CHAPTER 7

2124 Words
A kullum dan adam yana da mafarkai wanda yake da burin wata rana su zama gaske, haka dan adam, akwai wasu abubuwa da suke faruwa a rayuwarsa wadanda zai yi burin a ce mafarki ne yake. Wannan shine abinda Dauda yayi burin a ce mafarki yake, da ganin wannan rana dan uwansa a kan matarsa. Sanadin ranar da ake yi mai zafi da sanya kishi, Dauda ya ajiye aikin da yake yi, ya nufi cikin rumfar hutu dake cikin masana'antar domin samun ruwan da zai jika makoshinsa. Yayi mamaki na rashin ganin Idrisa, bai kawo komai ba a ransa yaje yasha ruwa ya cigaba da aikinsa. Tunawa yayi da abinda ya faru tsakanin shi da Idrisa, da alwashin da Idrisa yasha na sai yayi masa abinda har ya mutu ba zai manta dashi ba. "Tabbas zai iya aikata abinda yayi niya." ya fada a zuciyarshi. Tunawa yayi da ya ganshi lokacin da yake fita daga masana'antar, alhali kuma lokacin tashi daga aiki bai yi ba. "Jinah!" yada cikin tashin hankali, bai tsaya wani dogon tunani ba yaje ya fadawa mahaifinsa zai je gida. Lokacin da yazo gida ya nemi Jinah ko'ina bai ganta ba, haka shima Idrisa bai ganshi ba. Tunani kala-kala yayi tayi, ga kuma zuciyasa dake tsananta buguwa. Dakin Idrisa ya nufa, ya tarar da dakin a kulle. Juyawa yayi da niyyar dubawa makota, amma sai ya fasa da ya tuna babu inda Jinah take zuwa. Yana nan tsaye bakin kofar dakin Idrisan, sai ga Surayya 'yar yayarshi. -Surayya baki ga Jinah ba? -A'a ban ganta ba! -Kawunki fah Idrisa? -Dazu na ganshi ya shiga dakinsa. -Yauwa to jeka abinka. Ya fada kafin ya nufi dakin auntinshi wadda ke da duk wani sifayen yan makullayen dakunan gidan. Kusan sau biyar yana kwankwasa kofar kafin ta bude, fuskarta alamar bacci. -Ya aka yi ne? Ta fada cikin yanayin bacin rai da tunanin ko wasar da Dauda ya saba yi mata ne. Dan idan yayi niyyar yi mata shakiyanci, da ya bubbuga mata kofa ta bude, sai yace mata ai yayi makuwar daki ne. Murmushi yayi da ya fahimci abinda take nufi. -Baba ne ya aikoni daukan kayan aiki da suke dakin Idrisa, sai dai na manta ban karbo makullin dakin ba, shine nake son ki bani na hannunki na bude. Yayi mata karya, ita kuwa bata yi tunanin komai ba ta dauko masa makullin. Yaje ya bude kofar gabansa na dukan uku-uku. Jiri ne ya debeshi, Da sauri ya koma ya rufe kofar, kafafuwansa kasa daukanshi suka yi, ja da baya yayi ya jingina da bango. Bai taba tunanin tsanar da Idrisa ke nuna masa zai kai ya iya aikatawa matarsa wannan danyen aiki ba. Karasawa yayi, kokarin ture Idrisa yayi daga bisa gadon, ya girgiza ganin Idrisa ya fado kasa kamar gawa. Dan tun farko bai lura Idrisa bai motsi ba. Wani mugun kunci ne ya turnukeshi ganin matarshi ba kaya, jikin da ya dade yana mafarkin gani amma bai taba tunanin a irin wannan yanayin ba. Idanun Jinah a rufe suke, alamar tana bacci, anan ya fahimci sumar da ita ne Idrisa yayi, kayanta ya saka mata sannan ya dauketa ya kaita har dakinsu ya shimfideta kan gado. Komawa yayi dakin dan uwan nashi da har yanzu yake kwance a kasa. Nan fah hankalinshi ya tashi, kunnensa ya kara a kirjin Idrisa anan yaji zuciyarshi bata bugawa. A hankali ya sakama dan uwan nashi wando, sannan ya ya barshi anan kwance. Bai rufe dakin ba, yaje ya kaiwa auntynshi makullin. Kada Ashanti (godiyarshi) yayi, nesa da gida. Yayi hakan ne ko zai manta tare da rage damuwar abinda ya faru. Abinda dan uwansa yayi ko yake kokarin yiwa matarshi, ko kuma mutuwar dan uwan nashi bai san wane ne yafi masa ciwo ba. Bayan yayi tafiya mai nisa, ya juya ya koma gida. Tarar da gidan yayi makil da mutane, dan kusan kowa yana nan, sai dai abinda ya bashi mamaki babu alamun an yi mutuwa a gidan, sauke ajiyar zuciya dan yana tunanin wata kil Idrisa ba mutuwa yayi ba. Daki ya nufa dan ganin ko Jinah ta farka. Tarar da ita yayi ta hada kai da gwiwa a tsakiyar gado, sam baya jin dadin ganin matarshi kuma abar kaunarshi cikin damuwa. -Bansan me yayi min ba, ya..ya..umarceni da in bishi dakinsa, na bishi, naji tsoro, tsoron kar ya fada cikin dake a jikina ba naka bane..na..na.. Jinah ce ke fadin haka cikin kuka ba tare da ta jira ya tambayeta abinda ya faru ba. -Ki daina kuka dan Allah Jinah! -Na..naje dakinsa Dauda, hanani yin ihu yayi, ya tsoratani, san..sannan ya buga kaina a bango, sannan, sannan, sannan...Wayyoh Allah! bansan me yayi min ba. Me yayi min, ba zan iya tunawa ba... Ganin tashin hankalin da matarshi ta shiga, Dauda ji yayi yana son ya rarrasheta, ya kwantar mata da hankali, ya gusar mata da wannan tunanin da take. -Bai tabaki ba, nazo kan lokaci sannan na fitar dake daga wurin, bai yi maki komai ba. Shiru Jinah tayi da alamar rashin yarda tace -Ka tabbata? Tsareta yayi da ido don shi kam baida tabbaci, ya fada mata haka ne dan ganin ta kwantar da hankalinta. Itama Jinah tsareshi tayi da nata idon dan jin ya tabbatar mata da maganarshi. -Eh, na tabbata bai yi maki komai ba. Cikin dan kankanin lokacin da baiyi tsammani ba yaji ta fado jikinsa, ta kankameshi tana kuka marar sauti. Ji yayi zuciyoyinsu na bugawa a tare, lallausar fatarta na gugan tashi, tunda suke hakan bai taba faruwa ba, bai taba jin dadi irin na yau ba, haka bai taba jin matsanancin zafi da radadin jiki irin na yau ba. Dan ji yayi kamar an kunna mashi wuta a jiki. Lallai abu ne marar misaltuwa a wurinshi dadi da ciwo a lokaci guda. Ganin idan suka cigaba da kasancewa manne da juna to fah zai iya kamawa da wutar gaske yasa ya janye jikinshi daga nata. Ba'a dau lokaci ba kuwa ya bar jin zafin jikin. -Nagode kwarai da gaske! Jinah ta fada cike da farin ciki, murmushi kan lebenta. -Nauyina ne hakan, kuma ki kwantar da hankalinki ba zai taba fadawa kowa ba abinda yaji. Ya bata amsa kafin ta mike ta nufi ban daki. Wanka tayi da ta fito bata ganshi ba, kaya ta sake, tayi sallah sannan ta kwanta kan gado. Bata fatan ta kara haduwa da Idrisa, inuwar ma mai kama da Idrisa bata fatan sake gani dan ya tsoratata sosai, dan haka dole tayi taka tsantsan dashi. Da irin wannan tunanin bacci marar nauyi ya fara saceta. Cen cikin baccinta sama-sama taji kara daga wajen tsakar gida, zuciya na dukan uku-uku, Jinah ta fito daga daki dan ganin meke faruwa. Matan gidan ne ke ta kuka, Maza kuwa na kokarin rarrashinsu, wasu dora hannuwa biyu suka yi a kai, wasu na girgiza kai irin na anga abin alhini, Habi ta gani uwar gidan sirikinta kwance tana birgima a kasa, 'ya'yanta mata biyu suna riketa. Kasa fahimtar komai tayi, zuciyarta na bugawa kwarai. Neman Dauda ta fara yi kafin ta hangeshi kusan kofar dakin mamarshi, fuska a dame. -Wayyoh dana! me yasa Allah bai daukeni ba a maimakonsa, wayyoh Idrisana. Muryar Habi ke karade ko'ina da kukan rashin danta. Nan Jinah ta fahimci abinda ke faruwa, toshe bakinta tayi da hannuwanta ta zauna dirshen bisa wani benci dake kusa da ita. Duk abinda yayi mata, ba zata yi mashi fatan mutuwa ba. Cikin zuciyarta tace "to me ya faru dashi?" Dawowa hayyacinta tayi ganin Isa ya tunkari Dauda kamar wani mayunwacin zaki, Kanin Idrisa ne wanda suke uwa daya uba daya, wanda shima basu shiri ko kadan da Dauda kuma ya girmi Dauda da shekara biyu. -Kai ne ka kasheshi, naga lokacin da ka fito daga dakinshi, kai ne nan ka kasheshi! Isa ke fadin haka kafin ya kaima Dauda wani mugun naushi a fuska wanda yayi sanadiyar faduwar Dauda kasa, da sauri Jinah ta mike tsaye. Hankalin kowa dawowa yayi kansu. Wani kawu da wani dan uwan Dauda suka yi saurin janye Isa. -Ku kyaleni! Sai na kasheshi kamar yanda ya kashe mani dan uwa! shi... Bai karasa maganarshi ba yaji saukar wani gigitaccen mari a kuncinshi na hagu, da sauri ya dago yaga mahaifinsu ne. -Kada na kara jin wata magana makamanciyar irin wannan ta fito daga bakinka! Dan iska kawai! ta yaya zaka zargi dan uwanka da kashe dan uwanshi, baka ji kunya ba? Mahaifin nasu yake fadar haka cikin fushi hannunsa na rawa, bai gama farfadowa daga jin mutuwar babban danshi ba, yanzu kuma ga wannan abu da yake faruwa. -Kayi hakuri baba, zo ka zauna! Daya daga cikin 'ya'yansa ne ya fada yana kokarin kwantarwa da baban nasu hankali. Babu wanda ya yarda da maganar da Isa ya fada, dan sun san kiyayyar da yake yiwa Dauda komai zai iya kirkira ganin ya cutar dashi. Kuma duk sun san alakar dake tsakanin Idrisa da Isa, akwai abota mai karfi bayan yan uwantaka ma, dan haka komai zai iya cewa gameda mutuwar Idrisa, alhali Idrisan mutuwa ce yayi ta Allah da annabi ba wai kasheshi aka yi ba, abinda dai suke tunani dan babu wanda yayi tunanin akasin haka. Daren ranar babu wanda ya samu runtsawa, dan wannan shine karon farko da dadewa mutuwa bata konkwasa masu kofa ba. -Babu abinda nayi masa! Cewar Dauda yana fuskantar matarshi dake kan gado shi kuma yana zaune a kasa a lokacin da suka koma daki. -Nasan ba zaka aikata haka ba. Ta bashi amsa. -Bari tabbatar da hakan, dan abinda yayi kokarin yi maki, Abinda na kudira kenan, sai na kasheshi... -A'a, ka bar irin wannan tunanin, komin abinda mutum yayi mana, ba mu bane zamu yanke hukunci na rayuwarshi ba. Kai mutum ne na kwarai Dauda kuma dan Allah kar ka canja daga haka. Murmushi yayi mata, dan yaji dadin kalaminta. Yasan wata rana itama zata fara sonshi. Bubbuga masu kofa da ake yi kamar za'a balleta ne ya katse masu hirar da suke yi. Tashi Dauda yayi ya bude, sai dai da sauri ya ja da baya, lokacin da suka yi ido biyu da mai bubbuga kofar. Karasowa Jinah tayi wajensu, Dauda yayi mata umarni da ta koma bayanshi. Isa ne a gabansu, fuska a murtuke da kuma katuwar tabarya a hannunshi. -Dan Allah Isa kayi hakuri, ka kwantar da hankalinka, kar kayi abinda zai saka nadama. Jinah ce ke rokonshi, cikinta ya duru ruwan tsoro. -Sai na kasheka kamar yanda ka kashe Idrisa! -Na fada maka ba ni na kasheshi ba... -Karya kake yi, ai ya fada min abinda yake shirin yiwa wannan karuwar, shi yasa ka kasheshi! -Kada ka kara zagar min mata! -Dan Allah Dauda ba lokacin yin wannan rigimar bane. Jinah ta fada, ganin mijin nata shi kokarin kara kunna wutar yake. -Karuwa ce mana, idan ba haka ba, ya za'a yi ta shigo maka gida da cikin wani. Wani lafiyayyen naushi Dauda ya kaima Isa a fuska, shima Isa bai yi wata-wata ba ya kwada masa tabaryar dake hannunsa. Anan Dauda ya fadi kasa, jini na zuba kamar fanfo. Yar da tabaryar Isa yayi tare da saurin toshe bakin dake kokarin fasa ihu da hannunshi. Kuka Jinah take ganin mijinta a kasa baya motsi ga jini na zuba. Tsoro ya kama Isa, ya bar shedan yayi galaba a kanshi, so yake ya kasheshi, amma kuma yanzu da ya aikata nadama ce fal yake yi. Bai san me zai yi ba, idan mutane suka san abinda ya aikata, kashe dan uwansa na jini, kuma tabbas idan baba ya sani nima sai ya kasheni, ko kuma naje kurkuku, a'a ba zan bar hakan ta faru ba. Hakan zata faru ne idan mutane suka sani. Ya fada, yana kallon Jinah kafin ya saka hannayensa biyu ya shake mata wuya, kokarin kasheta yake yi, dan kar ta tona masa asiri. Kara makure Jinah yayi, ita kuma tari take tana kokowar kwatar numfashi, sai dai shima kamar ana yi masa hakan, shima ji yayi ya kasa numfashi, ga wata iriyar zufa da yake yi, jikinsa ya dauki wani zafi. Duk da wannan azabar kin sake Jinah yayi, dan kasheta shine mafita. Sassaucin makurar Jinah ta fara ji, iskan shaka taji ta fara samu lokacin da Isa ya fadi kasa matacce! ------------------------------------------------------ So pray for the deads lol. ? Ina mai barka da zuwa ga sabbin makaranta wannan labari, koda yaushe abin jin dadi ne gareni ganin sakonninku da kuma comments naku. Sannan ina mai baku hakurin lattin ganin cigaban wannan labari, hakan ta faru ne sakamakon azumi, da na bari ne sai bayan sallah to kuma wannan Monday din muke komawa school shine nace bari nayi maku ko 3 chapters ne kafin mu koma. Sai mun hadu a wata chapter din idan Allah ya kaimu.
Free reading for new users
Scan code to download app
Facebookexpand_more
  • author-avatar
    Writer
  • chap_listContents
  • likeADD