Asubar fari na yi, Sarah da Jinah suka fito da shirin zuwa asibitin dake kauyen. Suna fitowa, suka ga Safiya ce matar Lasaini kadai ta tashi, sauran har yanzu bacci suke. Bakin murhu take tana kokarin kunna wutar dumama tuwan karin kumallo.
-"Mat arango Safiya?" Ina kwana Safiya?
Sarah da Jinah ne suka gaisheta da yaren zabarmanci, ko kuma dai nace Sarah, dan Jinah tana cikin tashin hankalin da magana ma wahala take mata.
-"Samaï day no. Mat ni kani bani?" Lafiya lau, an tashi lafiya?
Safiya ta amsa masu gaisuwar.
-"Samaï day no wallah." Lafiya lau wallahi.
Sarah ta fada kafin tace
-"Jinah sigama inga gahamo kani, aygo ga dum loktoru koira." Jinah bata jin dadi, shine zan raka asibiti.
-"Ayyah! Irkoy madi ase, ma konda aran bani." Ayyah! Allah ya koro sauki, sai kun dawo.
-"Aminna, kala tonton." Amin sai mun dawo.
Hanyar asibiti suka dauka. Jinah har yanzu shiru babu alamar magana, duk tsoro da fargaba sun mamayeta. Bayan yar doguwar tafiyar da suka yi suka karaso asibitin, ba wata babbar asibiti bace kasancewar kauyuka irin Mambila sun fi ganewa yin maganin gargajiya akan na bature. Bayan sun je sun ciri tikitin ganin doctor. Kusa da Jinah Sarah ta zauna, ita kuma sai ta dora kanta bisa kafafun Sarah, Hankalin Jinah a matukar tashe yake tun jiya da Sarah ta tambayeta ko ciki ne da ita. Lallai idan dai ya tabbata ciki ne da ita, ta shiga uku dan bata san waye uban yaron ba, shin ta yaya ta samu cikin kuma wanne lokaci ne hakan ta faru. Addu'a ta cigaba da yi Allah yasa ba ciki bane, duk da tasan yanayinta yana nuna mai alamar mai ciki ne. Juyar da kanta tayi jin hawaye na son zubo mata. Hankalinta ne ya kai kan maganganun wata mata da bata zata wuce shekaru 50 ba da wata matashiyar budurwa da ba zata wuce 17 ba duke tana rizgar kuka.
-Me kike so na fada ma ubanki? Kin bani kunya Nana!
-Wallahi Mama ki yarda da ni, ba abinda nayi!
-"Ah to Nudu gunde par magie?" Ah kina nufin a ruwa kika shashi ko me? Kin bani kunya Nana, yanzu da wane ido zan kalli mutanen kauyen nan? Shikenan kin ja mutanen kauye su zageni suce na sakeki kin je kin yi ciki. To sai ki sani inda dare yayi maki dan yau kam ba dai a gidana ba, ni kinga tafiyata!
Juyawa matar tayi ta tafi cike da damuwa, ta bar yarinyar durkushe tana kuka. Mutane sai kallonta suke amma ita ko a jikinta.
-Bari naje na samo mana abin kari.
Cewar Sarah tana mikewa, gyada mata kai kawai Jinah tayi. Bayan tafiyar Sarah, Jinah matsawa tayi kusan yarinyar dake kuka.
-Yi shiru ki daina kuka, kar ki sawa kanki wani ciwon.
Jinah ta fada cikin sigar lallashi, ba tare da ta dago kai taga mai lallashinta ba, ta fara ba Jinah labarin abinda ya faru. Haka na kasancewa ga kowa, idan muna cikin damuwa mu kan so mu bayyanawa wani ita ko da ba zai iya yi mana maganinta ba kawai dai hakan nasa muji damuwar ta ragu.
-Na rantse da Allah ban yi komai ba, ni ban ma taba sanin yaya gaban namiji yake ba indai ba na yaro karami ba, ni ko saurayi banidashi, ba abinda na sani in ba karatu ba, ba anan kauyen nake ba, ina karatu ne a Niamey (babban birnin kasar Nijar). Nazo nan hutu ne, gashi yanzu wai nice da ciki, to wa yayi min shi?
Yanda take bada labarin da yanayinta zai tabbatar maka ita iya gaskiyarta take fada, hakan ya zama ruwan dare a kauyuka ba dama yarinya tazo daga birni, abin kamar maita. Haka saurayi zai je ma yarinya da sigar yana sonta, daga nan zai yaudareta, yayi mata ciki, in ma da saninta, ko kuma yayi mata asiri, ko kuma ya zuba mata wani abu a abin sha ta sha, daga nan ya gudu ya barta da taraddadi. Shikenan fa rayuwar yarinya ta lalace, haka zaka ga wasu sun zama karuwai, wasu su kashe kansu, wasu kuma ana samun maza masu tawakkali da dogon ilimi su auresu. Allah ya kyauta!
Hankalin Jinah kara tashi yayi jin labarin yarinyar gashi yana kamanceceniya da nata, sai dai ita tana ganin Sarah bata koreta bane, ganin ba a tabbatar da nata cikin ba.
Lokacin da layi yazo kanta, lokacin yarinya mai kuka ta tafi, Sarah ta dawo har sun karya. Wani bugawa zuciyar Jinah ke yi da sauri sauri dan da tafiyar hawainiya ta shiga ofishin doctor. Yana zaune yana duba wasu takardu, ba tare da ya dago kai ba yayi masu izini da zasu zauna, tareda cewa
-Ku dan jira yanzu abokin aikina yazo ya duba marar lafiyar.
Ganin har lokaci ya dan ja, abokin aikin nasa bai zo ba, ya dago kai yace
-Tinda har yanzu bai zo ba, bari ni na dubaku. Yanzu fada min me yake damunki?
Ya fada yana kallon agogo.
Sarah tace
-Kwanan nan ne take fama da zazzabi da tashin zuciya, shine muke son sanin ko...
-Ko me?
-Ina son sanin inada ciki ko a'a!
Jinah ta fada dan ita ta matsu taji wanne hali take ciki.
Bayan yan gwaje-gwaje da doctor yayi, ya tabbatar masu da Jinah tana da ciki. Doctor ya basu shawarar suna iya sake zuwa wani wajen ayi masu gwajin dan kara tabbatarwa sai dai ita Jinah batada wannan ra'ayin. Fita tayi daga asibitin da dan gudunta Sarah ta bita a baya. Sai dai Sarah bata yi nasarar cimmata ba sai da suka kai gida.
-Kalleni nan Jinah.
Sarah ta fada, cusa kanta tayi cikin katifa tana kuka. Ba wai tana kuka bane dan tanada ciki, a'a tunawa ne tayi matar nan ta dazu a asibiti dake hantarar yarta dan tayi ciki. Gani take itama haka Sarah zata yi mata, tasan itama haka mutanen garin zasu rinka nunenta suna zaginta.
-Ki daina kuka Jinah, nasan ke ba irin wannan yaran bane masu kai kansu ga maza.
-Kinada tabbacin haka Sarah? Idan fa saboda hakan ne aka koreni daga gida?
Jinah ta fada tana fito da kanta daga cikin katifa.
-Me kike cewa haka? kika sani ko kinada aure ne?
-Ki duba fa samari nawa suka zo neman aurena, ai ba wanda aka taba fadawa inada aure. To yanzu kina tunanin akwai wanda zai yarda idan aka ce na taba aure ko inada aure? Yanzu wane kallo kike tunanin zasu yi maki keda kika bani mafaka? Ina ga zan yi tafiyata kafin mutanen kauyen nan su gane har na ja maki abin kunya...
Kuka ne yaci karfinta.
-Eh na sani dole zasu yi ta fada, dan kina karkashin kulawata ne, kuma hakan ba zai yimin dadi ba. Amma hakan kasheni zai yi? ko kwantar dani zai yi rashin lafiya? A'a ba fah abinda zai sameni. dan haka ki daina wannan kukan ki natsu muyi tunanin samun mafita.
Mikewa Jinah tayi tana goge fuskarta tace zata je bakin kogi.
Sarah bata hanata ba don tana ganin wata kila hakan zai ragewa Jinar damuwa. Da zuwanta bakin kogi ta zauna ta hade kai da gwiwa. Zuwa cen taji kamar kana kallonta, juyawa tayi taga Dauda ne, karasowa yayi ya zauna gefenta.
-Yaya kike?
-Lafiya lau.
Ta bashi amsa a takaice.
-Anya dai?
Ya fada yana kare mata kallo, dan ya hangi damuwa a tattare da ita.
-Na fada maka lafiya nake.
Ta fada a dan tsawace.
Duk da hakan bai hakura ba ya kara tambayarta.
-Fada mun me yake damunki dan Allah?
-Kaga ko na fada maka ba abinda zaka iya yi a kai, kuma wai wane sani ne nayi maka da har zan fada maka damuwata? Dan haka ka rabu dani.
Duk wannan maganganun da ta fada mashi, basu hanashi yin dariya ba.
-Abin dariya ma ya baka kenan? Dan Allah ka rabu dani.
-Fushi baya maki kyau, kanki sai ya koma wani kala abin dariya.
Ya fada yana dariya. Ganin so yake ya kara bata mata rai yasa ta mike da niyyar tafiya.
Da sauri yace
-Yi hakuri dawo ki zauna dan Allah, duk da bansan me yake damunki ba, amma na damu ganinki cikin wannan hali.
Dawowa tayi ta zauna, sannan ta bashi hakuri akan daga masa murya da tayi dazun. Ya nuna mata ba komai.
Cewa yayi ta fada masa abinda ke damunta, amma taki. Rokonta yayi ta yi akan sai ta fada mashi, ganin nacin da yake mata, kuma ita kanta taji tana son ta bashi labarinta. Dan yan kwanakin da suka yi a tare ta fahimci Dauda mutum ne mai tausayi da kuma barkwanci. Sai dai tana tsoron idan yaji tanada ciki ya kasa fahimtarta. Daga karshe dai yanke sharawar ta fada masa tayi, bayan ta gama bashi labarin yace
-Yanzu kina nufin babu wani abu da kike iya tunawa na rayuwarki ta baya?
-Eh, abinda kawai nake tunawa ranar da na bude ido na ganni a wannan kauyen sai sunana. Kuma babban tashin hankalin shine....
-Ina jinki meye?
-Inada ciki!
Da sauri Dauda ya mike, cikin tashin hankali yace
-Ciki?
Sunne kai Jinah tayi tana hawaye sannan tace
-Wallahi bansan ya aka yi hakan ta faru ba, inada aure ne ko kuwa, ban sani ba? Nasan mutane zasu ta min kallon yar iska, ita kuma Sarah suyi ta nunata. Na jawo mata abin kunya.
Hada kai da gwiwa tayi ta cigaba da rera kuka. Shi kuwa Dauda safa da marwa ya fara a wurin kafin yace
-Ni nasan yanda za'ayi!
Da sauri Jinah ta dago tace
-Ta yaya?
-Abu mai sauki, na aureki kinga mutane zasu yi tunanin dan nawa ne.
Duk da hawayen dake fuskar Jinah hakan bai hanata kyalkyata dariya ba tana yi tana cewa
-Daman na dade ina wannan tunanin, ba isashiyar lafiya gareka ba...
-Allah Jinah da gaske nake!
-Gaskiya bakada hankali, ni kaga tafiyata.
-Ki dakata Jinah, Allah da gaske nake, hakan ita kadai ce mafita.
-Kaga, bamu san juna ba kace kana sona, haka ka cigaba da bibiyata tin daga ranar da wannan abun ya faru, a duk lokacin da nazo cikin jeji ko bakin kogi sai na tarar da kai. Yanzu kuma nace maka inada ciki ba tareda nasan ta yaya na sameshi ba, kai kace zaka aureni. Fada mani wane mai hankali ne zai yin irin wannan?
-Kinada gaskiya Jinah, amma kin manta da cewa idan mutum ya kamu da soyayya, zaucewa yake yi. Saboda daga ranar ba kwalwa bace ke jagorantarsa, Zuciyarsa ce, zuciya Jinah!
-A dauka na amince, idan kuma aka je inada aure, kuma na tuna komai?
-Daga ranar babu aurenmu, na amince zan barki ki tafi.
-Ni fah bana sonka Dauda!
Duk da yaji maganar tata kamar saukar aradu, hakan bai hanashi cijewa yayi dariya ba.
-Kai abin dariya ma ya baka kenan?
-Ina dariya ne, dan zan aureki dan ina sonki duk da ke baki sona, amma zan zauna zaman jiran ranar da kema zaki bude baki kice kina sona.
-Gaskiya ba zan iya ba Dauda, kayi hakuri.
Ta juya ta tafi, ta barshi a tsaye kamar an dasashi, shi kanshi yayi mamakin kalamanta sai dai wannan itace mafitar da zai iya samun Jinah, don har cikin zuciyarshi yana sonta. Tun jiya da ya fada mata yana sonta, bai ga alamar amincewa a idonta ba, yasan taki fada masa ne dan kar yaji ba dadi.
Yanzu kuma yana cikin farin ciki ganin zai aureta, sai dai sam bai ji dadin jin tanada ciki ba. Amma yana tunanin komai zai zama daidai da ya aureta.
Jinah karasawa tayi gida da kuka, ita dai bata san me yasa rayuwa tazo mata a haka ba, duk da ta fara sabawa da cutar mantau din da yake damunta, sai dai yanzu abin ya dawo mata sabo sanadiyar wannan cikin. Abincinta Sarah ta kawo mata, sai dai bata cikin yanayin da zata iya cin abinci. Tunani ta fara
Yanzu idan na auri Dauda, mutane zasu dauka Dansa ne, kuma hakan ba zai taba mutuncin Sarah ba, ba zan iya ja mata abin kunya ba, dan tayi min halacci kwarai. Kuma Dauda mutumin kirki ne, nasan ba zai wulakantani ba...
Tana idar da tunaninta, ta duro daga kan gado ta nufi bakin kogi inda ta baro Dauda. Tarar dashi tayi a gurin zaune yana wasar jefa kananan duwatsu a ruwa. Wani dogon numfashi ta ja, kafin ta kira sunanshi.
-Dauda!
Ba tare da ya juyo ba yace
-Oh Allah, haukacewa zanyi, har muryarta nake ji alhali bata wajen.
Zaunawa kusa dashi Jinah tayi tareda cewa
-Ni din dai ce da gaske.
Har wata yar zabura Dauda yayi dan baiyi tunanin zata dawo ba.
Sunkuyar da kai tayi kafin tace
-Nayi tunani kuma na amince zan aureka.
Wani farin ciki ne ya lullube Dauda, ta yanda kasa fadin wani abu yayi. Ji yake tamkar a mafarki, wanda kuma ba zai so ya farka ba.
Kowannen su tunani ya fara ta yanda wannan al'amari zai kasance, sai dai basu yi tunanin me zai je ya dawo ba. Dauda yana matukar sonta, Sai dai bai san abinda zai sameshi ba idan ya auri JINAH matar aljani.
---------------------------
Madallah, a nan zan tsaya a yau, sai kuma idan Allah ya kaimu a wata sabuwar chapter.
Kada ku manta da fadar ra'ayinku na wannan labari...!?