah tana mikewa. Bayan sun ci abinci, kowa ya shige dakinsa, Jinah ta tarar da Lasaini dan uwan Sarah zaune tsakiyar gida. Yau tsawon kwanaki kenan tana son yi masa magana, sai dai bata samu dama ba dan bai cika zama gida ba. -Ina wuni? Ta fada, dago kai yayi ya kalleta, suka hada ido kafin ya amsa gaisuwarta. -Zamu iya magana? -Ina saurarenki. Zaunawa tayi bisa benci dake kusa dashi. -Magana ce nake son muyi akan Sarah. Yamutsa fuska yayi kafin yace -Kinga yarinya, ina mai baki shawara da kar ki shiga abinda ba ruwanki, dan baki san komai ba. -Ta bani labarin komai. -Wannan ba abinda ya dameki ba ne, dan haka ki fita daga wannan maganar kuma ki je ki kwanta dare yayi. -Ba'a gyara wata matsalar da kunno kan wata matsalar. Dakatar da ita yaso yi, amma ta rokeshi da ya saurareta. -Yanzu kamar kai, idan rana tsaka aka ce ka rabu da matarka, zaka iya?... ko kuma idan aka ce ita ta barka, ya zaka ji? Sunne kai Lasaini yayi alamar yana tunani. -Lasaini, Sarah tana son wannan mutumin sosai, ta yanda lokaci daya a nuna mata wani aibu nashi ba zata yarda ba. Wani lokacin soyayya tana hana mu ganin aibun masoyi. Ka dan yi tunanin ace kai ne ita na wani dan lokaci kaji. Tana cutuwa da irin rashin ko in kula da kake yi mata, wanda har ta kasa boye hakan, batada iyaye, batada 'ya'ya, kai ne komai nata a halin yanzu. Har zuwa wane lokaci zaka bar cutar da ita? Har zuwa wane lokaci zaka dawo yayanta na da? 'yar uwarka ce fah, kuma wajibinka ne ka kula da ita. Shiru Jinah tayi sannan ta mike da niyyar tafiya, itama tana jin tayi gangancin fadama mutumin da ya girme mata irin wadannan maganganun amma kuma tasan gaskiya ta fada. -Jinah! Kiran sunanta yayi, ta juyo tana fuskantarsa. - Wai nace shekarunki nawa? Idanu ta fiddo, tana mamakin me ya kawo kuma wannan tambayar? -Kawai naji kamar mahaifiyata ce a gabana... Ba tare da ta bashi amsa ba ta juya tana murmushi, cikin ziciyarta tace "Ashe dai maganganuna sunyi tasiri cikin dan karamin kanshi!" Ai kuwa, safiyar ranar, Lasaini yaje har gun kanwarsa ya nemi gafagarta. Sarah kasa gasgata hakan tayi, dan ranar tasha kuka, tayi ta yiwa Jinah buhu buhun godiya, gashi ta sanadinta ta shirya rashin jituwar dake tsakanin yan uwa. Fita Jinah tayi, ta barsu. Ta nufi bakin kogi. Rage kayan jikinta tayi ta fada cikin kogin. Cen taji ance -Kyanki ya kara fitowa, da kika yi kitso. Sauri tayi ta fito, ta saka kayanta sanin ta gane mai muryar. -Sarkin naci! Ta fada kasa da murya. -Sunana dai Dauda ba sarkin naci ba. Ya fada yana mai nuna mata alamar ya ji abinda ta fada. Kunya ce ta kamata. -A'a ai da kin cigaba da wankanki, kiyi kamar bana wajen. Ya fada ganin ta juya zata tafi. -A'a dama na kare. -Toh, dan Allah kar ki tafi, daman yau tsawon kwanaki kenan nake ta son na ganki. -Ni kuma? -Eh -Saboda me? -Ai na fada maki, kin riga kin fada komata. -Ni kuma ai na fada maka, bansan me kake nufi da hakan ba! -Zo ki zauna dan Allah, sai na fada maki ma'anar hakan. Haka dai ta hakura ganin magiyar da yake ta yi mata. Zaunawa suka yi bisa wan dutse. -Toh ina sauraronka? Cikin wata marainiyar murya ya fara fadin -Jinaaaaah, tuuuuun lokaaacin... Dakatar dashi tayi, tace -Dauda bafa waka nace ka yimin ba. -Jinah, bana ganin komai a duk lokacin da na ganki, bana tunanin komai a duk lokacin da nake tunaninki! -Ni fah ban gane komai ba a cikin wannan waken naka, ka yimin gwari gwari. -A takaice kin fada komata ne! -Oh Allah, wai Dauda wannan kalamin naka ba fahimtarshi nake ba. -Yi hakuri, to "ay gaba ni Jinah" -Da Hausa! -Ina sonki Jinah, ina matukar kaunarki, kuma ina son ki kasance matata. Tuni ta dade da harbo jirginshi, kawai dai tana so taji daga bakinshi ne. Sai dai bata so yaji ba dadi, dan tasan amsar da zata bashi ba zata yi masa dadi ba. Itama tana son Dauda, gashi hadadde, sai dai ta bashi zuciyarta wannan ba mai yiyuwa bane. Shuru dukansu suka yi, kafin ita ta mike da niyyar tafiya gida. jiri ne ya debeta ta koma ta zauna. -Bana jin dadi Dauda! Ta fada tana dafe kai. -Sannu, me yake damunki? tashi muje na rakaki gida. Mikewa tayi yana mata sannu, suka kama hanyar gida, sai dai ba wanda ke yiwa wani magana har suka karaso kofar gida. -Yauwa ya isa nan, Dauda zaka iya tafiya nagode. Ta fada tana rike da kanta. -Kin tabbata? Ya tambayeta da alamar damuwa a fuskarshi. -Eh kar ka damu! nagode Ta juya da niyyar shiga gida, ya kira sunanta -Jinah! Waiwayowa tayi, yace -Ina jiran amsarki. Bai jira jin me zata ce ba, ya juya ya tafi. Jinah tarar da Sarah tayi ita kadai cikin daki, Sarah ta damu ganin halin da Jinah take ciki. Kwantar da ita Sarah tayi, ta kura mata ido kafin tace -Jinah, amma kwanan nan kina jin tashin zuciya ko? -Eh ina jin haka dan wani lokacin sai naji kamar nayi amai. -Tinda kika zo gidan nan, ko kin taba ganin al'adarki? -A'ah ban taba ba. -Innalillahi, Jinah kar dai ciki ne da ke? --------------------------------------- Bon, zan dakata nan a yau. Sai kuma zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Fatan dai wannan chapter ta burge ku? To ku fada min abinda kuke tunani, i want to know hahaha. ? Muje zuwa a wata sabuwar chapter, kuma kar ku manta da yin comment domin shi nafi bukata. ?
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD