CHAPTER 5

2284 Words
Kalmomi sun yi kadan wajen fayyace maku irin farin cikin da Dauda yake ciki. Har yanzu ya kasa gasgata cewa Jinah ta yarda zata aureshi, ganin kin amincewa da tayi a baya. Duk da wawanci ne auren mace da ciki, sai dai Dauda yana ma Jinah matsanancin son da idanunsa sun rufe ba zai iya ganin aibun da zai hanashi aurenta ba. Abinda yake ji game da ita kwarai ne, wanda shi kanshi ba zai iya fassarashi ba. Muna iya fadawa soyayyar wani a kowanne lokaci, ta dalilin haduwar farko ko kuma a kallon farko. Haka so yake. -Yauwa ka bani labarinka. Jinah ta fada tana mai kawo karshen zurfin tunanin da kowannensu ya fada. -Da farko dai, anawa gidan mu lakabi da gidan Malam Shehu, inada 'yan uwa maza uku da mata biyar wanda muke uwa daya uba daya. akwai kuma yan uwa maza da mata wanda muke uba daya. Mamata itace mace ta biyu cikin su hudu a gun babana. Ke a takaice dai mu mun kasance babban dangi da muke zaune a gida daya... -Kai kace babban gidane? -Sosai ma kuwa ai sai kin shiga ciki zaki gani. Murmushi Jinah tayi tana kallonsa. Cigaba yayi da bata labarin gidansu. -Babana yanada babbar masana'antar sarrafa auduga, babban mutum ne kauyen mu. Ke dai sai kinje kin ganema idonki. Jinah na murmushi tace -Naji labarin gidanku, saura naka. -Shekaruna 20 daidai, tun ina da shekaru goma na bar school na koma masana'antar babana da aiki. kinsan anan bamu baiwa karatu muhimmanci ba. Saura ke bani labarinki. Kwalo ido Jinah tayi tace -Amma wasa kake ko? -Da aka yi me? -Kai da na fada bana iya tuna komai... Ta fada cikin yanayin damuwa. -Oh yi hakuri, na manta. -bari naje gida, na fadawa Sarah. -Toh, amma ki shirya gobe zan zo muje ki gaida yan gidan mu. -Ok, Allah ya kaimu. Ta fada tana mikewa. -Ameen, ki gaida yan gidan. Koda Jinah tayi nisa, Dauda dan tsalle yayi tare da cewa "Yes!" rawa ya fara tika kamar mahaukaci. Gida ya nufa, mahaifiyarshi ce ta farko da ya fara ba labarin Jinah. Yana yan tsalle tsalle, yana fadawa mamanshi -Na samota Mama, mama na samota! -Me ka samu dana? Mamarshi ta fada tana kallon ikon Allah ganin yanda yake tikar rawa gabanta. -Na samo matar aure mama! Inda kin ganta kamar aljana tsabar kyau, sai idan ma tayi magana mama, sai inji kamar tayi ta magana kar tayi shiru. Muryarta idan kika ji kamar algaita, murmushinta wayyoh.. hakorinta sai kice na karamin yaro. Dariya mamarshi ke yi, dan idan da sabo ta saba da shirmen dan autanta. Kawai gani take giyar soyayya ce take diban dan nata yake wannan sambatun. Yana gama shirmenshi ya nufi masana'anta ya tarar da mahaifin nashi. Daure fuska mahaifin nashi yayi, kafin yace -Sai yau kayi niyyar zuwa? Yaushe rabonka da zuwa aiki? -Ai Abbah, yanzu ma ba aikin bane ya kawoni, nazo ne na fada maka wani labari kuma sai kayi farin ciki da jinsa. -Meye wannan da ya hana min yaro zuwa gurin aiki? -Abbah, na samu mata, duk wannan lokacin da na dauka ina wajenta ne, dan in san halinta sosai, in san ko matar aure ce. Kuma Abba komai ta hada, kyau, hankali da komai ma. Yanda Dauda ke ta zuba gaban mahaifin nashi zai tabbatar maka da shagwababbe ne sosai. Cike da fara'a Mahaifin nashi yace -Ah to madallah, dole kaki zuwa aiki, ashe ka fara zama mutum. Fada min yar gidan waye? -Ba anan kauyen take ba, a Mambila take. -Ah hakan yayi kyau, Allah yasa alheri. -Ameen Abbah, gobe insha Allahu zan kawota ta gaisheku, jibi kuma sai kuje ku nema min aurenta... -To ba damuwa, Allah ya kaimu lokacin. -Ameen Abbah, bari naje na kama aikin. -A'ah yau na yafe maka, kaje ka huta. -toh nagode abbah! Ya fada cike da zumudi ya nufi gurin abokinshi. Ita kuwa Jinah zuwa tayi ta fadawa Sarah. Hakan ya girgiza Sarah, dan kasa cewa komai tayi. -Dan Allah kice wani Abu Sarah! -Ni..Ni bansan me ya kaiki yin wannan gangancin ba. Kin ga na farko baki san wannan mutumin ba, ke ba sonshi kike ba, kina tunanin aure wasa ne da zaki yanke wannan shawarar ba tareda kin fada min ba? Kunya ce ta kama Jinah ta sunkuyar da kanta, dan wannan shine karon farko da taga ran Sarah ya baci. Kuma tasan Sarah tafi ta gaskiya. -Dan Haka wannan aure ba yiwu ba, dan sam ni ban amince ba. -Na fa riga nace masa na amince Sarah, kuma wannan ita kadai ce mafita, idan ba haka ba kema kinsan abinda zai faru. Shiru Sarah tayi na wani lokaci kafin tace -Wannan ba hujjah bace Jinah, ni dai ban amince ba, dan haka ki fidda wannan tunanin a ranki. Fita tayi ta bar Jinah a gurin. Kuka kam Jinah tashashi, dan daren ranar kasa bacci tayi. Washe gari, Dauda yazo daukan Jinah, ranar, ranar hutu ce, kowa yana gida, har da Lasaini da yayi mamakin ganin Dauda. Koda Jinah ta ganshi kallon kayi hakuri tayi masa, shi kuwa yayi kamar bai gani ba. Bayan ya gama gaisawa da yan gidan, ya nemi da su kebe da Lasaini ganin shine babba a gidan. Bayan sun kebe Lasaini yace -Ya sunan malamin ma? -Sunana Dauda Ibrahim. -Madallah malam Dauda, ko me yake tafe da kai? -Am.. Nazo ne daman na gabatar maku da kaina, ina son auren Jinah ne. -Ikon Allah, amma ita Jinar ta sani? -Eh ta sani, dan har ma ta amince. -To madallah hakan yayi kyau, sai dai ni banida iko da ita, iyayenta ba anan suke ba, tana karkashin kulawar yar uwata ne, amma bari na kirata dan jin me zata ce. Kiran Sarah Lasaini yayi, bayan wani dan lokaci ta zo. -Sarah, wannan saurayin da kike gani yazo ne da maganar yana son Jinah, kasancewar tana karkashin kulawarki, kuma ke kika san iyayenta yasa na kiraki dan ki ji. -Eh Jinah ta fada min, sai dai zan so muyi magana da shi, daga ni sai shi. -Ok, ba damuwa, bari na baku waje. Lasaini ya fada tareda mikewa ya tafi. -Me kake so ne da wannan yarinyar? Sarah ta fada fuska a tamke. -Ban fahimta ba, me kike nufi? -Wanne namiji ne zai yarda ya auri yarinya tana cikin wannan halin, ba tare da ita kanta tasan ya aka yi hakan ta faru ba? -Nasan kina son Jinah, kuma ba zaki so wani abu ya sameta ba, ina mai tabbatar maki ba wani abu nake so ga Jinah ba, face farin cikinta. Ina sonta har cikin zuciyata, duk da nasan ita bata sona kamar yanda nake sonta. Kuma ke kin sani, duk yawancin auren da ake yi cikin kauyen nan, auren hadi ne, daga karshe bayan aure ya juye zuwa na soyayya. Nayi maki alkawarin zan saka Jinah farin ciki, kuma ba zan taba cutar da ita ba. Nayi maki wannan alkawarin. Jin abinda Dauda ya fada yasa jikin Sarah yayi sanyi. Tayi shiru na wani dan lokaci kafin tace -Amma kasan ba'a yin aure da ciki ko? Kuma ya zaku yi da darenku na farko? dan kasan ba budurwa bace. -Kar ki damu, ke dai a daura auren, nayi maki alkawarin babu wata matsala da za'a samu. Kiran Lasaini Sarah tayi. -Lasaini, iyayen Jinah sun bani ita ne, tareda bani duk wani iko akanta, ganin ni mace ce ba zan iya bada aurenta ba, yasa nace zan baka ramagar komai, kuma kaga kai ne babba a nan. -Idan haka ne, babu damuwa, kai Dauda ka turo min magabatanka domin mu tsaida magana. Kuma a gaskiya naji dadi da zata yi aure dan na gaji da ganin samarin da ke min sintiri a kofar gida. -Naji dadin jin wannan kuma insha Allahu idan na koma gida zan turo magabatana. Amma yanzu ina son ku yimin izini muje da ita don ta gaishe da mahaifiyata. -Wannan ba matsala bace. Cewar Lasaini. -Shikenan bari nayi mata magana. Sarah ta fada tana mikewa. Dakinta ta nufa ta tarar da Jinah zaune ta kurawa window ido. -Tashi ki shirya zaku je ki gaida iyayen mijinki na gobe. Tsalle Jinah tayi bisa gado tare da cewa -Wai kin amince!? -Eh, munyi magana dashi kuma naga tsantsar sonki a idonshi. Nasan ba zai cutar dake ba. Da sauri Jinah ta shirya, ta nufi gun Dauda da ya hangota yake ta watse hakora. A tare suka fito daga gidan. Wani kyakkywan doki Jina ta gani a bakin kofa. -Kai dokin waye wannan mai kyau? Ina matukar kaunar dawakai! Ta fada tana karasawa kusan dokin tare da shafa kanshi. -Nawa ne! Cewar Dauda. -Dagaske? amma me yasa ban taba ganinka dashi ba? -Ya dan yi rashin lafiya ne, shi yasa na barshi ya dan huta. -Mace ce ma ko? meye sunanta? -Ashanti sunanta! -Suna mai dadi! Zan iya hawa? -Me zai hana? tsaya ki gani. Hawa ya fara yi sanann itama Jinah tayi kamar yanda yayi ta hau. Kada kan ashanti yayi, Sai da suka yi tafiya mai nisa kafin su kawo gidan. Jinah tayi mamakin ganin gidan, dan babban gida ne. Gabatar da ita ya fara yi ga mahaifiyarshi wadda tayi mutuwar zaune dan bata taba zaton maganar da danta ya fada gameda kyan Jinah gaskiya ne ba. Ta yaba da hankalin Jinah kuma taji tana sonta. Sauran yan gidan ya gabatar ma da Jinah, tsabar yawansu kasa rike duka sunayen su tayi. Gida ya dauka "Matar Dauda, kamar aljana." Washe gari, iyayen Dauda suka je gidan su Jinah neman aurenta, ba wata-wata aka tsaida maganar aure, domin mahaifin Dauda babban mutum ne da duk kauyukan dake yankin an sanshi. Kwanci tashi asarar mai rai, yau an daura auren Jinah da Dauda. Farin cikin Jinah kasa boyuwa yayi, har wani zumudi take. Bayan ta fito daga wanka, Sarah ta kunce mata kitso, sake mata wani tayi saidai bai kai na farkon ba, dan irin simple din nan ne tayi mata, ta dunkule gashin duka, yayi mata tozo a tsakiyar kai. Zuwa karfe goma, gidan ya cika da mutane, makada da maraya sai cashewa ake. Kasancewar abin yazo da gaggawa babu abinda Sarah ta dinkawa Jinah, sai Wani leshi madaidaici da kuma wata doguwar riga tata da bata taba sakawa ba. Da leshin tayi yinin ranar, da dare kuma Sarah ta bata doguwar rigar ta saka. Rigar tayi mata bala'in kyau. -Wow, gaskiya wannan riga ba dai kyau ba! Jinah ta fada tana juyi dan ganin yanda rigar take a jikinta. -Eh ta jima gareni, amma ban taba son sakata ba, gashi yanzu tayi rana. Rungumeta Jinah tayi, dan nuna godiyarta. Zuwa karfe tara na dare kafin a dauki Jinah zuwa gidan su Dauda, Sarah ta zaunar da ita a daki dan yi mata huduba. -Toh Sarah, yau Allah gashi yayi kin yi aure. Mijinki yayi min alkawarin babu wata matsala akan maganar budurci, kuma ina fatan hakan. Dama tsorona dangin mijinki. Dan Allah ki kasance mai yiwa mijinki biyayya, duk da nasan baki sonshi amma kuma babu wanda ya takuraki da sai kin aureshi dan haka dole kiyi masa biyayya. Kuma gashi kinyi sa'ar miji mai hankali, duk da hakan nima nayi tsammani a aurena. Dan Maza sai ana yi ana taka tsantsan dasu. Ina son dan Allah kiyi masa biyayya kamar yanda kike min, yi nayi, bari na bari. Sannan kiyi hankali da danginshi wasu zasu soki wasu kuma a'a, duk da haka ki zauna dasu lafiya. Ina son ki dauki Mahaifiyarshi da kishiyoyinta tamkar mahaifiyarki, mahaifinshi tamkar mahaifinki, 'ya'yan yan uwanshi tamkar 'ya'yanki. Sannan kuma kiyi hankali da yan uwanshi maza, dan kinsan namiji ba ruwanshi da ke sirika ce ko akasin haka, bare kuma ke ga yanda kike masha Allah. Ki tarairayi mijinki tamkar jinjiri... Tashi muje yanzu wata rayuwar na jiranki. Kuka Jinah ta fashe dashi. Dan har ga Allah taji bata son rabuwa da Sarah to amma ya zata yi. Rakata Sarah tayi har gurin yan daukar amarya. Suka tafi ana guda, wasu na waka wasu na raye raye. Bayan sun kaita kowa ya watse banda Sarah da zata kwana a gidan dan ta zama shaida idan Jinah budurwa ce. Sanin Jinah ba budurwa bace yasa hankalinta ya kasa kwanciya, bata san wace dabara Dauda zai yi ba gobe. Jinah ce zaune a tsakiyar gado ita kadai cikin wani babban daki. Ganin Dauda shuru babu alamun Dauda tayi niyyar kinshigidawa sai gashi ya shigo. A hankali ta mike zaune. Ajiye ledar hannunshi yayi tare da tambayarta gajiyar biki. Bakar ledar da ya shigo da ita ya janyo ya bude, dakwalan kaji ne guda biyu. Tashi yayi ya dauko faranti ya fiddo kaza guda ya babbaleta sannan yayi mata bisimillah. Nokewa tayi, akan ita a koshe take. Da naci da lallashi yasa ta dan ci kadan. Tashi tayi ta wanke bakinta sannan ta dawo ta kwanta. Bayan shima ya gama ci, ya tattare yaje yayi brushing. Fira ya fara janta sama sama tana biye mashi, har bacci ya dauketa, shima ganin tayi bacci ya kwanta. Da safe karar bugun kofa ne ya tashesu. Dauda yaja dan guntun tsaki kafin yace -Waye? -Sarah ce! Wani bugawa zuciyarshi tayi, dan shi sam ya manta da wani farin zanin gadon da ya kamata yan uwanshi su ga jinin budurcin Jinah, gashi bai yi tunanin yin wata dabara tun jiya da dare ba. Tsoro ne ya kamashi, dan bai san wane kallo mutane zasu yiwa Jinah ba. Karin bugun kofar ne ya karu, muryoyin biyu daga cikin aunties dinshi yaji. Cike da tashin hankali ya fara Safa da Marwa a cikin dakin yana tunanin mafita. ---------------------------- Dauda a cikin tsaka mai wuya, yanada kyau ku bashi shawarar abinda zai yi Fans ko dan ku ceci Jinah abar kaunarsa. ?
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD