
Karfe biyu da rabi na dare naji Ana bugamin kufan gidan mu lokacin banyi bacci ba domin lokacin ina chatting da abokai na a f*******: nawa. Cikin hassala na fusata da karfin murya haba shafa waike wannan wani Irin wulakaci ne toh walahi yau bazan lamunta ba, babban abunda yasamin mamaki shine daina bugun kofan danaji alhalin nasan idon shafa ne tafara Sai na tsargu, banyi kasa a guywaba nazo nabude kofan domin ganin meke faruwa kwatsam Sai gawar khadija Isa a bakin kofata a baje cikin jini.
A wannan lokacin ne gabana yayi masifan bugawa domin abunda ya faru da safiyar yau misalin Karfe 9:00 na safe. Nida kanwana hadiza zamuje kasuwa cefane kasance wa bama iya rabuwa da junan mu duk ina da aka aiki dayan mu Sai daya ya rakasa, munzo gurin wani shago Kenan Sai kanwata hadiza ta hango khadija Isa a tsakiyar wasu samari su hudu bantashi aune ba kawai gani nayi hadiza ta ci mata kwala tana kokarin ciro wata kwalbar coca cola zata fasamata ita aka. Daker mutane muka shiga tsakanin su a wannan lokacin ne hadiza ta dauki alwashin daukan ranta a cikin taron al'umma. Ganin gawar khadija Isa a bakin kofan dakina ne ya tabbatar cewa hadiza ta aikata aikin da tace zatayi akan khadija Isa.
Amma mai hadina da gawan khadija Isa kuma maiyasa aka kawomin ita bakin kofana nan take nayanke hukunci Kawar da gawar domin gujewa zargin jami'an tsaro akan kanwata hadiza da kuma ni kaina, moto nadauko nashigar da gawar nafara nisa Kenan nanufi wani jeji domin jefa gawar ta a ruwa. Dai dai lokacin da nake kokarin bude motan ne sai naga tako ina Ana kaskani tare da kukin din bindiga bantashi aune ba kawai sai naji kalmar nanda police ke amfani da'ita aduk lokacin da suka kusa Kama mai laifi wato you are under arrest. Lokacin da naji sun ambaci wannan munmunar kalman agunnan take naji zuciya na yabuga domin nasan nashiga hannu, cikin karfin Kali nayi ta maza daniyar koma wa cikin mota domin gudura wannan lokacin ne suka fara sakarwa motar wuta a gaggauce nafito daga motar na gudu tahakane na tsere musu, amma ba gudur tsira ba domin gawar da takar duna tare da password dina duk suna cikin motar, a Wannan lokacin ne nayi gagawar Isa gida daniyan ganawa da kanwana dagane da wannan abun dake faruwa, da isata kai tsaye dakin kanwata hadiza na wuce, nayi mamakin ganin dakin kanwana hadiza abude misalin Karfe 3:30 na dare kofa nashiga dakin. Sai naga babban abun al'ajabi domin gawar kanwata hadiza nagani tareda Kuka a cikin ta, a wannan lokacin ne tunanin mahaifiyar mu ya fadomin ita kuma wani hali take ciki nan take natafi dakinta ganin yadda nasame tane na fahimci batasan Komai yake faruwa a gidan nan ba. Domin kwance nasameta tana sharar bacci akan darduman ta a tsakiyar daki, a gaggauce nafito daga dakin ta domin nasan kafin nasanar da ita abunda ke faruwa jami'an tsaro sun samu isowa guna, aguje na bar gidan kafin nakai karshin ginin gidan sai naji jiniya alamun police sun Kara so Kenan.
Nan take na Kama ginin bayan gidan muna fada Kaman wani barawo ko mai laifi. Bayan naje nabuya a bayan wani kangon dake bayan gidan mune tunani ya fadomin
shin waye yakashe khadija Isa.
Waye yakashe kanwata hadiza.
Kuma maiyasa aka sakani acikin wannan laifukan? Dai dai lokacin da nake tunanin ne sai naji samari sauna fadin ai yanzu yada tarko babu mahalukin da Zai iya fiddashi. Da sauri nafito daga inda nabuya domin Kama daya daga cikin su.

