JINAH (Matar Aljani)Updated at Jun 29, 2022, 11:19
Soyayya tsakanin jinsi biyu, jinsin mutum da na aljan
Soman taɓi :
Hankalin Sarah yayi matukar tashi lokacin da ta tabbatar Kimba ya rigata dawowa gida. Tsoron nata kasa boyuwa yayi har Jinah ta fahimci halin da take ciki. Kokarin kwantar mata da hankali tayi.
-Babu abinda zai yi maki, ba ce maki yayi, idan yaje cen zai dade bai dawo ba? To kenan ban ga dalilin tada hankali ba ganin ba wani dadewa yayi ba sosai.
-Eh, amma...
-Ba wani amma, ki kwantar da hankalinki, ni nan nasan me zan yi.
-Me zaki yi?
Sarah ta tambayeta tana kwalalo ido.
-Ke dai ki jira zaki gani.
Jinah ta fada cike da tabbatarwa, dariya Sarah take wanda har tsoron nata ya gushe. Ita kuma Jinah fuska tayi, irin yanayin ita fa ba da wasa take ba. Ta tsani mutumin nan duk da bata taba ganinsa ba, kuma lallai ya cancanci a koya masa hankali. Kokarin shiga gidan suka yi ta baya, sai dai ganin kowacce da yaro a hannunta, so ba zasu iya shiga da kayan baki daya ba. Goya Aya Jinah tayi a bayanta sannan ta dauki Ayyu a hannu, ita kuma Sarah ta shiga da kayan. Duk wani taku idan tayi zuwa cikin gidan, sai taji tana kara kusanto muryoyin dake magana cikin gidan, muryar mijinta da wasu da ta kasa gane su waye take ji. Su waye wadannan mutanen? Wata kila daya daga cikin kishiyoyina ne. Ta fada cikin ranta. Dakinta ta nufa a maimakon ta nufi inda mijin nata yake, domin ajiye kayan nasu, sai dai...
-Sarah!
Muryar Kimba taji ya kwala mata kira. Wani bugawa zuciyarta tayi, taji yin numfashi na shirin gagararta, Sakin Jikunan dake hannunta tayi. Kamar wata sakago, ta juya a hankali suna fuskantar juna.
-Ina son magana dake, ki sameni a daki.
Ya fada cikin wani yanayi da ta kasa fahimta.
-Ina..ina zuwa.
Kayan ta fara kaiwa daki, sannan ta yiwa Jinah da tagwayen masauki kafin taje amsa kiran mijinta.
-Ina yini?
Ta fara gaidashi.
-An zo lafiya? Ya gajiyar hanya?...tun yaushe kazo?... Me kake so na hada maka, ko na kai maka ruwan wanka?...