CHAPTER 6

2396 Words
Sintirin da Dauda ke yi a tsakiyan daki, kamar zakin da aka kulle a keji. Tunani kawai yake ko zai samu mafita. A jiya sam ya manta da alkawarin da yayi wa Sarah, dan shi hankalinsa ya karkata ne a zumudin son cikar mafarkinsa na ganin abar kaunarsa a gidansa. -Me yake faruwa ne? Jinah ta fada cikin muryar bacci. Tausayinta ne ya lullube Dauda, yayi mata irin kallon kiyi hakuri. -Me yake faruwa ne Dauda, kayi magana? Ta sake tambayarshi, amma wannan karon muryarta ram take ganin yanda mijin nata ke safa da marwa yasa dole baccin ya gudu. -Sune a waje! Ba sai yayi mata wani karin bayani ba, ta fahimci yan uwanshi ne dan Sarah tayi mata bayani. Amma ganin halin da mijin nata yake ciki ya tabbatar mata da ba wani shiri da yayi. Rawa jikinta ya fara, tsoro duk ya mamayeta. Toshe bakinta tayi kafin ta fashe da kuka. Ita ba kanta take tausayawa ba, Sarah dake waje, dan tasan tabbas sai tasha kunya ganin ita ce ta tsaya tayi sheda. -A'a kar kiyi kuka dan Allah, zamu nemi mafita! -Wace irin mafita? Ta fada hankali a tashe. Tunani Dauda yayi na wani dan lokaci kafin yace -Ko zakara nake samu na yanka sai mu zuba jinin a zanin gadon? -Me? Hauka kake yi? Kana fa fita su zasu shigo kuma ma me zaka ce masu idan suka ganka da zakara? Dafe kai yayi dan mafitar da kadai ya iya samu kenan. -Me zai hana muyi abinda suke so? Jinah ta fada tana kallon Dauda. -Toh me hakan zai samar, ai a budurwa kadai ake samun abinda suke so. Haka kowanensu yayi ta kawo shawarwari wanda ba zasu fiddasu ba. Ana cikin haka Dauda ya nufi wata yar karamar wuka da ya gani bisa dressing table ajiye. -Me zaka yi da ita Dau...? Kafin ta karasa tambayarsa, ya bude tafin hannunshi na hagu ya yanka. Zuwa yayi ya tara bisa zanin gadon a take jini ya fara zuba. -Wayyo Allah...! Cike da tsoro Jinah ta fada tana toshe bakinta da hannuwanta. -Ke, ba fa wani abu bane, kawai dan karamin ciwo ne kuma bada jimawa ba zai warke. Ya fada dan ya kwantar mata da hankali. Ganin jinin ya tsaya yasa ya goge hannunsa. Sannan yace mata ta kwanta, yaje ya bude kofa. Kusan kadashi aunties din nashi suka yi, shigowa dakin sukayi Sarah na biye dasu a baya fuska a dame. -Ka wani garkame daki kai ga mai mata ko, baka son kowa ya shigo. Daya daga cikin aunties din nashi ce ta fadi haka. -Ai ba laifina bane, kusan kasheni fah tayi... Dauda ya fada cikin rada yana wani murmushi. -Kai jah cen ko kunyar mu baka ji... Dariya suka yi, sannan suka karaso kusan amarya dake dunkule. Jan abu suka gani ga zanin gadon. Nan fa matan biyu suka hau guda. Daya daga cikinsu ce tayi kokarin daukar zanin gadon amma Dauda ya hana. -Wannan kuma ba zai yiwu ba! Nine zan ajiyeshi, dan zai zama abin tunawa na karamcin da matata ta yimin, na bani wannan kyautar. Jinah ji tayi kamar ta nutse tsabar kunya. Fita matan sukayi, suna guda suna fadawa sauran mutanen gidan Jinah budurwa ce. Nan fah gida ya dauka "Matar Dauda danya ce kamar tuffa sabuwa fil a leda".... Abinda basu sani ba, Dauda yaki basu zanin ne, dan kar suje wani dan konkonto ya gano ba jinin budurci bane. Ajiyar zuciya Sarah tayi. Ta shiga ta tarar da Jinah, Rungumeta tayi ba tare da tace wani abu ba. Haka suka kasance rungume da juna na tsawon dan lokaci kafin Sarah ta rada mata a kunne. -Nasan baku yi wani abu ba Jinah, amma ki shirya lokaci na zuwa. Dan Allah kiyi kwanciyarki daki, kar ki fita su fahimci wani abu. Kuma idan kina bukatar wani abu ki zo ki ganni zan baki, idan kin tuna da rayuwarki ta baya ki zo ki fadamin. Ki kula da kanki, zan kasance kullum domin ki kuma zan yi kewarki. Gyada mata kai kawai Jinah tayi, tana hawaye, dan itama tasan zata yi kewar Sarar. A haka Dauda yazo ya tarar dasu, ya dade yana mamakin irin wannan shakuwa tasu, gashi basu hada komai ba, amma Sarah tana jin Jinah tamkar 'yar uwarta ko kuma 'yar da ta haifa. Mikewa Sarah tayi, kafin ta tafi ta kara jaddadawa Dauda alkawarin da yayi mata na kulawa da Jinah. Bayan ya raka Sarah, ya dawo daki wajen matarshi. Babban daki ne da makeken gado a tsakiya, a gefe kuma akwai dressing table da wardrobe, sannan bathroom madaidaici. Dakin ya kawatu sosai, har da gidan ma baki daya. Saboda idan ka shigo cikinsa zaka dauka a birni kake, duk da yanzu kauyuka da dama ana ta samun cigaba amma wannan ya banbata da sauran, dan a kauyen babu irinsa. Bayan wani dan lokaci, Jinah ta fara jiwo wani sauti, wata murya, ba yau ba ne na farko da ta fara jiwo wannan sautin. Amma wannan karon taji kamar sautin kusa yake ba kamar da ba da take jiwoshi daga nesa. Shurun da tayi tana sauraran sautin ne yasa Dauda ya tambayeta. -Me yake faruwa? -Daga ina wannan sautin yake fitowa? -Wane sauti kike magana? -Saurara kaji. Saurarawa Dauda yayi kafin ya fahimci me take nufi. -Wannan kiran sallah ne! -Kiran Sallah? me hakan ke nufi? A da ina jiwo sautin ne daga nesa amma yanzu kamar... -Eh anan cikin gidan ne, muryar Buraima ce, yayana. Hakan yana nuna alamar lokacin sallah yayi. Ya fada cikin yanayin damuwa, dan ya fahimci matarshi babu abinda ta sani game da musulunci, wata kila yana daga cikin matsalar mantau da ta samu ne. Ya fahimci hakan ne tun ranar da ya fada mata yana sonta. Duk da irin wannan ba wani abin mamaki bane a kauyuka. A kauye mutane na amsa sunan musulmai ne amma basa yin komai da ya danganci musuluncin, suna yawan fadar za suyi idan sun tsufa, su a tunaninsu addinin ana yinsa ne idan aka cimma kabari wato tsufa, akasarinsu matasa ne suka yi imani da wannan da'awar. Shi kanshi Dauda a baya yana fadar hakan har zuwa lokacin da yaje Maradi wajen wani kawunsa, anan yaga yaro dan shekara 7 bakwai yana sallah abin gwanin ban sha'awa. A ranar yaji kunya ba kadan ba, tun daga ranar ya shiga neman ilimin addini. Anan ya gano muhimmanci da kuma wajibi na gudanar da addini. Yana dawowa kauyensu yasa mahaifinsa ya gina masallaci a cikin gidansu kuma da taimakon wani malami a kauyen yayi nasarar jawo hankalin yan gidansu da ma makota suna zuwa sallah. Duk da har yanzu ba wani sani gareshi sosai a cikin addinin ba, amma yasan hakkoki da kuma gujewa duk wani sabon Allah. Duk da yan kwanakin nan yana fama da muguwar sha'awa, hakan yasa yake yawaita azumi da tsayuwar dare dan gudun fadawa tarkon shedan. -Matso nan kusa dani! Ya umarci Jinah, ba musu ta matso ta zauna dab dashi bisa gado. -Kinsan addinin musulunci? Ya tambayeta. -A'a. -Ok, bari yanzu idan na dawo daga masallaci, sai muje gurin liman. Bata fahimci komai ba cikin maganar, shi kuma murmushi yayi ganin yanda take ta kyafce-kyafce. Kamar yanda yayi alkawari, yana dawowa, ya kaita wurin Liman. Liman ya biya mata kalmar shahada. Cikin yan kwanaki kadan Jinah ta iya abubuwa sosai na musulunci, haka itama ta koyawa Sarah lokacin da taje gida. Kamar walkiya lokaci yake wucewa, Jinah tana zaune lafiya da mijinta da sauran danginshi. Sai dai matsalarta daya rashin iya girki, amma cikin sa'a Dauda yayiwa mahaifiyarsa bayani. Ba tare da bata lokaci ba, a boye mahaifiyar tashi ta fara koyamata. Dan ita kanta abin kunya ne gareta sauran mutanen gidan su fahimci sirikarta bata iya girki ba. Jinah tayi sa'ar sirika, dan bayan girki har da abubuwa da dama take koya mata. A farkon watan June cikin Jinah ya fara bayyana, dan yanzu zai kai wata hudu. Dauda yana nuna kulawarsa sosai akan cikin, amma ita sam bata son cikin dan ko maganarshi bata so ana yi, wani lokacin ma shigewa daki take ta yita kuka. Kullum Dauda cikin rarrashinta yake da nuna mata ko ta wanne hali ta samu cikin, jininta ne kuma dole ta kaunaceshi. Duk zaman nan da suke, ko kuskuren tabata Dauda yayi to fa ranar sai ya kwana da jinya. Ganin haka da kanshi yaba kanshi baki, kuma shima hakan ce ta fiye masa. Wata ranar lahadi da yamma, Dauda ne zaune ya buga uban tagumi, ya fada duniyar tunani. Wanda hakan ba halinsa bane. Ganin haka, Sarah ta tambayeshi ko lafiya. Dan karamin tsaki yaja kafin yace -Ba komai, kawai bana jin dadi ne. Mikewa yayi ya nufi tsakar gida. Tarar da Kakarshi yayi ta tara yara tana yi masu tatsuniya. Wata aljana ce mai kyau da dogon gashi. Da dare yayi sai ta boye fuskarta, ta sa fararen kaya, ta shiga cikin kauye tana cinye mutanen kauyen yara da manya... Bai tsaya jin karshen labarin ba, ya juya cikin daki wajen matarshi. -Inada wata dabara! Ya fada tareda yin murmushin mugunta. -Toh, wace irin dabara? Jinah ta tambayeshi. -Kinada farar riga doguwa? -Eh... inada.. me zaka yi da ita? -Ina so ki sakata, dan yau ina son kallon drama ne. -Ban fahimta ba, me zamu yi da ita? -Kaka ce ta tara yara tana masu tatsuniya. Bata labarin abinda yaji kakar na fada yayi, sannan ta fahimta. -Ka tabbatar tsorata su zaka yi? Kar fa a samu matsala? -Ba wata matsala da za'a samu ke dai sako rigar, kawai dan ayi nishadi ne. Ya fada yana murmushi. Ba tare da tana son yin wannan wasa ba, dan kawai bin umarninsa zata yi. Saka rigar tayi, doguwa har kasa sannan ta kunce gashinta ya barbazu a fuskarta. Fita suka yi tsakiyar gida, labewa Jinah tayi, shi kuma Dauda yaje cikin yaran yayi zaune. -Kinga Kaka ki daina basu labarin aljanun nan, kinsan idan ana bada labarinsu bayyana suke... Dauda ya fada yana mai gargadin kakar tashi. Karyatashi kakar tayi sannan ta cigaba da ba yaran labari. -Shikenan ni dai na fada maku, amma baku ji ba. Ya fada yana mikewa, Jinah ce ta fito daga inda ta buya ta dunfarosu. Kaka ce ta fara kara sannan ta gudu, yaran ma suka rufa mata baya suna fadin "Da gaske Dauda yake akwai aljana", Kyalkyacewa da dariya Jinah da Dauda suka yi, sannan suka gudu suka buya. Mutanen gidan ne suka fito dan ganin meke faruwa. -Wallahi ku dai anyi yara, bansan yaushe zaku girma ba. Mahaifiyar Dauda ce ke fadar haka da ta tarar dasu suna kyalkyatar dariya. -Ai Mama ko ba komai, Kaka ta motsa jikinta. Dauda ya fada yana dariya. -Haba zaku gane kurenku idan ta gano kune, kuka yi mata wannan shakiyancin. Mahaifiyar ta fada kafin ta koma daki. -Gaskiya ka cika yarinta Dauda! Jinah ta fada. -hahaha, ai ni ba abinda nayi, kece kika tsorata su. Kinga yanda kika yi kuwa? Kin bazo gashi ga kuma katon cikin ki. Dauda ya fada yana dariya. Bata rai Jinah tayi jin yayi maganar cikin. Dan sam bata son maganar cikin. -Ke lafiya, wannan fa danki ne, ya kamata ki daina wannan abun. Me yasa baki son ana maganarshi? Wallahi ni ina jinsa kamar dana ne, duk da ba nawa bane. Dan haka ki daina wannan abun. Kinga zo muje ki dan tattaka. Suna yin taku kadan, wani ya tari gabansu. Idrisa ne, daya daga cikin yan uwan Dauda da suke uba guda. Murtuke fuska Dauda yayi, dan sam basu shiri tsakanin su, kuma Jinah ta lura da hakan tun zuwanta gidan, haka ma akwai wasu sauran yan uwan da duk basu shiri. -Zaka iya matsawa, dan muna so mu wuce. Dauda ya fada cikin yanayin bacin rai. -Naji duk abinda kuke fada, kuma nasan wannan shegen cikin ba danka bane. Idrisa ya fada yana nuna cikin Jinah tare da yin wani shu'umin murmushi. Zuciyar Jinah ce ta bada wani dum, shi kuma Dauda yi yayi kamar bai ji abinda Idrisa ya fada ba. Kama hannun matarsa yayi suka yi gaba suka bar Idrisa dashe a wurin. Idrisa baida wani makiyi duniya da ya wuce Dauda, kuma yasha alwashin ko ta wane hali sai ya yiwa Dauda illa, gashi yanzu yaji wannan labari sai dai rashin tsoro da ya gani a idon Dauda yasa ya fara konkonto. Tunani ya fara, kafin daga bisani ya tuna koda ya fallasa wannan sirrin babu wanda zai yarda dashi dan kowa yasan ba kaunar Dauda yake ba, cewa za'a yi kawai sharri ne. Rarrashin Jinah Dauda yayi ta yi, kan babu abinda dan uwansa zai ce. Sai dai ita tsoro duk ya mamayeta dan tana tsoron Idrisa ya fallasa wannan sirri. Bayan kwana biyu, zuwa karfe uku na rana kusan kowa yana wurin aiki, ciki har da Dauda. Bugun kofarta Jinah taji ana yi, budewar da zata yi taga Idrisa. -Ki biyoni dakina yanzu ko na fallasa wannan cikin naki, yanzu kowa ya sani. Ganin yanayin da yayi maganar, yasa Jinah bata yi tunanin komai ba, ta bishi a baya ba tare da tayi tunanin me zata yi a dakin dan uwan mijinta ba. Suna shiga, yaja kofa ya garkame. -Yau dan iskan mijin nan naki zai gane kurensa. Zan nuna masa shi karamin dan iska idan yazo ya tarar da abinda zan maki yanzu. Nine babba gareshi amma har yanzu banyi aure ba, shine shi har da zuwa ya auro zukekiyar mace! Kokarin bude kofa Jinah tayi, shi kuma ya janyota tareda gamata da bango, kokarin kwatar kanta ta fara, ya kifa mata wani gigitaccen mari. Ganin ba sarki sai Allah Jinah ta fara hawaye. -Dama na dade, ina fakonki! Harshe yasa yana lasar kuncinta kafin ya gaura kanta da gini ta suma. Daukanta yayi ya jefa kan gado tare da cire kayan jikinta. Ba tareda wani tunani ba yayi kokarin shigarta. Sandarewa yayi sakamakon wani addababben zafi da ya shiga jikinsa, haka yayi ta kokowa neman numfashi amma babu dama, bayan wani dan lokaci da ya dauka cikin wannan azabar Kamar buhun dankali haka ya fadi tim gefen Jinah matacce! ---------------------------- Ko kuma nasan zaku ce, yanzu kuka san labarin Jinah matar aljani kuke karantawa. Tinda gashi Aljani har ya fara aikin kula da matarshi. lol.? Sai kuma idan mun hadu a sabuwar chapter. Amma fa kuyi hakuri ba lokaci, ku dai kawai sai in kun ga update.
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD